Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Law

175 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Dokar Ubangiji cikakkiya ce, takan wartsakar da rai. Farillan Ubangiji abin dogara ne, suna mai da hikima da sauƙi.

  2. Ƙa’idodin Ubangiji daidai ne, suna ba da farin ciki ga zuciya. Umarnan Ubangiji haske ne suna ba da haske ga idanu.

  3. Tsoron Ubangiji yakan kawo tsabtar zuciya, zai kasance har abada. Farillan Ubangiji tabbatattu ne, kuma gaba ɗaya masu adalci ne.

  4. Albarka ta tabbata ga waɗanda rayuwarsu ba ta da abin zargi, waɗanda suke tafiya bisa ga dokar Ubangiji.

  5. Albarka ta tabbata ga waɗanda suke kiyaye ƙa’idodinsa suke kuma nemansa da dukan zuciyarsu.

  6. Ba sa yin wani abin da ba daidai ba; suna tafiya a hanyoyinsa.

  7. Ka shimfiɗa farillan da dole a yi biyayya da su.

  8. Kash, da a ce hanyoyina tsayayyu ne a yin biyayya da ƙa’idodinka mana!

  9. Da ba zan sha kunya ba sa’ad da na lura da dukan umarnanka.

  10. Zan yabe ka da zuciya ta gaskiya yayinda nake koyon dokokinka masu adalci.

  11. Zan yi biyayya da ƙa’idodinka; kada ka yashe ni ɗungum.

  12. Duk waɗanda ba sa bin doka yabon mugaye suke yi, amma waɗanda suke yin biyayya da doka suna gāba da mugaye ke nan.

  13. Mugaye ba su san gaskiya ba, amma waɗanda suke neman Ubangiji sun santa sosai.

  14. “Kada ku yi tsammani na zo ne domin in kawar da Doka ko kuma Annabawa; ban zo domin in kawar da su ba ne, sai dai domin in ciccika su.

  15. Gaskiya nake gaya muku, kafin sama da ƙasa sun shuɗe, babu ko ɗan wasali, babu wani ɗigo ta kowace hanya da zai ɓace daga Dokar, sai an cika kome.

  16. Duk wanda ya karya ɗaya daga cikin mafi ƙanƙanta na umarnan nan, ya kuma koya wa waɗansu su yi haka, za a ce da shi mafi ƙanƙanta a mulkin sama. Amma duk wanda ya aikata, ya kuma koyar da waɗannan umarnai, za a kira shi mai girma a cikin mulkin sama.

  17. Gama ina faɗa muku cewa in dai adalcinku bai fi na Farisiyawa da na malaman dokoki ba, faufau, ba za ku shiga mulkin sama ba.

  18. “Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā cewa, ‘Kada ka yi kisankai;kuma duk wanda ya yi kisankai za a hukunta shi.’

  19. Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da ɗan’uwansa, za a hukunta shi. Kuma duk wanda ya ce wa ɗan’uwansa ‘Raka,’za a kai shi gaban Majalisa. Amma duk wanda ya ce, ‘Kai wawa!’ Zai kasance a hatsarin shiga jahannama ta wuta.

  20. “Saboda haka, in kana cikin ba da baikonka a kan bagade, a can kuwa ka tuna cewa ɗan’uwanka yana riƙe da kai a zuci,

  21. sai ka bar baikonka a can gaban bagade. Ka je ka shirya tukuna da ɗan’uwanka; sa’an nan ka zo ka ba da baikonka.

  22. “Ka yi hanzari ka shirya al’amura da maƙiyinka wanda yake ƙararka a kotu. Ka yi haka, tun kana tare da shi a kan hanya, in ba haka ba, zai miƙa ka ga alƙali, alƙali kuma yă miƙa ka ga ɗan sanda, mai yiwuwa kuwa a jefa ka a kurkuku.

  23. Gaskiya nake gaya maka, ba za ka fita ba, sai ka biya kobo na ƙarshe.

  24. “Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’

  25. Amma ina gaya muku, duk wanda ya dubi mace, sa’an nan ya yi sha’awarta a zuci, ya riga ya yi zina ke nan da ita a zuciyarsa.