Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Anger: General references

13 ayoyi · 38 fannoni

Ayoyi game da General references

  1. Hikimar mutum kan ba shi haƙuri; ɗaukakarsa ce ya ƙyale laifi.

  2. Fushin sarki yana kama da rurin zaki, amma tagomashinsa yana kama da raba a kan ciyawa.

  3. Kada ka yi abokantaka da mai zafin rai, kada ka haɗa kai da wanda ba shi da wuya ya yi fushi,

  4. in ba haka ba za ka koyi hanyoyinsa ka kuma sa kanka a tarko.

  5. Dutse yana da nauyi yashi kuma wahala ce, amma tsokanar wawa ta fi su duka nauyi.

  6. Fushi mugun abu ne mai hallakarwa, amma wa zai iya tsaya a gaban kishi?

  7. Masu ba’a kan kuta faɗa a birni, amma masu hikima sukan kwantar da fushi.

  8. In mai hikima ya je wurin shari’a da wawa, wawa kan yi ta fushi yana ta dariya, ba kuwa za a sami salama ba.

  9. Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke. Wato, fasikanci, ƙazanta da kuma lalata;

  10. bautar gumaka da sihiri; ƙiyayya, faɗa, kishi, fushi mai zafi, sonkai, tsattsaguwa, hamayya,

  11. da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba.

  12. ’Yan’uwana ƙaunatattu, ku lura da wannan. Ya kamata kowa yă kasance mai saurin saurara, ba mai saurin magana ba, ba kuma mai saurin fushi ba,

  13. gama fushin mutum ba ya kawo rayuwar adalcin da Allah yake so.