Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Law

175 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Tare da su suka aika da wannan wasiƙa. Daga manzanni da dattawa, ’yan’uwanku. Zuwa ga Al’ummai masu bi a Antiyok, Suriya da Silisiya. Gaisuwa.

  2. Mun ji cewa, waɗansu da sun fita daga cikinmu ba tare da izininmu ba suka kuma dame ku, suna tā da hankalinku ta wurin abin da suka ce.

  3. Saboda haka dukanmu mun yarda mu zaɓi waɗansu mutane mu kuma aike su wurinku tare da ƙaunatattun abokanmu Barnabas da Bulus

  4. mutanen da suka sa rayukansu cikin hatsari saboda sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi.

  5. Saboda haka muna aika Yahuda da Sila don su tabbatar muku da baki abin da muka rubuta.

  6. Ya gamshe Ruhu Mai Tsarki da mu ma kada a ɗora muku nauyi fiye da na waɗannan abubuwa.

  7. Ku guji abincin da aka yi wa alloli hadaya, da jini, da naman dabbar da aka murɗe da kuma fasikanci. Za ku kyauta in kun kiyaye waɗannan abubuwa. Ku huta lafiya.

  8. Da suka ji haka, sai suka yabi Allah. Sa’an nan suka ce wa Bulus, “Ka gani ɗan’uwa, yawan dubban Yahudawan da suka gaskata, kuma dukansu masu himma ne a wajen bin doka.

  9. An sanar da su cewa kana koya wa dukan Yahudawan da suke zama a cikin Al’ummai cewa su juye daga Musa, kana kuma faɗa musu kada su yi wa ’ya’yansu kaciya ko su yi rayuwa bisa ga al’adunmu.

  10. To, me za mu yi ke nan? Lalle za su ji cewa ka iso,

  11. saboda haka, ka yi abin da muka faɗa maka. Akwai mutum huɗu tare da mu da suka yi alkawari.

  12. Ka ɗauki waɗannan mutane, ka tafi da su ku tsarkaka gaba ɗaya, ka kuma biya musu kome don su samu su yi aski. Ta haka kowa zai sani babu gaskiya a waɗannan rahotanni game da kai, za a kuma ga cewa kai kanka kana kiyaye dokar.

  13. Game da Al’ummai masu bi kuwa, mun yi musu wasiƙa a kan shawararmu cewa su guji abincin da aka miƙa wa gumaka, da jini, da naman dabbar da aka maƙure da kuma fasikanci.”

  14. Tabbatacce, sa’ad da Al’ummai, waɗanda ba su da dokar, suka aikata abubuwan da dokar take bukata, abubuwan sun zama doka ke nan gare su, ko da yake ba su da dokar.

  15. To, da yake sun nuna cewa abubuwan da dokar take bukata suna a rubuce a zukatansu, lamirinsu yana kuma ba da shaida, tunaninsu kuwa yanzu yana zarginsu ko kuma yana kāre su.

  16. To, mece ce ribar zama mutumin Yahuda, ko kuwa mene ne amfanin kaciya?

  17. Akwai riba ƙwarai ta kowace hanya! Da farko dai, su ne aka danƙa wa kalmomin nan na Allah.

  18. Ba ku sani ba, ’yan’uwa, ina magana ne fa da mutanen da suka san doka, cewa dokar tana da iko a kan mutum muddin yana a raye ne kawai.

  19. Misali, bisa ga doka mace mai aure tana daure ga mijinta muddin mijin yana da rai, amma in mijinta ya mutu, an sake ta ke nan daga dokar aure.

  20. Saboda haka fa, in ta auri wani yayinda mijinta yana raye, za a ce da ita mazinaciya. Amma in mijinta ya mutu, an sake ta ke nan daga wannan doka, ita kuwa ba mazinaciya ba ce, ko da yake ta auri wani.

  21. Saboda haka ’yan’uwana, ku ma kun mutu ga dokar ta wurin jikin Kiristi, domin ku zama na wani, gare shi wanda aka tashe shi daga matattu, don mu ba da amfani ga Allah.

  22. Gama sa’ad da halin mutuntaka yake mulkinmu, sha’awace-sha’awacen zunubi waɗanda dokar ta zuga sun yi ta aiki a jikunanmu, don mu ba da amfani wa mutuwa.

  23. Amma yanzu, ta wurin mutuwa ga abin da dā ya daure mu, an sake mu daga dokar saboda mu yi hidima a sabuwar hanyar Ruhu, ba a tsohuwar hanyar rubutaccen ƙa’ida ba.

  24. To, in hidimar da ta kawo mutuwa, wadda an rubuta a kan allon dutse, ta zo da ɗaukaka har Isra’ilawa suka kāsa duban fuskar Musa saboda tsananin haskenta, ko da yake mai shuɗewa ce,

  25. ashe, hidimar Ruhu ba za tă fi wannan ɗaukaka ba?