Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Law

175 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. In hidimar da take jawo wa mutane hukunci tana da ɗaukaka haka, to, lalle, hidimar da take kawo adalci za tă fi ta ɗaukaka nesa!

  2. Gama abin da dā take da ɗaukaka, ba ta da ɗaukaka a yanzu, in aka kwatantata da mafificiyar ɗaukaka ta yanzu.

  3. In kuma aba mai shuɗewa ta zo da ɗaukaka, ashe, abin da yake dawwammame, lalle ne yă kasance da ɗaukakar da ta fi haka nesa!

  4. Da yake muna da bege irin wannan, to, muna da ƙarfin zuciya sosai ke nan.

  5. Mu ba kamar Musa ba ne, wanda ya rufe fuskarsa da lulluɓi, don kada Isra’ilawa su ga ƙarewar ɗaukakan nan mai shuɗewa.

  6. Amma aka sa hankulansu suka dushe, gama har yă zuwa yau akwai lulluɓin nan a duk sa’ad da ake karatun tsohon alkawari. Ba a kawar da shi ba, sai a cikin Kiristi ne kaɗai ake kawar da shi.

  7. Amma ko Titus ma da yake tare da ni, ba a ce dole sai ya yi kaciya ba, ko da yake shi mutumin Al’ummai ne.

  8. Wannan zancen kaciya ya taso domin waɗansu ’yan’uwan ƙarya sun shiga cikinmu domin su yi leƙe a kan ’yancin da muke da shi a cikin Kiristi Yesu, su kuma mai da mu bayi.

  9. Ba mu kuwa ba su zarafi ba ko kaɗan, don gaskiyar bishara ta ci gaba da kasance tare da ku.

  10. Game da waɗanda aka ɗauka a dā a kan su wani abu ne, ko wane ne su, duk ɗaya ne a wurina; gama Allah ba ya nuna bambanci, ina dai gaya muku waɗannan da suke wani abu ne a dā, ba su ƙara mini kome ba.

  11. A maimakon haka, sun ga cewa an danƙa mini hakkin wa’azin bishara ga Al’ummai, kamar yadda aka danƙa wa Bitrus ga Yahudawa.

  12. Gama Allah wanda ya yi aiki a cikin hidimar Bitrus a matsayin manzo ga Yahudawa, haka ma ya yi aiki a cikin hidimata a matsayin manzo ga Al’ummai.

  13. Yaƙub, Bitrus da Yohanna waɗanda suke fitattun ginshiƙai, sun karɓe ni da Barnabas da hannu biyu biyu sa’ad da suka gane alherin da aka ba ni. Suka kuma yarda cewa ya kamata mu tafi wajen Al’ummai, su kuwa su tafi wajen Yahudawa.

  14. Amma me Nassi ya ce? Nassi ya ce, “Kori macen nan ’yar aikin gida da ɗanta don ɗan mace ’yar aikin gida ba zai taɓa raba gādo tare da ɗa na ainihin matarka ba.”

  15. Saboda haka, ’yan’uwa, mu ba ’ya’yan mace ’yar aikin gida ba ne, amma na ainihin matan gidan ne.

  16. Ya soke rubutacciyar doka tare da ƙa’idodinta, wadda take gāba da mu, take kuma hamayya da mu; ya kuma kawar da ta, ya kafe ta a kan gicciye.

  17. Bayan ya ƙwace makaman ikoki da hukumomi, ya kunyata su a sarari, ya ci nasara a bisansu ta wurin gicciye.

  18. Saboda haka kada ku bar wani yă shari’anta ku a kan abin da kuke ci ko sha, ko bisa ga abin da ya shafi wani bikin addini, ko Bikin Sabon Wata ko na ranar Asabbaci.

  19. Waɗannan su ne hoton abubuwan da za su zo; amma Kiristi ne ainihinsu.

  20. Kada ku yarda wani yă ɓata ku, cewa shi wani abu ne don yă ga wahayi. Irin mutumin nan yakan nuna ƙasƙancin kai na ƙarya, yă kuma ce yana yi wa mala’iku sujada. Irin mutumin nan yana kumbura kansa ba dalili, sai son zuciya irin na halin mutuntaka.

  21. Ya yanke dangantaka da Kiristi wanda yake kai, wanda ta gare shi ne dukan jiki yake a haɗe, yake tsaye ta wurin taimakon gaɓoɓi da jijiyoyi, yana kuma girma kamar yadda Allah yake sa yă yi girma.

  22. Kun mutu tare da Kiristi. Yanzu ƙa’idodin wannan duniya ba su da iko a kanku. Don me kuke zama har yanzu kamar ku nasu ne? Kuna biyayya da umarnansu cewa,

  23. “Kada ka kama! Kada ka ɗanɗana! Kada ka taɓa”?

  24. Irin waɗannan dokoki suna magana a kan abubuwan da ba sa daɗewa. Su ayyukan mutane ne, sun kuma fito daga koyarwar mutane.

  25. Yin biyayya da irin waɗannan ƙa’idodi za su yi kamar su ne abu mafi kyau da za a yi. Sukan yi kamar suna sa a ƙaunaci Allah sosai a kuma kasance da sauƙinkai a kuma kasance da kamunkai. Amma ba su da wani iko a kan sha’awace-sha’awacenmu.