Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Afflictions and Adversities

526 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Lokacin yunwa yana tsare ka daga mutuwa, a cikin yaƙi kuma yana kāre ka daga sarar takobi.

  2. Zai kāre ka daga ɓata suna, kuma ba ka bukata ka ji tsoro in hallaka ta zo.

  3. Za ka yi wa hallaka da yunwa dariya; kuma ba ka bukata ka ji tsoron manyan namun jeji.

  4. Gama za ka zauna lafiya da duwatsu a gonaki, kuma manyan namun jeji za su yi zaman salama da kai.

  5. Za ka zauna lafiya a cikin tenti naka, za ka ƙirga kayanka za ka samu kome na nan.

  6. Za ka san cewa ’ya’yanka za su zama da yawa, zuriyarka kuma kamar ciyawa a ƙasa.

  7. Za ka yi kyakkyawan tsufa kafin ka mutu, kamar yadda ake tara dammuna a lokacin girbi.

  8. “Mun yi nazarin wannan, kuma gaskiya ne. Saboda haka ka ji, ka kuma yi amfani da shi.”

  9. Kibiyoyin Maɗaukaki suna a kaina, ruhuna yana shan dafinsa; fushin Allah ya sauka a kaina.

  10. Wane ne ya isa yă hana shi in ya ƙwace abu? Wa zai ce masa, ‘Me kake yi?’

  11. Ko da na yi kira gare shi ya amsa mini, ban yarda cewa zai saurare ni ba.

  12. Zai sa hadari yă danne ni yă ƙara mini ciwona ba dalili.

  13. Ba zai bari in yi numfashi ba, sai dai yă ƙara mini azaba.

  14. In maganar ƙarfi ne, shi babban mai ƙarfi ne! In kuma maganar shari’a ne, wa zai kai kararsa?

  15. Ko da ni marar ƙarfi ne, bakina ya isa yă sa in zama mai laifi; in ba ni da laifi, zai sa in yi laifi.

  16. “Ko da yake ba ni da laifi, ban damu da kaina ba; na rena raina.

  17. Ba bambanci; shi ya sa na ce, ‘Yana hallaka marasa laifi da kuma mugaye.’

  18. Lokacin da bala’i ya kawo ga mutuwa, yakan yi dariyar baƙin cikin marasa laifi.

  19. Lokacin da ƙasa ta faɗa a hannun mugaye, yakan rufe idanun masu shari’a. In ba shi ba wa zai yi wannan?

  20. “Kwanakina sun fi mai gudu wucewa da sauri; suna firiya babu wani abin jin daɗi a cikinsu.

  21. Suna wucewa kamar jirgin ruwan da aka yi da kyauro, kamar jahurma da ta kai wa namanta cafka.

  22. ‘In na ce zan manta da abin da yake damu na, zan yi murmushi in daina nuna ɓacin rai,’

  23. duk da haka ina tsoron duk wahalata, domin na san ba za ka ɗauke ni marar laifi ba.

  24. Tun da an riga an ɗauke ni mai laifi, duk ƙoƙarina a banza yake.

  25. Ko da na wanke jikina duka da sabulu, na wanke hannuwana kuma da soda,