Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Mattiyu 11:11kusan 31 M.

    Gaskiya nake gaya muku. A cikin dukan waɗanda mata suka haifa, ba wani da ya taso da ya fi Yohanna Mai Baftisma girma; duk da haka mafi ƙanƙanta a mulkin sama ya fi shi girma.

  2. Mattiyu 11:12kusan 31 M.

    Tun daga kwanakin Yohanna Mai Baftisma har yă zuwa yanzu, mulkin sama yana sha da ƙyar, fitanannu kuma sun kama mulkin sama sun riƙe gam.

  3. Mattiyu 11:13kusan 31 M.

    Gama dukan Annabawa da kuma Doka sun yi ta annabci har yă zuwa kan Yohanna.

  4. Mattiyu 11:14kusan 31 M.

    In kuna niyya ku yarda da wannan, to, shi ne Iliya da dā ma zai zo.

  5. Mattiyu 11:15kusan 31 M.

    Duk mai kunnen ji, yă ji.

  6. Mattiyu 11:16kusan 31 M.

    “Da me zan kwatanta wannan zamani? Suna kama da yara da suke zaune a kasuwa, suna kiran juna, suna cewa,

  7. Mattiyu 11:17kusan 31 M.

    “ ‘Mun yi muku busa, ba ku kuwa yi rawa ba, mun rera waƙar makoki, ba ku kuwa yi makoki ba.’

  8. Mattiyu 11:18kusan 31 M.

    Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo ba ya ciye-ciye, ba ya shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ai, yana da aljani.’

  9. Mattiyu 11:19kusan 31 M.

    Ɗan Mutum ya zo yana ciye-ciye, yana shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ga mai haɗama da kuma mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi.’ Amma akan tabbatar da hikima ta wurin ayyukanta.”

  10. Mattiyu 11:20kusan 31 M.

    Sai Yesu ya fara yin tir da biranen da aka yi yawancin ayyukansa na banmamaki, don ba su tuba ba.

  11. Mattiyu 11:21kusan 31 M.

    “Kaitonki, Korazin! Kaitonki, Betsaida! Da a ce ayyukan banmamakin da aka yi a cikinki ne aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba sanye da rigar makoki da toka.

  12. Mattiyu 11:22kusan 31 M.

    Amma ina gaya muku, za a fi jin tausayin Taya da Sidon a ranar shari’a, fiye da ku.

  13. Mattiyu 11:23kusan 31 M.

    Ke kuma Kafarnahum, za a ɗaga ki sama ne? A’a, za ki gangara zuwa zurfafa ne. Da a ce ayyukan banmamakin da aka yi a cikinki ne a aka yi a Sodom, da tana nan har yă zuwa yau.

  14. Mattiyu 11:24kusan 31 M.

    Amma ina gaya miki, za a fi jin tausayin Sodom fiye da ke a ranar shari’a.”

  15. Mattiyu 11:25kusan 31 M.

    A wannan lokaci sai Yesu ya ce, “Ina yabonka, Uba, Ubangijin sama da ƙasa, gama ka ɓoye waɗannan abubuwa ga masu hikima da masu ilimi, ka kuma bayyana su ga ƙananan yara.

  16. Mattiyu 11:26kusan 31 M.

    I, Uba, gama wannan shi ne abin da ka ji daɗin yi.

  17. Mattiyu 11:27kusan 31 M.

    “Dukan kome Ubana ya danƙa mini. Ba wanda ya san Ɗan sai dai Uban, ba kuma wanda ya san Uban, sai dai Ɗan da kuma waɗanda Ɗan ya so yă bayyana musu shi.

  18. Mattiyu 11:28kusan 31 M.

    “Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu.

  19. Mattiyu 11:29kusan 31 M.

    Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku.

  20. Mattiyu 11:30kusan 31 M.

    Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne.”

  21. Mattiyu 12:1kusan 31 M.

    A lokacin nan Yesu ya bi ta gonakin hatsi a ranar Asabbaci. Almajiransa kuwa suna jin yunwa, sai suka fara kakkarya kan hatsi suna ci.

  22. Mattiyu 12:2kusan 31 M.

    Sa’ad da Farisiyawa suka ga wannan, sai suka ce masa, “Duba! Almajiranka suna yin abin da doka ta hana a yi a ranar Asabbaci.”

  23. Mattiyu 12:3kusan 31 M.

    Sai ya amsa ya ce, “Ba ku karanta abin da Dawuda ya yi ba ne sa’ad da shi da abokan tafiyarsa suka ji yunwa?

  24. Mattiyu 12:4kusan 31 M.

    Ya shiga gidan Allah, da shi da abokan tafiyarsa suka ci keɓaɓɓen burodin, wanda doka ta hana su yi, sai firistoci kaɗai.

  25. Mattiyu 12:5kusan 31 M.

    Ko kuwa ba ku karanta a Doka cewa a ranar Asabbaci firistoci sukan karya dokar Asabbaci duk da haka ba da yin wani laifi ba?