Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Parables

452 ayoyi · 74 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Saboda haka ya kira bayinsa goma ya ba su mina goma. Ya ce, ‘Ku yi kasuwanci da kuɗin nan, sai na dawo.’

  2. “Amma talakawansa suka ƙi shi, sai suka aikar da wakilai bayansa, domin su ce, ‘Ba mu son wannan mutum ya zama sarkinmu.’

  3. “Duk da haka, aka naɗa shi sarki, sa’an nan ya dawo gida. Sai ya aika aka kira bayin da ya ba su kuɗin, don yă san ribar da suka samu.

  4. “Na fari ya zo ya ce, ‘Ranka yă daɗe, minarka ya sami ribar goma.’

  5. “Maigidan ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawana mai kirki! Tun da ka yi aminci a kan abu ƙanƙani, ka yi riƙon birane goma.’

  6. “Na biyun ya zo ya ce, ‘Ranka yă daɗe, minarka ya sami ribar biyar.’

  7. “Maigidansa ya ce, ‘Kai ka yi riƙon birane biyar.’

  8. “Sai wani bawan ya zo ya ce, ‘Ranka yă daɗe, ga minarka. Na ɓoye shi a wani ɗan tsumma.

  9. Na ji tsoronka, don kai mai wuyan sha’ani ne. Kakan ɗauki abin da ba ka ajiye ba, kakan kuma yi girbin abin da ba ka shuka ba.’

  10. “Sai maigidansa, ya amsa ya ce, ‘Zan hukunta ka a kan kalmominka, kai mugun bawa! Ashe, ka san cewa ni mai wuyan sha’ani ne, nakan ɗauka abin da ban ajiye ba, ina kuma girbin abin da ban shuka ba?

  11. Don me ba ka sa kuɗina a wajen ajiya, don in na dawo, in sami riba a kai ba?’

  12. “Sai ya ce wa waɗanda suke tsaye a wajen, ‘Ku karɓi minarsa ku ba wa wanda yake da mina goma.’

  13. “Suka ce, ‘Ranka yă daɗe, ai, yana da guda goma ko!’

  14. “Ya amsa ya ce, ‘Ina gaya muku, duk wanda yake da abu, za a ƙara masa. Amma wanda ba shi da shi kuwa, ko abin da yake da shi ma, za a karɓe.

  15. Amma waɗannan abokan gābana, waɗanda ba su so in zama sarkinsu ba, ku kawo su nan, ku karkashe su, a gabana.’ ”

  16. “Gaskiya nake gaya muku, mutumin da bai shiga inda ake ajiye garken tumaki ta ƙofa ba, amma ya hau ta katanga, ɓarawo ne, ɗan fashi kuma.

  17. Mutumin da ya shiga ta ƙofa makiyayin tumakinsa ne.

  18. Mai gadin yakan buɗe wa makiyayin ƙofa, tumakin kuma sukan saurari muryarsa. Yakan kira tumakinsa da suna, yă kuma fid da su waje.

  19. Sa’ad da ya fitar da dukan nasa waje, sai ya ja gabansu, tumakinsa kuma sukan bi shi domin sun san muryarsa.

  20. Amma ba za su taɓa bin baƙo ba; sai dai ma su guje masa don ba su san muryar baƙo ba.”

  21. Yesu ya yi musu wannan misali, amma ba su fahimci abin da yake faɗa musu ba.

  22. “Ni ne kuringar inabi na gaskiya, Ubana kuwa shi ne manomin.

  23. Yakan sare kowane reshe a cikina da ba ya ’ya’ya, amma yakan ƙundume kowane reshe da yake ba da ’ya’ya, domin yă ƙara ba da ’ya’ya.

  24. Kun riga kun zama masu tsabta saboda maganar da na yi muku.

  25. Ku kasance a cikina, ni kuma zan kasance a cikinku. Babu reshen da zai iya yin ’ya’ya da kansa, dole yă kasance a jikin kuringar inabin. Haka ku ma, ba za ku iya ba da ’ya’ya ba sai kun kasance a cikina.