- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446–1406 BC
The Wilderness Years
Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Maimaitawar Shari’a 2:17kusan 1453 K.H.
sai Ubangiji ya ce mini,
- Maimaitawar Shari’a 2:18kusan 1453 K.H.
“Yau za ku wuce ta yankin Mowab a Ar.
- Maimaitawar Shari’a 2:19kusan 1453 K.H.
Sa’ad da kuka iso kusa da Ammonawa, kada ku dame su, ko ku tsokane su da yaƙi, gama ba zan ba ku mallakar wata ƙasar da take ta Ammonawa ba. Na riga na ba da ita mallaka ga zuriyar Lot.”
- Maimaitawar Shari’a 2:20kusan 1453 K.H.
(Wannan ita ma a ɗauka ta a matsayin ƙasar Refahiyawa waɗanda dā sun zauna a can ne; amma Ammonawa suna ce da su Zamzummawa.
- Maimaitawar Shari’a 2:21kusan 1453 K.H.
Mutane ne masu ƙarfi da kuma yawa, suna kuma da tsayi kamar Anakawa. Ubangiji ya hallaka su daga gaban Ammonawa, waɗanda suka kore su, suka kuma zauna a wurinsu.
- Maimaitawar Shari’a 2:22kusan 1453 K.H.
Ubangiji ya yi daidai yadda ya yi wa zuriyar Isuwa waɗanda suka zauna a ƙasar Seyir, sa’ad da ya hallaka Horiyawa a gabansu. Su kuma suka kore su, suka zauna a wurinsu. Har wa yau, zuriyar Isuwa ne suke zama a can.
- Maimaitawar Shari’a 2:23kusan 1453 K.H.
Kusan abu ɗaya ya faru, sa’ad da Kaftorawa daga ƙasar Kaftor suka hallaka Awwiyawa, waɗanda dā suke zaune a yankin ƙauyukan da suke kewaye da Gaza. Suka zauna a wurinsu.)
- Maimaitawar Shari’a 2:24kusan 1453 K.H.
“Ku fito yanzu ku ƙetare Kwarin Arnon. Duba, na ba da Sihon mutumin Amoriyawa a hannunku, na kuma ba da sarkin Heshbon da ƙasarsa. Ku fara mallake ta, ku kuma yi yaƙi da shi.
- Maimaitawar Shari’a 2:25kusan 1453 K.H.
A wannan rana zan fara sa tsoro da fargabanku a kan dukan al’ummai, a ƙarƙashin sama. Za su ji labarinku, za su yi rawan jiki, su kuma damu saboda ku.”
- Maimaitawar Shari’a 2:26kusan 1453 K.H.
Daga hamadar Kedemot, na aiki ’yan saƙo zuwa wurin Sihon sarkin Heshbon, a kan ina neman zaman lafiya, ina cewa,
- Maimaitawar Shari’a 2:27kusan 1453 K.H.
“Bari mu wuce cikin ƙasarka. Za mu bi ta kan hanya ne kaɗai; ba za mu ratse dama ko hagu ba.
- Maimaitawar Shari’a 2:28kusan 1453 K.H.
Ka sayar mana da abincin da za mu ci, da kuma ruwan da za mu sha a farashinsu na azurfa. Ka dai bar mu mu wuce ta ƙasarka kawai,
- Maimaitawar Shari’a 2:29kusan 1453 K.H.
kamar yadda zuriyar Isuwa, waɗanda suke zaune a Seyir, da Mowabawa, waɗanda suke zaune a Ar, suka yardar mana, gama muna so mu ƙetare Urdun zuwa ƙasa wadda Ubangiji, Allahnmu yake ba mu.”
- Maimaitawar Shari’a 2:30kusan 1453 K.H.
Amma Sihon sarkin Heshbon ya ƙi yă bar mu mu wuce a ciki. Gama Ubangiji Allahnku ya sa ruhunsa ya taurare don yă ba da shi a hannuwanku kamar yadda ya yi yanzu.
- Maimaitawar Shari’a 2:31kusan 1453 K.H.
Ubangiji ya ce mini, “Duba, na fara ba da Sihon da ƙasarsa gare ku. Yanzu ku fara cinta, ku kuma mallake ƙasarsa.”
- Maimaitawar Shari’a 2:32kusan 1453 K.H.
Sa’ad da Sihon da dukan sojojinsa suka fito don su sadu da mu, a yaƙi, a Yahaz,
- Maimaitawar Shari’a 2:33kusan 1453 K.H.
sai Ubangiji Allahnmu ya ba da shi gare mu, muka kuwa buga shi tare da ’ya’yansa maza da kuma dukan sojojinsa.
- Maimaitawar Shari’a 2:34kusan 1453 K.H.
A wannan lokaci mun ci dukan biranensa, muka kuma hallaka su, maza, mata da kuma yara. Ba mu bar wani da rai ba.
- Maimaitawar Shari’a 2:35kusan 1453 K.H.
Amma muka washe, muka kuma kwasa shanu da kuma ganima daga biranen wa kanmu.
- Maimaitawar Shari’a 2:36kusan 1453 K.H.
Ubangiji Allahnmu ya taimake mu muka ci Arower wadda take a gefen Kwarin Arnon, da garin da yake a cikin kwarin, har zuwa Gileyad. Babu garin da ya gaggare mu.
- Maimaitawar Shari’a 2:37kusan 1453 K.H.
Amma bisa ga umarnin Ubangiji Allahnmu, ba ku yi kusa da wata ƙasar Ammonawa, ko ƙasar da take gefen kwarin kogin Yabbok, ko kuwa wadda take kewaye da birane cikin tuddai ba.
- Maimaitawar Shari’a 3:1kusan 1452 K.H.
Biye da wannan muka juya muka haura ta hanyar wajen Bashan, inda Og, sarkin Bashan tare da dukan mayaƙansa suka fito don su sadu da mu a yaƙi, a Edireyi.
- Maimaitawar Shari’a 3:2kusan 1452 K.H.
Ubangiji ya ce mini, “Kada ka ji tsoronsa, gama na riga na miƙa shi da dukan mayaƙansa da kuma ƙasarsa gare ka. Yi masa abin da ka yi wa Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulkin Heshbon.”
- Maimaitawar Shari’a 3:3kusan 1452 K.H.
Saboda haka Ubangiji Allahnmu ya ba da Og, sarkin Bashan da dukan mayaƙansa a hannuwanmu. Muka karkashe su, ba mu bar wani da rai ba.
- Maimaitawar Shari’a 3:4kusan 1452 K.H.
A wannan lokaci muka kwashe dukan biranensa. Babu ɗaya daga birane sittin da ba mu ɗauke daga gare su ba, dukan yankin Argob, masarautar Og a Bashan.