Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Psalms

896 ayoyi · 16 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Kada ku ɗaga ƙahoninku gāba da sama; kada ku yi magana da miƙaƙƙen wuya.’ ”

  2. Ba wani daga gabas ko yamma ko hamada da zai ɗaukaka mutum.

  3. Amma Allah ne mai yin shari’a, yakan saukar da wannan, yă kuma tayar da wani.

  4. A hannun Ubangiji akwai kwaf cike da ruwan inabi mai kumfa gauraye da kayan yaji; yakan zuba shi, dukan mugayen duniya kuwa su sha shi tas.

  5. Game da ni dai, zan furta wannan har abada; zan rera yabo ga Allah na Yaƙub,

  6. wanda ya ce, “Zan yanke ƙahonin dukan mugaye, amma za a ɗaga ƙahonin adalai sama.”

  7. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Tare da kayan kiɗi masu tsirkiya. Zabura ta Asaf. Waƙa ce. A cikin Yahuda an san Allah; sunansa da girma yake a cikin Isra’ila.

  8. Tentinsa yana a Salem mazauninsa yana a Sihiyona.

  9. A can ya kakkarya kibiyoyin wuta, garkuwoyi da takuban, makaman yaƙi. Sela

  10. Darajarka tana da haske, fiye da darajar tuddai waɗanda suke cike da namun jeji masu yawa.

  11. Jarumawa sun zube kamar ganima sun yi barcinsu na ƙarshe; ba ko jarumi guda da zai iya ɗaga hannuwansa.

  12. A tsawatawarka, ya Allah na Yaƙub, doki da keken yaƙi suka kwanta ba motsi.

  13. Kai kaɗai ne za a ji tsoro. Wane ne zai iya tsayawa sa’ad da ka yi fushi?

  14. Daga sama ka yi shelar hukunci, ƙasa kuwa ta ji tsoro ta kuwa yi tsit,

  15. sa’ad da kai, ya Allah, ka tashi don ka yi shari’a, don ka cece dukan masu shan wahala a ƙasar. Sela

  16. Tabbatacce fushinka a kan mutane kan jawo maka yabo, waɗanda suka tsira daga fushinka za su zama kamar rawaninka.

  17. Ku yi alkawari wa Ubangiji Allahnku ku kuma cika su; bari dukan ƙasashen maƙwabta su kawo kyautai ga Wannan da za a ji tsoro.

  18. Ya kakkarya ƙarfin masu mulki; sarakunan duniya suna tsoronsa.

  19. Zabura ta Asaf. Ya Allah, al’ummai sun mamaye gādonka; sun ƙazantar da haikalinka mai tsarki, sun bar Urushalima kufai.

  20. Sun ba da gawawwakin bayinka kamar abinci ga tsuntsayen sararin sama, nama jikin tsarkakanka ga namun jejin duniya.

  21. Sun zubar da jini kamar ruwa ko’ina a Urushalima, kuma babu wani da zai binne matattu.

  22. Mun zama abin reni ga maƙwabta, abin ba’a da reni ga waɗanda suke kewaye da mu.

  23. Har yaushe, ya Ubangiji za ka yi ta fushi? Har abada ne? Har yaushe kishinka zai yi ta ƙuna kamar wuta?

  24. Ka zuba fushinka a kan al’umman da ba su yarda da kai ba, a kan mulkokin da ba sa kira bisa sunanka;

  25. gama sun cinye Yaƙub suka lalatar da ƙasar zamansa.