Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Solomon: Divides his kingdom into subsistence departments; the daily subsistence rate for his court

19 ayoyi · 46 fannoni

Ayoyi game da Divides his kingdom into subsistence departments; the daily subsistence rate for his court

  1. Solomon yana da gwamnoni yankuna goma sha biyu a bisa dukan Isra’ila, waɗanda suke tanaji abinci domin sarki da kuma gidan sarauta. Kowanne yakan tanada abinci na wata ɗaya a shekara.

  2. Ga sunayensu, Ben-Hur, shi ne a ƙasar tudun Efraim;

  3. Ben-Deker, shi ne a Makaz, Sha’albim, Bet-Shemesh da Elon Bet-Hanan;

  4. Ben-Hesed, shi ne a Arubbot (Soko da dukan ƙasar Hefer);

  5. Ben-Abinadab, shi ne a Nafot Dor (ya auri Tafat ’yar Solomon);

  6. Ba’ana ɗan Ahilud, shi ne a Ta’anak da Megiddo, da kuma dukan Bet-Sheyan biye da Zaretan ƙasa da Yezireyel, daga Bet-Sheyan zuwa Abel-Mehola a ƙetaren Yokmeyam;

  7. Ben-Geber, shi ne a Ramot Gileyad (Mazaunan Yayir ɗan Manasse a Gileyad suna a ƙarƙashinsa, haka ma yankin Argob a Bashan tare da manyan biranen sittin masu katanga da suke da ƙyamare na tagulla);

  8. Ahinadab ɗan Iddo, shi ne a Mahanayim;

  9. Ahimawaz, shi ne a Naftali (ya auri Basemat ’yar Solomon);

  10. Ba’ana ɗan Hushai, shi ne a Asher da Bayelot;

  11. Yehoshafat ɗan Faruwa, shi ne a Issakar;

  12. Shimeyi ɗan Ela, shi ne a Benyamin;

  13. Geber ɗan Uri, shi ne a Gileyad (ƙasar Sihon sarkin Amoriyawa da kuma Og sarkin Bashan). Shi ne kaɗai gwamna a bisa yankin.

  14. Mutanen Yahuda da na Isra’ila sun yi yawa sai ka ce yashi a bakin teku. Suka ci, suka sha, suka kuma yi farin ciki.

  15. Solomon kuwa ya yi mulki a bisa dukan masarautai daga Kogi zuwa ƙasar Filistiyawa, har zuwa iyakar Masar. Waɗannan ƙasashe sun yi ta kawo haraji, suka kuma zama bayin Solomon dukan kwanakin ransa.

  16. Tanajin Solomon na kowace rana su ne, garwa talatin na garin abinci,

  17. shanun da aka yi kiwo a gida guda goma, shanu ashirin da suka ƙoshi daga kiwo, tumaki da awaki ɗari; ban da ƙishimai, bareyi, batsiyoyi, da kaji masu ƙiba.

  18. Shugabannin yankuna, kowanne a watansa yakan yi tanajin abinci domin Sarki Solomon da kuma duk wanda ya zo teburin sarki. Sun tabbatar ba a rasa kome ba.

  19. Kowa a cikinsu, bisa ga lokacin da aka ba shi, yakan kai hatsin sha’ir da ciyawa domin dawakan-kekunan yaƙi, da sauran dawakai a inda aka ajiye su.