Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sacrifices

248 ayoyi · 55 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Kashegari suka miƙa hadayu ga Ubangiji suka kuma miƙa hadayu bijimai dubu, raguna dubu da kuma ’yan raguna dubu na ƙonawa gare shi, tare da hadayunsu na sha da sauran hadayu a yalwace saboda dukan Isra’ila.

  2. Sarki Solomon kuwa da taron Isra’ila gaba ɗaya da suka taru kewaye da shi suna a gaban akwatin alkawarin, suna miƙa tumaki da shanu masu yawa da suka wuce ƙirge ko lissafi.

  3. Sa’ad da Solomon ya gama yin addu’a, sai wuta ya sauko daga sama ya cinye hadaya ta ƙonawa da kuma sadakokin, ɗaukakar Ubangiji kuwa ta cika haikalin.

  4. Sarki Solomon kuwa ya miƙa hadayar bijimai dubu ashirin da biyu da kuma tumaki da awaki dubu ɗari da dubu ashirin. Ta haka sarki da dukan mutane suka keɓe haikalin Allah.

  5. sai Ubangiji ya bayyana gare shi a daren ya ce, “Na ji addu’arka na kuma zaɓi wannan wuri don kaina, a matsayin haikali don hadayu.

  6. Sarki ya ba da taimako daga mallakarsa domin hadayun ƙonawa, safe da yamma da kuma don hadayun ƙonawa a Asabbatai, Sabon Wata da kuma ƙayyadaddun bukukkuwa kamar yadda yake a rubuce a cikin Dokar Ubangiji.

  7. Domin sun yashe ni suka kuma ƙone turare wa waɗansu alloli, suka tsokane ni in yi fushi ta wurin dukan abin da hannuwansu suka yi, fushina zai zuba a kan wannan wuri, ba kuma za a kwantar da shi ba.’

  8. Bayan lokacin bikin ya wuce, sai Ayuba yă aika su zo don yă tsarkake su. Tun da sassafe zai miƙa hadaya ta ƙonawa domin kowannensu, don yana tunani cewa, “Mai yiwuwa ’ya’yana sun yi wa Allah zunubi, ko sun la’anta shi a cikin zuciyarsu.” Haka Ayuba ya saba yi.

  9. Ku miƙa hadayun da suka dace ku kuma dogara ga Ubangiji.

  10. Sa’an nan kaina zai ɗaukaka a bisa abokan gābana waɗanda suka kewaye ni; a tabanakul nasa zan miƙa hadaya da sowa ta farin ciki; zan rera in kuma yi kiɗi ga Ubangiji.

  11. Hadaya da sadaka ba ka sha’awa, amma kunnuwana ka huda; hadayun ƙonawa da hadayun zunubi ba ka bukata.

  12. “Ku tattara mini shafaffuna, waɗanda suka yi alkawari da ni ta wurin hadaya.”

  13. Hadayun Allah su ne karyayyen ruhu; karyayyiya da kuma zuciya mai tuba, Ya Allah, ba za ka ƙi ba.

  14. Ta haka za a kasance da hadayu masu adalci, hadayun ƙonawa ɗungum don su faranta ka; sa’an nan za a miƙa bijimai a bagadenka.

  15. Zan miƙa kitsen dabbobi gare ka da kuma baye-baye na raguna; zan miƙa bijimai da awaki. Sela

  16. Suka miƙa ’ya’yansu maza hadaya ’yan matansu kuma ga aljanu.

  17. Bari su miƙa hadaya ta godiya su kuma ba da labarin ayyukansa da waƙoƙin farin ciki.

  18. Zan yi hadayar godiya gare ka in kuma kira bisa sunan Ubangiji.

  19. Ubangiji shi ne Allah ya kuma sa haskensa ya haskaka a kanmu. Da kwanoni a hannunmu, muka shiga jerin gwanon biki ku kai su ƙahoni na bagade.

  20. Bari a sa addu’ata a gabanka kamar turaren ƙonawa; bari ɗagawa hannuwana ta zama kamar hadayar yamma.

  21. Yin abin da yake daidai da kuma nagari Ubangiji ya fi yarda da shi fiye da hadaya.

  22. Ubangiji ya ce, “Yawan hadayunku, mene ne suke a gare ni?” Ina da isashen hadayun ƙonawa, na raguna da na kitsen dabbobi masu ƙiba; ba na jin daɗin jinin bijimai da na tumaki da kuma na awaki.

  23. Sa’ad da kuka ɗaga hannuwanku wajen yin addu’a, zan ɓoye fuskata daga gare ku; ko da kun miƙa addu’o’i masu yawa, ba zan kasa kunne ba. Hannuwanku sun cika da jini!

  24. Ba ku kawo mini tumaki don hadaya ta ƙonewa ba, balle ku girmama ni da hadayunku. Ban nawaita muku da hadaya ta gari ba balle in gajiyar da ku da bukatar turare.

  25. Ba ku saya wani turaren kalamus domina ba ko ku gamshe ni da kitsen hadayunku. Amma kun nawaita ni da zunubanku kuka kuma gajiyar da ni da laifofinku.