Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sacrifices: For the whole nation

17 ayoyi · 55 fannoni

Ayoyi game da For the whole nation

  1. “Sa’an nan zai yanka akuya na hadaya don zunubi saboda mutane, yă kai jinin bayan labule, yă yi da shi yadda ya yi da jinin bijimin. Zai yayyafa shi a kan murfin kafarar da kuma a gabansa.

  2. Ta haka zai yi kafara domin Wuri Mafi Tsarki saboda ƙazantar tawayen Isra’ilawa, da laifofinsu, da dukan zunubansu. Haka zai yi saboda Tentin Sujada wanda yake a cikinsu a tsakiyar ƙazantarsu.

  3. Kada kowa yă kasance a Tentin Sujada daga lokacin da Haruna ya shiga don yă yi kafara a Wuri Mafi Tsarki har sai ya fita, bayan ya yi kafara domin kansa, gidansa da kuma dukan jama’ar Isra’ila.

  4. “Sa’an nan zai fita zuwa bagade da yake a gaban Ubangiji, yă yi kafara dominsa. Zai ɗibi jinin bijimi da na akuya yă zuba a ƙahonin bagade.

  5. Zai yayyafa jinin a kan bagade da yatsarsa sau bakwai, yă tsabtacce shi yă kuma tsarkake shi daga ƙazantar Isra’ilawa.

  6. “Sa’ad da Haruna ya gama yin kafara domin Wuri Mafi Tsarki, Tentin Sujada da kuma bagade, sai yă kawo akuya mai rai.

  7. Haruna zai ɗibiya hannuwansa a kan akuya mai ran, yă furta a kansa dukan mugunta da tawayen Isra’ilawa, dukan zunubansu, yă kuma sa su a kan akuyan. Zai kori akuyan zuwa cikin jeji a hannun mutumin da aka ba shi aikin yin haka.

  8. Akuyan zai ɗauka a kansa dukan zunubansu zuwa kaɗaitaccen wuri, a can mutumin zai sake shi a jeji.

  9. “Sa’an nan Haruna zai shiga Tentin Sujada yă tuɓe rigunansa na lilin da ya sa, kafin yă shiga Wuri Mafi Tsarki, zai kuma bar su a can.

  10. Zai yi wanka a tsattsarkan wuri yă sa rigunarsa na kullum. Sa’an nan zai fita yă miƙa hadaya ta ƙonawa domin kansa da hadaya ta ƙonawa domin mutane, don yă yi kafara domin kansa da kuma domin mutane.

  11. Zai kuma ƙone kitsen hadaya don zunubi a kan bagade.

  12. “Dole mutumin da ya saki akuya na azazel yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka; bayan haka zai iya shiga sansani.

  13. Dole a ɗauki jini, fata, nama da kuma ƙashin bijimi da akuyan hadaya don zunubi, waɗanda aka kawo jininsu cikin Wuri Mafi Tsarki don kafara, a kai waje da sansani a ƙone.

  14. Dole mutumin da ya ƙone su yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, bayan haka zai iya shiga sansani.

  15. “Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a gare ku. A rana ta goma ga wata na bakwai, dole ku yi mūsu kanku, ba kuwa za ku yi wani aiki ba, ko da mutum baƙo ne a cikinku ko kuwa ɗan ƙasa,

  16. gama a wannan rana za a yi kafara dominku, don a tsarkake ku. Sa’an nan a gaban Ubangiji, za a tsarkake ku daga dukan zunubanku.

  17. Kashegari suka miƙa hadayu ga Ubangiji suka kuma miƙa hadayu bijimai dubu, raguna dubu da kuma ’yan raguna dubu na ƙonawa gare shi, tare da hadayunsu na sha da sauran hadayu a yalwace saboda dukan Isra’ila.