Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Afflictions and Adversities

526 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. in mutanena, waɗanda ake kira da sunana, sun ƙasƙantar da kansu, suka kuma yi addu’a, suka nemi fuskata, suka kuma juye daga mugayen hanyoyinsu, zan ji daga sama in kuma gafarta zunubinsu in kuwa warkar da ƙasarsu.

  2. Yanzu, idanuna za su buɗu, kunnuwata kuma za su saurara ga addu’o’in da aka miƙa a wannan wuri.

  3. Na zaɓi na kuma tsarkake wannan haikali saboda Sunana yă kasance a can har abada. Idanuna da kuma zuciyata kullum za su kasance a can.

  4. “Game da kai kuwa, in ka yi tafiya a gabana kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, ka kuma yi dukan abin da na umarta, ka kiyaye ƙa’idodina da dokokina,

  5. zan kafa kujerar sarautarka, yadda na alkawarta wa Dawuda mahaifinka sa’ad da na ce, ‘Ba za ka taɓa rasa wani mutumin da zai yi mulki a bisa Isra’ila ba.’

  6. “Amma in ka juya daga gare ni ka yashe ƙa’idodi da umarnan da na ba ka, ka yi gaban kanka don ka bauta wa waɗansu alloli ka kuma yi musu sujada,

  7. zan tumɓuke Isra’ila daga ƙasata, wadda na ba su, zan kuma ƙi wannan haikalin da na tsarkake domin Sunana. Zan mai da shi abin karin magana da abin ba’a cikin dukan mutane.

  8. Ko da yake wannan haikali yanzu mai girma ne, dukan wanda ya wuce zai kaɗa kai yă ce, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi irin wannan abu ga wannan ƙasa da kuma ga wannan haikali?’

  9. Mutane za su amsa, ‘Domin sun yashe Ubangiji Allah na kakanninsu, wanda ya fitar da su daga Masar, suka rungumi waɗansu alloli, suna musu sujada, suna bauta musu, shi ya sa ya kawo dukan wannan masifa a kansu.’ ”

  10. ya ce, “Tsirara na fito daga cikin mahaifiyata, tsirara kuma zan koma. Ubangiji ya bayar, Ubangiji kuma ya karɓa; yabo ya tabbata ga Ubangiji.”

  11. Amma yanzu wahala ta zo maka, sai ka karaya; wahala ta sa ka rikice.

  12. Gama ba daga cikin ƙasa wahala take fitowa ba, ko kuma bala’i daga ƙasa.

  13. Duk da haka an haifi mutum don wahala ne, kamar yadda ba shakka tartsatsin wuta yake tashi.

  14. “Amma da a ce ni ne, da zan roƙi Allah; zan gaya masa damuwata.

  15. Yana yin abubuwan al’ajabi waɗanda ba a ganewa, mu’ujizai waɗanda ba a ƙirgawa.

  16. Yana zuba ruwan sama a ƙasa; yana zuba ruwa a gonaki.

  17. Yana ɗaukaka masu sauƙinkai, yana kāre waɗanda suke makoki.

  18. Yana dagula shirye-shiryen masu wayo don kada su yi nasara cikin abubuwan da suke shirin yi.

  19. Yana kama masu wayo cikin wayonsu, yana kawar da shirye-shiryensu ba za su yi nasara ba.

  20. Da rana sukan yi karo da duhu; da rana ma suna lallube kamar a duhun dare suke.

  21. Yana ceton matalauta daga takobin da za tă kashe su da shi; yana cetonsu daga hannun waɗanda suka fi su ƙarfi.

  22. Saboda haka matalauta suna da bege, rashin gaskiya kuma ta yi shiru.

  23. “Mai albarka ne wanda Allah yake yi masa gyara in mutumin ya yi kuskure; saboda haka kada ka guje wa horon Maɗaukaki.

  24. Ko da yake yana sa ciwo, shi ne kuma yake warkar da ciwon; ciwon da ya ji maka, shi da kansa zai warkar da shi.

  25. Zai cece ka daga bala’o’i guda shida; har bakwai ma ba abin da zai same ka.