Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Afflictions and Adversities

526 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. yakan tsare dukan ƙasusuwansa, ba ko ɗayansu da zai karye.

  2. In Ubangiji ya ji daɗin hanyar da mutum yake bi, zai sa sawu su kahu;

  3. ko ya yi tuntuɓe, ba zai fāɗi ba, gama Ubangiji yakan riƙe shi da hannunsa.

  4. Mugaye suna fako suna jira masu adalci, suna ƙoƙari neman ransu;

  5. amma Ubangiji ba zai bar su a ikonsu ba ko ya bari a hukunta su sa’ad da aka kawo su shari’a ba.

  6. Saboda hasalarka babu lafiya a jikina; ƙasusuwana ba lafiya saboda zunubina.

  7. Ubangiji zai ba shi ƙarfi a gadon rashin lafiyarsa ya mayar masa da lafiya daga ciwon da ya kwantar da shi.

  8. Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina? Me ya sa ka damu a cikina? Ka dogara ga Allah, gama zai sāke yabe shi, Mai Cetona da kuma Allahna.

  9. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’Ya’yan Kora maza. Bisa ga alamot Waƙa ce. Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu, kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala.

  10. ku kira gare ni a ranar wahala; zan cece ku, za ku kuwa girmama ni.”

  11. Ku kawo damuwoyinku ga Ubangiji zai kuwa riƙe ku; ba zai taɓa barin mai adalci yă fāɗi ba.

  12. Ka lissafta makokina; ka jera hawayena a littafinka, ba a rubuce suke a cikin littafinka ba?

  13. Ta haka abokan gābana za su juya da baya sa’ad da na nemi taimako. Ta haka zan san cewa Allah yana tare da ni.

  14. Ga Allah, wanda nake yabon maganarsa, ga Ubangiji, wanda nake yabon maganarsa,

  15. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Yedutun. Zaburar Dawuda. Raina na samun hutu a wurin Allah ne kaɗai; cetona na zuwa daga gare shi.

  16. Shi kaɗai ne dutsena da cetona; shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba.

  17. Ka nemi hutu, ya raina, a wurin Allah kaɗai; dogarata kan zo daga gare shi ne.

  18. Shi ne kaɗai dutsena da cetona; shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba.

  19. Cetona da girmata sun dangana ga Allah ne, shi ne dutsena mai ƙarfi, mafakata.

  20. Ku dogara a gare shi a duk lokuta, ya mutane; ku faɗi albarkaci bakin zukatanku a gare shi, gama Allah ne mafakarmu. Sela

  21. Abu guda Allah ya ce, abubuwa biyu na ji, “Cewa kai, ya Allah, kake mai ƙarfi,

  22. kuma cewa kai, ya Ubangiji, mai ƙauna ne. Tabbatacce za ka sāka wa kowane mutum bisa ga abin da ya yi.”

  23. Ka kawo mu cikin kurkuku ka kuma jibga kaya masu nauyi a bayanmu.

  24. Allah ya shirya masu kaɗaici a cikin iyalai, ya jagorance ’yan kurkuku da waƙoƙi; amma ’yan tawaye suna zama a ƙasa mai zafin rana.

  25. Ba’a ta sa zuciyata ta karai ta bar ni ba mataimaki; Na nemi a ji tausayina, amma ban sami ko ɗaya ba, na nemi masu ta’aziyya, amma ban sami ko ɗaya ba.