Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sacrifices: Yearly

4 ayoyi · 55 fannoni

Ayoyi game da Yearly

  1. “Ga yadda Haruna zai shiga wuri mai tsarki, zai zo da ɗan bijimi domin hadaya don zunubi da kuma rago domin hadaya ta ƙonawa.

  2. Shekara-shekara wannan mutum yakan haura daga garinsa zuwa Shilo domin yin sujada da miƙa hadayu ga Ubangiji Maɗaukaki. A can kuwa ’ya’yan Eli maza biyu, Hofni da Finehas su ne firistoci na Ubangiji.

  3. Da shekara ta kewayo, sai Elkana da iyalinsa suka sāke tafi Shilo domin su yi hadaya ga Ubangiji, yă kuma cika alkawarin da ya yi.

  4. In mahaifinka bai gan ni ba, ka gaya masa cewa, ‘Dawuda ya nemi izinina domin yă hanzarta yă tafi garinsa a Betlehem saboda ana hadaya ta shekara-shekara don dukan zuriyarsa.’