- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 6 BC – AD 30
The Life of Jesus
The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Mattiyu 10:28kusan 33 M.
Kada ku ji tsoron masu kashe jiki amma ba sa iya kashe rai. A maimakon haka, ku ji tsoron Wannan wanda yake da iko yă hallaka rai duk da jiki a jahannama ta wuta.
- Mattiyu 10:29kusan 33 M.
Ba akan sayar da kanari biyu kobo ɗaya ba? Duk da haka ba ɗayansu da zai fāɗi ƙasa ba da yardar Ubanku.
- Mattiyu 10:30kusan 33 M.
Kai, ko gashin kanku ma duk an ƙidaya su.
- Mattiyu 10:31kusan 33 M.
Saboda haka kada ku ji tsoro; kun fi kanari masu yawa, daraja nesa.
- Mattiyu 10:32kusan 33 M.
“Duk wanda ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, ni ma zan bayyana yarda a gare shi a gaban Ubana da yake cikin sama.
- Mattiyu 10:33kusan 33 M.
Amma duk wanda ya yi mūsun sani na a gaban mutane, ni ma zan yi mūsun saninsa a gaban Ubana da yake cikin sama.
- Mattiyu 10:34kusan 33 M.
“Kada fa ku ɗauka na zo ne don in kawo salama a duniya. A’a, ban zo don in kawo salama ba, sai dai takobi.
- Mattiyu 10:35kusan 33 M.
Gama na zo ne in sa, “ ‘gāba tsakanin mutum da mahaifinsa, ’ya da mahaifiyarta, matar ɗa da surukarta,
- Mattiyu 10:36kusan 33 M.
abokan gāban mutum, za su zama mutanen gidansa ne.’
- Mattiyu 10:37kusan 33 M.
“Duk wanda ya fi ƙaunar mahaifinsa ko mahaifiyarsa fiye da ni, bai dace yă zama nawa ba; duk kuwa wanda yake ƙaunar ɗansa ko diyarsa fiye da ni, bai dace yă zama nawa ba;
- Mattiyu 10:38kusan 33 M.
duk wanda kuma bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, bai dace yă zama nawa ba.
- Mattiyu 10:39kusan 33 M.
Duk mai son adana ransa zai rasa shi, duk wanda kuwa ya rasa ransa saboda ni zai same shi.
- Mattiyu 10:40kusan 33 M.
“Wanda ya karɓe ku, ya karɓe ni ne, wanda kuma ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne.
- Mattiyu 10:41kusan 33 M.
Duk wanda ya karɓi annabi don shi annabi ne, zai sami ladar annabi, duk kuwa wanda ya karɓi mutum mai adalci don shi mai adalci ne, zai sami ladar mai adalci.
- Mattiyu 10:42kusan 33 M.
In kuma wani ya ba wa ɗaya daga cikin ƙananan nan ko da kwaf ruwan sanyi ne kan shi almajirina ne, gaskiya nake gaya muku, ba shakka ba zai rasa ladarsa ba.”
- Mattiyu 11:1kusan 31 M.
Bayan Yesu ya gama yi wa almajiransa sha biyun nan umarni, sai ya yi gaba daga can don yă koyar yă kuma yi wa’azi a garuruwan Galili.
- Mattiyu 11:2kusan 31 M.
Sa’ad da Yohanna Mai Baftisma ya ji a kurkuku abin da Kiristi yake yi, sai ya aiki almajiransa
- Mattiyu 11:3kusan 31 M.
su tambaye shi, “Kai ne wanda zai zo, ko kuwa mu sa ido ga wani?”
- Mattiyu 11:4kusan 31 M.
Yesu ya amsa ya ce, “Ku koma ku gaya wa Yohanna abin da kuka ji, kuka kuma gani.
- Mattiyu 11:5kusan 31 M.
Makafi suna gani, guragu suna tafiya, ana warkar da waɗanda suke da kuturta, kurame suna ji, ana tā da matattu, ana kuma yi wa matalauta wa’azin labari mai daɗi.
- Mattiyu 11:6kusan 31 M.
Mai albarka ne mutumin da bai yi tuntuɓe ba saboda ni.”
- Mattiyu 11:7kusan 31 M.
Sa’ad da almajiran Yohanna suke barin wurin, sai Yesu ya fara yi wa taron magana game da Yohanna. “Me kuka je kallo a hamada? Ciyawar da iska take kaɗawa ne?
- Mattiyu 11:8kusan 31 M.
In ba haka ba, to, me kuka je kallo? Mutum mai sanye da riguna masu kyau ne? A’a, masu sa riguna masu kyau, ai, a fadan sarakuna suke.
- Mattiyu 11:9kusan 31 M.
To, me kuka je kallo ne? Annabi? I, ina gaya muku, ya ma fi annabi.
- Mattiyu 11:10kusan 31 M.
Wannan shi ne wanda aka rubuta game da shi cewa, “ ‘Zan aiki ɗan saƙona yă sha gabanka, wanda zai shirya hanyarka a gabanka.’