Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Paul

619 ayoyi · 103 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Kashegari Agiriffa da Bernis suka yi shiga irin ta sarauta suka shiga ɗakin jama’a tare da manyan sojoji da manyan mutanen birni. Da umarnin Festus, sai aka shigo da Bulus.

  2. Sai Festus ya ce, “Sarki Agiriffa, da kuma dukan waɗanda suke tare da mu, kun ga wannan mutum! Dukan jama’ar Yahudawa sun kawo mini kararsa a Urushalima da kuma a nan Kaisariya, suna kururuwa suna cewa bai kamata a bar shi da rai ba.

  3. Ban same shi da wani laifin da ya isa kisa ba, amma saboda ya ɗaukaka ƙararsa zuwa gaban Babban Sarki sai na yanke shawara in aika da shi Roma.

  4. Ba ni da wata tabbatacciyar maganar da zan rubuta wa Mai Girma game da shi. Saboda haka na kawo shi a gabanku duka, musamman a gabanka, Sarki Agiriffa, saboda a sakamakon wannan bincike zan iya samun abin da zan rubuta.

  5. Don a ganina wauta ce a aika da ɗan kurkuku ba tare da an nuna zargin da ake yi a kansa ba.”

  6. “Yahudawa duk sun san yadda na yi rayuwa tun ina yaro, daga farkon rayuwata a ƙasarmu da kuma a Urushalima.

  7. Sun san ni tun da daɗewa za su kuwa shaida, in suna so, cewa bisa ga ɗarikar addininmu mafi tsanani, na yi rayuwar Bafarisiye ne.

  8. “Ni ma a dā na tabbata cewa ya kamata in yi duk abin da zan iya yi domin in yi gāba da sunan Yesu Banazare.

  9. Abin da na yi ke nan a Urushalima. Da izinin manyan firistoci na sa tsarkaka da yawa a kurkuku, sa’ad da kuma ake kashe su, nakan ka da ƙuri’ata gāba da su.

  10. Sau da dama nakan bi majami’a-majami’a, in sa a yi musu hukunci. Na kuma yi ƙoƙarin tilasta su su yi saɓo. Don kuma tsananin fushi da su, sai da na fafare su har waɗansu garuruwa na ƙetaren iyaka, ina tsananta musu.

  11. “A cikin irin tafiye-tafiyen nan ne ina kan hanya zuwa Damaskus tare da izini daga manyan firistoci.

  12. Da tsakar rana, ya sarki, sa’ad da nake kan hanya, sai na ga wani haske daga sama, fiye da hasken rana, yana haskakawa kewaye da ni da abokan tafiyata.

  13. Dukanmu muka fāɗi ƙasa, na kuwa ji wata murya tana ce mini da harshen Arameyik, ‘Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini? Yana da wuya ka shuri tsinken tsokanar dabba.’

  14. “Sai na yi tambaya na ce, ‘Wane ne kai, ya Ubangiji?’ “Ubangiji ya ce, ‘Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.

  15. Yanzu ka tashi, ka tsaya da ƙafafunka. Na bayyana a gare ka don in naɗa ka bawa da kuma mai shaidar abin da ka gani game da ni da kuma abin da zan nuna maka.

  16. Zan tsirar da kai daga mutanenka da kuma daga Al’ummai. Ina aikan ka zuwa gare su domin

  17. ka buɗe idanunsu su kuwa juyo daga duhu zuwa haske, daga mulkin Shaiɗan kuma zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai da kuma matsayi a cikin waɗanda aka tsarkake ta wurin bangaskiya a cikina.’

  18. Sa’ad da aka yanke shawara cewa za mu tashi a jirgin ruwa zuwa Italiya, sai aka danƙa Bulus da waɗansu ’yan kurkuku a hannun wani jarumin mai suna Juliyos, wanda yake na Bataliyar Babban Sarki.

  19. Muka shiga jirgin ruwa daga Andiramitiyum wanda yake shirin tashi zuwa tasoshin da suke bakin tekun lardin Asiya, sai muka kama tafiya. Aristarkus, mutumin Makidoniya daga Tessalonika, yana tare da mu.

  20. Kashegari muka sauka a Sidon; Juliyos kuwa, cikin alheri ga Bulus, ya bar shi yă je wajen abokansa domin su biya masa bukatunsa.

  21. Daga can kuma muka sāke kama tafiya muka zaga ta bayan tsibirin Saifurus saboda iska tana gāba da mu.

  22. Sa’ad da muka ƙetare tekun da yake sassan gaɓar Silisiya da Famfiliya sai muka sauka a Mira ta Lisiya.

  23. A can jarumin ya sami wani jirgin ruwan Alekzandariyan da za shi Italiya sai ya sa mu a ciki.

  24. Tafiyar ta ɗauki kwanaki da yawa muna yi kaɗan-kaɗan da ƙyar muka iso kusa da gaɓar Kinidus. Da iskar ta hana mu ci gaba, sai muka bi ta bayan tsibirin Kirit ɗaura da Salmone.

  25. Muka ci gaba a gefen gaɓar da ƙyar har muka iso wani wurin da ake kira Kyakkyawan Mafaka, kusa da garin Laseya.