Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sacrifices: Could not take away sin

13 ayoyi · 55 fannoni

Ayoyi game da Could not take away sin

  1. Hadaya da sadaka ba ka sha’awa, amma kunnuwana ka huda; hadayun ƙonawa da hadayun zunubi ba ka bukata.

  2. Wannan ma yana da ma’ana wa mutane a yau. Ya nuna cewa ba za mu iya wanke lamirinmu ta wurin miƙa baye-baye da hadayu ba.

  3. Dokar, inuwa ce kawai ta kyawawan abubuwa masu zuwa, wannan inuwar ba ita ce ainihin abubuwan ba ne. Saboda haka ba za tă taɓa mai da masu matsowa kusa don yin sujada cikakku ta wurin irin hadayun da ake maimaitawa ba fasawa shekara-shekara ba.

  4. Da a ce za tă iya, da ba su daina miƙa hadayu ba? Ai, da an riga an tsabtacce masu yin sujada sau ɗaya tak, da kuma ba za su ƙara damuwa da zunubansu ba.

  5. Amma waɗancan hadayu abin tunawa da zunubai ne na kowace shekara,

  6. domin ba zai taɓa yiwuwa jinin bijimai da na awaki yă kawar da zunubai ba.

  7. Saboda haka, sa’ad da Kiristi ya shigo duniya ya ce, “Hadaya da sadaka kam ba ka so, sai dai ka tanadar mini jiki;

  8. hadayun ƙonawa da kuma hadayun zunubi ba ka ji daɗin.

  9. Sai na ce, ‘Ga ni nan, a rubuce yake cikin naɗaɗɗen littafi na zo in aikata nufinka, ya Allah.’ ”

  10. Da farko ya ce, “Hadayu da sadakoki, hadayun ƙonawa da hadayun zunubi ba ka so, ba ka kuwa jin daɗinsu” (ko da yake doka ta bukaci a yi su).

  11. Sa’an nan ya ce, “Ga ni nan, na zo in aikata nufinka.” Ya kawar da na farkon domin yă kafa na biyun.

  12. Kuma bisa ga wannan nufi, aka mai da mu masu tsarki ta wurin miƙa hadayar jikin Yesu Kiristi sau ɗaya tak.

  13. Kowace rana kowane firist yakan tsaya yin hidimar ibadarsa; sau da sau yakan miƙa hadayu iri ɗaya, waɗanda ba za su taɓa kawar da zunubai ba.