Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Law: General references

22 ayoyi · 2 fannoni

Ayoyi game da General references

  1. Dokar Ubangiji cikakkiya ce, takan wartsakar da rai. Farillan Ubangiji abin dogara ne, suna mai da hikima da sauƙi.

  2. Ƙa’idodin Ubangiji daidai ne, suna ba da farin ciki ga zuciya. Umarnan Ubangiji haske ne suna ba da haske ga idanu.

  3. Tsoron Ubangiji yakan kawo tsabtar zuciya, zai kasance har abada. Farillan Ubangiji tabbatattu ne, kuma gaba ɗaya masu adalci ne.

  4. Albarka ta tabbata ga waɗanda rayuwarsu ba ta da abin zargi, waɗanda suke tafiya bisa ga dokar Ubangiji.

  5. Albarka ta tabbata ga waɗanda suke kiyaye ƙa’idodinsa suke kuma nemansa da dukan zuciyarsu.

  6. Ba sa yin wani abin da ba daidai ba; suna tafiya a hanyoyinsa.

  7. Ka shimfiɗa farillan da dole a yi biyayya da su.

  8. Kash, da a ce hanyoyina tsayayyu ne a yin biyayya da ƙa’idodinka mana!

  9. Da ba zan sha kunya ba sa’ad da na lura da dukan umarnanka.

  10. Zan yabe ka da zuciya ta gaskiya yayinda nake koyon dokokinka masu adalci.

  11. Zan yi biyayya da ƙa’idodinka; kada ka yashe ni ɗungum.

  12. Duk waɗanda ba sa bin doka yabon mugaye suke yi, amma waɗanda suke yin biyayya da doka suna gāba da mugaye ke nan.

  13. Mugaye ba su san gaskiya ba, amma waɗanda suke neman Ubangiji sun santa sosai.

  14. Daidai ne mu biya haraji ga Kaisar, ko babu?”

  15. Ya gane makircinsu, sai ya ce musu,

  16. “Nuna mini dinari. Hoton wane ne, kuma rubutun wane ne a kai?” Suka amsa, “Na Kaisar.”

  17. Sai ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.”

  18. Tabbatacce, sa’ad da Al’ummai, waɗanda ba su da dokar, suka aikata abubuwan da dokar take bukata, abubuwan sun zama doka ke nan gare su, ko da yake ba su da dokar.

  19. To, da yake sun nuna cewa abubuwan da dokar take bukata suna a rubuce a zukatansu, lamirinsu yana kuma ba da shaida, tunaninsu kuwa yanzu yana zarginsu ko kuma yana kāre su.

  20. Mun san cewa doka tana da kyau in an yi amfani da ita yadda ya kamata.

  21. Mun kuma san cewa an yi doka ba domin masu adalci ba sai dai masu tawaye, da marasa biyayya, da marasa bin Allah, da masu zunubi, da marasa tsarkaka, da masu saɓon Allah, da masu kashe iyaye maza da mata, da masu kisankai,

  22. da masu zina da kuma da maza masu kwana da maza, ko mata masu kwana da mata, da masu cinikin bayi da masu ƙarya da kuma masu shaidar ƙarya, da kuma duk wani abin da ya saɓa wa sahihiyar koyarwa,