Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Parables

452 ayoyi · 74 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ni ban isa a ƙara kira na ɗanka ba. Ka mai da ni kamar ɗaya daga cikin bayinka.” ’

  2. Sai ya tashi ya kama hanya ya koma wurin mahaifinsa. “Amma tun yana nesa, mahaifinsa ya hange shi. Tausayi kuma ya kama shi, sai ya tashi ya ruga da gudu wurinsa, ya rungume shi, ya yi masa sumba.

  3. “Sai ɗan ya ce masa, ‘Baba, na yi wa sama, na kuma yi maka zunubi. Ni ban isa a ƙara kira na ɗanka ba.’

  4. “Amma mahaifin ya ce wa bayinsa, ‘Maza! Ku kawo riga mafi kyau ku sa masa. Ku sa zobe a yatsarsa, da takalma kuma a ƙafafunsa.

  5. Ku kawo ɗan saniya mai ƙiba ku yanka. Bari mu yi biki mu yi shagali.

  6. Gama ɗan nan nawa, da ya mutu, amma yanzu yana da rai kuma. Da ya ɓata, amma yanzu an same shi.’ Sai suka fara shagali.

  7. “Yayinda ake haka, babban ɗan yana gona. Da ya zo kusa da gida, sai ya ji ana kiɗi ana rawa.

  8. Sai ya kira ɗaya daga cikin bayin, ya tambaye shi abin da yake faruwa.

  9. Bawan ya ce, ‘Ai, ɗan’uwanka ne ya dawo, shi ne mahaifinka ya yanka ɗan saniya mai ƙiba, gama ya yi murna ya karɓi ɗansa da ya dawo gida lafiyayye, ba abin da ya same shi.’

  10. “Sai yayan ya yi fushi, ya ƙi shiga gida. Sai mahaifinsa ya fita ya roƙe shi.

  11. Amma ya amsa wa mahaifinsa ya ce, ‘Duba! Duk waɗannan shekaru, ina yin maka aiki kamar bawa, ban taɓa maka rashin biyayya ba. Duk da haka, ba ka taɓa ba ni ko ɗan akuya domin in yi shagali da abokaina ba.

  12. Amma da wannan ɗan naka, wanda ya ɓatar da dukiyarka a kan karuwai ya dawo, ka yanka masa ɗan saniya mai ƙiba!’

  13. “Sai mahaifin ya ce masa, ‘Ɗana, kullum kana nan tare da ni, kuma duk abin da nake da shi, naka ne.

  14. Amma ya zama mana dole, mu yi shagali, mu yi murna, domin ɗan’uwan nan naka, da ya mutu, yanzu kuwa yana da rai, da ya ɓata, amma yanzu an same shi.’ ”

  15. Yesu ya ce wa almajiransa, “An yi wani mai arziki wanda aka yi wa manajansa zargin yin banza da dukiyarsa.

  16. Sai ya kira manajan, ya tambaye shi, ‘Me nake ji haka a kanka? Ka kawo lissafin aikinka, domin ba za ka iya cin gaba da aikinka ba.’

  17. “Sai manajan ya ce cikin tunaninsa, ‘Maigidana zai kore ni daga aiki, me zan yi? Ba ni da ƙarfin noma, kuma ina jin kunyan yin bara.

  18. Na san abin da zan yi, don mutane su karɓe ni a gidajensu, bayan an kore ni daga aiki a nan.’

  19. “Sai ya kira kowane ɗaya da maigidansa yake bin bashi. Ya tambayi na farkon ya ce, ‘Nawa ne maigidana yake bin ka?’

  20. “Ya amsa ya ce, ‘Garwar mai na zaitun guda ɗari tara.’ “Manajan ya ce, ‘Ga takardarka, ka zauna maza ka mai da shi ɗari huɗu.’

  21. “Ya kuma tambayi na biyun, ‘Kai fa, nawa ne ake bin ka?’ “Sai ya amsa ya ce, ‘Buhunan alkama dubu.’ “Ya ce, ‘Ga takardarka, ka mai da shi ɗari takwas.’

  22. “Maigidan kuwa ya yabi manajan nan marar gaskiya saboda wayonsa. Gama ’yan duniyan nan suna da wayon yin hulɗa da junansu fiye da ’yan haske.

  23. “An yi wani mutum mai arziki wanda yakan sa tufafi masu ruwan shunayya, da kuma na lallausan lilin, yana kuma cikin rayuwar jin daɗi kullum.

  24. A ƙofar gidansa kuma akan ajiye wani mai bara, mai suna Lazarus, wanda jikinsa duk gyambuna ne.

  25. Shi kuwa yakan yi marmarin cin abin da yakan fāɗi daga tebur na mai arzikin nan. Har karnuka ma sukan zo su lashe gyambunansa.