Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sacrifices: Condemned for offering, to idols

5 ayoyi · 55 fannoni

Ayoyi game da Condemned for offering, to idols

  1. Domin sun yashe ni suka kuma ƙone turare wa waɗansu alloli, suka tsokane ni in yi fushi ta wurin dukan abin da hannuwansu suka yi, fushina zai zuba a kan wannan wuri, ba kuma za a kwantar da shi ba.’

  2. mutanen da suna cin gaba da tsokanata a fuskata, suna miƙa hadayu a gonaki suna ƙone turare a bagadan tubali;

  3. saboda zunubanku da kuma zunuban kakanninku,” in ji Ubangiji. “Gama sun ƙone turare a kan duwatsu suka kuma ƙazantar da ni a kan tuddai, zan yi musu awo in zuba a cinyoyinsu cikakken ramuwa saboda ayyukansu na dā.”

  4. Sa’ad da na kawo su cikin ƙasar da na rantse zan ba su suka kuma ga tudu mai tsawo ko itace mai ganye, a can suka miƙa hadayunsu, suka yi sadakokin da suka tsokane ni na yi fushi, suka miƙa turaren ƙanshinsu suka kuma zuba sadakokinsu na sha.

  5. Sa’ad da kuka miƙa kyautai naku, hadayar ’ya’yanku maza a wuta, kuna cin gaba da ƙazantar da kanku da duka gumakanku har wa yau. Zan bari ku nemi shawarata, ya gidan Isra’ila? Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ba zan bari ku nemi shawarata ba.