Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Anger

72 ayoyi · 38 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ban da haka, maganar Ubangiji ta zo ta wurin annabi Yehu ɗan Hanani wa Ba’asha da gidansa, saboda dukan muguntar da ya aikata a gaban Ubangiji, ya tsokane shi yă yi fushi ta wurin abubuwan da ya yi, da kuma zama kamar gidan Yerobowam, da kuma domin ya hallaka gidan Yerobowam.

  2. A shekara ta ashirin da shida ta Asa sarkin Yahuda, Ela ɗan Ba’asha ya zama sarkin Isra’ila, ya kuma yi mulki a Tirza shekaru biyu.

  3. Zimri, ɗaya daga cikin shugabanni, wanda ya shugabanci rabin kekunan yaƙin Ela, ya yi maƙarƙashiya a kansa. Ela yana a Tirza a lokacin, ya bugu a gidan Arza, sarkin fada a Tirza.

  4. Zimri ya shiga, ya buge shi ya kashe a shekara ta ashirin da bakwai na Asa sarkin Yahuda. Sa’an nan ya gāje shi a matsayin sarki.

  5. Nan da nan sai ya fara mulki ya kuwa zauna a kujerar sarauta, ya kashe dukan iyalin Ba’asha. Bai bar namiji guda ɗaya ba, ko dangi, ko aboki.

  6. Ta haka Zimri ya hallaka dukan iyalin Ba’asha, bisa ga maganar da Ubangiji ya yi game da Ba’asha ta wurin annabi Yehu.

  7. Wannan ya faru saboda dukan zunuban Ba’asha da waɗanda ɗansa Ela ya yi, da ya sa Isra’ila suka yi, har suka tsokane Ubangiji, Allah na Isra’ila, yă yi fushi ta wurin gumakansu marasa amfani.

  8. Ya saki musu fushinsa mai zafi, hasalarsa, zafin rai da kuma ɓacin ransa, ƙungiyar mala’iku masu hallakarwa.

  9. Ya shirya hanya wa fushinsa; bai tsare ransu daga mutuwa ba amma ya miƙa su ga annoba.

  10. Ubangiji mai tausayi ne da kuma alheri, mai jinkirin fushi, cike da ƙauna.

  11. Ba zai yi ta zargi ba ba kuwa zai yi ta jin fushi har abada ba;

  12. Hikimar mutum kan ba shi haƙuri; ɗaukakarsa ce ya ƙyale laifi.

  13. Fushin sarki yana kama da rurin zaki, amma tagomashinsa yana kama da raba a kan ciyawa.

  14. Kada ka yi abokantaka da mai zafin rai, kada ka haɗa kai da wanda ba shi da wuya ya yi fushi,

  15. in ba haka ba za ka koyi hanyoyinsa ka kuma sa kanka a tarko.

  16. Dutse yana da nauyi yashi kuma wahala ce, amma tsokanar wawa ta fi su duka nauyi.

  17. Fushi mugun abu ne mai hallakarwa, amma wa zai iya tsaya a gaban kishi?

  18. Masu ba’a kan kuta faɗa a birni, amma masu hikima sukan kwantar da fushi.

  19. In mai hikima ya je wurin shari’a da wawa, wawa kan yi ta fushi yana ta dariya, ba kuwa za a sami salama ba.

  20. Ba zan tuhume su har abada ba, ba kuwa kullum zai yi fushi ba, gama a haka ruhun mutumin zan yi suma a gabana, shi numfashin mutumin da na halitta.

  21. Na yi fushi saboda kwaɗayin zunubinsa; na yi masa horo, na kuma ɓoye fuskata saboda fushi, duk da haka ya ci gaba da ayyukan zunubinsa.

  22. “Na tattake ’ya’yan inabi ni kaɗai; cikin al’ummai kuma babu wani tare da ni. Na tattake su cikin fushina Na matse su cikin hasalata; jininsu ya fantsamar wa rigunana, na kuma ɓata dukan tufafina.

  23. Gama ranar ɗaukan fansa tana a cikin zuciyata, kuma shekarar fansata ta zo.

  24. Na duba, amma babu wanda zai taimaka, na yi mamaki cewa ba wanda ya goyi baya; saboda haka hannuna ya yi mini ceto, fushina kuma ya rayar da ni.

  25. Na tattake al’ummai cikin fushina; cikin hasalata kuma na sa sun bugu na kuma zub da jininsu a ƙasa.”