Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Afflictions and Adversities: Despondency in

28 ayoyi · 5 fannoni

Ayoyi game da Despondency in

Tace bisa littafi
  1. Amma yanzu wahala ta zo maka, sai ka karaya; wahala ta sa ka rikice.

  2. Ko da na yi kira gare shi ya amsa mini, ban yarda cewa zai saurare ni ba.

  3. Zai sa hadari yă danne ni yă ƙara mini ciwona ba dalili.

  4. Ba zai bari in yi numfashi ba, sai dai yă ƙara mini azaba.

  5. In maganar ƙarfi ne, shi babban mai ƙarfi ne! In kuma maganar shari’a ne, wa zai kai kararsa?

  6. Ko da ni marar ƙarfi ne, bakina ya isa yă sa in zama mai laifi; in ba ni da laifi, zai sa in yi laifi.

  7. “Ko da yake ba ni da laifi, ban damu da kaina ba; na rena raina.

  8. Ba bambanci; shi ya sa na ce, ‘Yana hallaka marasa laifi da kuma mugaye.’

  9. Lokacin da bala’i ya kawo ga mutuwa, yakan yi dariyar baƙin cikin marasa laifi.

  10. Lokacin da ƙasa ta faɗa a hannun mugaye, yakan rufe idanun masu shari’a. In ba shi ba wa zai yi wannan?

  11. “Kwanakina sun fi mai gudu wucewa da sauri; suna firiya babu wani abin jin daɗi a cikinsu.

  12. Suna wucewa kamar jirgin ruwan da aka yi da kyauro, kamar jahurma da ta kai wa namanta cafka.

  13. ‘In na ce zan manta da abin da yake damu na, zan yi murmushi in daina nuna ɓacin rai,’

  14. duk da haka ina tsoron duk wahalata, domin na san ba za ka ɗauke ni marar laifi ba.

  15. Tun da an riga an ɗauke ni mai laifi, duk ƙoƙarina a banza yake.

  16. Ko da na wanke jikina duka da sabulu, na wanke hannuwana kuma da soda,

  17. duk da haka za ka jefa ni cikin ƙazamin wuri, yadda ko rigunan jikina ma za su ƙi ni.

  18. “Shi ba mutum ba ne kamar ni wanda zan iya amsa masa, har da za mu yi faɗa da juna a wurin shari’a.

  19. In da akwai wanda zai iya shiga tsakaninmu, ya ɗora hannunsa a kanmu tare,

  20. wani wanda zai sa Allah yă daina duka na, don yă daina ba ni tsoro.

  21. Sa’an nan ne zan iya yin magana ba tare da jin tsoronsa ba, amma a yadda nake a yanzu ba zan iya ba.

  22. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da salon “Matar Zomon Safiya.” Zabura ta Dawuda. Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni? Me ya sa ka yi nisa da cetona, ka yi nesa daga kalmomin nishina?

  23. Ya Allahna, na yi kuka da rana, amma ba ka amsa ba, da dare kuma ban yi shiru ba.

  24. In ba ka da ƙarfi a lokacin wahala, ka tabbatar kai marar ƙarfi ne sosai!

  25. Don mene ne wani mai rai zai yi gunaguni sa’ad da aka ba shi horo domin zunubansa?