Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Afflictions and Adversities

526 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. sai ku san cewa Allah ya yi mini ba daidai ba ya kewaye ni da ragarsa.

  2. “Ku tausaya mini, abokaina, ku ji tausayina, gama hannun Allah ya sauko a kaina.

  3. “Duk da haka, sau nawa fitilar mugu take mutuwa? Sau nawa bala’i yake auka masa, ko Allah ya taɓa hukunta mugu cikin fushi?

  4. Amma ya san hanyar da nake bi; sa’ad da ya gwada ni zan fito kamar zinariya.

  5. Allah ya sa zuciyata ta yi sanyi; Maɗaukaki ya tsorata ni.

  6. “Na rantse da Allah mai rai, wanda ya danne mini gaskiyata, Maɗaukaki, wanda ya sa nake cikin ɗacin rai.

  7. Na zaɓar masu inda za su bi na kuma zauna kamar sarkinsu; na zauna kamar sarki a cikin rundunansu; ina nan kamar mai yi wa masu makoki ta’aziyya.

  8. Yanzu da Allah ya kunce bakana ya ba ni wahala sun raba ni da mutuncina.

  9. In da na ga wani yana mutuwa don rashin sutura, ko wani mai bukata da ba shi da riga,

  10. kuma zuciyarsa ba tă gode mini ba don na yi masa sutura da gashin tumakina,

  11. in na ɗaga hannuna don in cuci maraya, domin na san in na faɗa za a ji ni a wurin masu shari’a,

  12. bari hannuna yă guntule daga kafaɗata, bari yă tsinke daga inda aka haɗa shi.

  13. Amma in ya yi shiru, wa zai ba shi laifi? In ya ɓoye fuskarsa, wa zai gan shi? Duk da haka shi yake da iko kan mutum da al’umma duka,

  14. Amma ba wanda ya ce, ‘Ina Allah wanda ya halicce ni, mai ba da waƙoƙi cikin dare,

  15. Ubangiji shi ne mafakan waɗanda ake danniya, mafaka a lokutan wahala.

  16. Waɗanda suka san sunanka za su dogara da kai, gama kai, Ubangiji, ba ka taɓa yashe waɗanda suke nemanka ba.

  17. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da salon “Matar Zomon Safiya.” Zabura ta Dawuda. Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni? Me ya sa ka yi nisa da cetona, ka yi nesa daga kalmomin nishina?

  18. Ya Allahna, na yi kuka da rana, amma ba ka amsa ba, da dare kuma ban yi shiru ba.

  19. Ko da na yi tafiya ta kwari na inuwar mutuwa, ba zan ji tsoron mugu ba, gama kana tare da ni; bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya, za su yi mini ta’aziyya.

  20. Gama a lokacin wahala, zai kiyaye ni lafiya a wurin zamansa; zai ɓoye ni cikin inuwar tabanakul nasa ya kuma sa ni can a bisa dutse.

  21. Sa’an nan kaina zai ɗaukaka a bisa abokan gābana waɗanda suka kewaye ni; a tabanakul nasa zan miƙa hadaya da sowa ta farin ciki; zan rera in kuma yi kiɗi ga Ubangiji.

  22. Gama fushinsa na ɗan lokaci ne amma alherinsa har matuƙa ne; mai yiwuwa a yi kuka da dare amma farin ciki kan zo da safe.

  23. Zan yi murna in kuma yi farin ciki a cikin ƙaunarka, gama ka ga azabata ka kuma san wahalar raina.

  24. Na nemi Ubangiji, ya kuwa amsa mini; ya cece ni daga dukan tsoro.

  25. Adali zai iya kasance da wahala da yawa, amma Ubangiji yakan cece shi daga dukansu;