circa 6 BC – AD 30
The Life of Jesus
The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Mattiyu 12:6kusan 31 M.
Ina faɗa muku cewa waniwanda ya fi haikali yana a nan.
- Mattiyu 12:7kusan 31 M.
Da a ce kun san abin da waɗannan kalmomi suke nufi, ‘Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba,’da ba ku zargi marar laifi ba.
- Mattiyu 12:8kusan 31 M.
Gama Ɗan Mutum shi ne Ubangijin Asabbaci.”
- Mattiyu 12:9kusan 31 M.
Da ya ci gaba daga wurin, sai ya shiga majami’arsu,
- Mattiyu 12:10kusan 31 M.
a nan kuwa akwai wani mutum mai shanyayyen hannu. Don neman dalili su zargi Yesu, sai suka tambaye shi suka ce, “Ya dace a warkar a ranar Asabbaci?”
- Mattiyu 12:11kusan 31 M.
Ya ce musu, “In waninku yana da tunkiya, ta kuma fāɗa a rami ran Asabbaci, ba zai cire ta daga ramin ba?
- Mattiyu 12:12kusan 31 M.
Sau nawa mutum ya fi tunkiya daraja! Saboda haka ya dace a aikata alheri ran Asabbaci.”
- Mattiyu 12:13kusan 31 M.
Sa’an nan ya ce wa mutumin, “Miƙa hannunka.” Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye, kamar dai ɗayan.
- Mattiyu 12:14kusan 31 M.
Amma Farisiyawa suka fita suka ƙulla shawara yadda za su kashe Yesu.
- Mattiyu 12:15kusan 31 M.
Da ya gane wannan, sai Yesu ya janye daga wurin. Da yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da dukan masu ciwonsu,
- Mattiyu 12:16kusan 31 M.
yana jan musu kunne kada su faɗa wa kowa akan ko shi wane ne.
- Mattiyu 12:17kusan 31 M.
Wannan kuwa domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya ne cewa,
- Mattiyu 12:18kusan 31 M.
“Ga bawana da na zaɓa, ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi; zan sa Ruhuna a kansa, zai kuma yi shelar adalci ga al’ummai.
- Mattiyu 12:19kusan 31 M.
Ba zai yi faɗa ko yă ɗaga murya ba, ba kuwa wanda zai ji muryarsa a kan tituna.
- Mattiyu 12:20kusan 31 M.
Kyauron da ya tanƙwasa ba zai karye shi ba. Fitilar da ta yi kusan mutuwa ba zai kashe ta ba, sai ya jagoranci adalci zuwa ga nasara.
- Mattiyu 12:21kusan 31 M.
Cikin sunansa al’ummai za su dogara.”
- Mattiyu 12:22kusan 31 M.
Sai aka kawo masa wani bebe kuma makaho mai aljani, Yesu kuwa ya warkar da shi, har ya iya magana ya kuma sami ganin gari.
- Mattiyu 12:23kusan 31 M.
Dukan mutane suka yi mamaki, suka ce, “Wannan Ɗan Dawuda ne kuwa?”
- Mattiyu 12:24kusan 31 M.
Amma da Farisiyawa suka ji haka, sai suka ce, “Ahab, da Be’elzebub sarkin aljanu ne kaɗai, wannan mutum yake fitar da aljanu.”
- Mattiyu 12:25kusan 31 M.
Yesu kuwa ya san tunaninsu sai ya ce musu, “Duk mulkin da yake gāba da kansa zai lalace, kuma duk birni ko gidan da yake rabe gāba da kansa ba zai ɗore ba.
- Mattiyu 12:26kusan 31 M.
In Shaiɗan yana fitar da Shaiɗan, ai, ya rabu yana gāba da kansa ke nan. Yaya kuwa mulkinsa zai ɗore?
- Mattiyu 12:27kusan 31 M.
In kuwa ta wurin Be’elzebub nake fitar da aljanu, to, ta wa mutanenku suke fitar da su? Saboda haka, su ne za su zama alƙalanku.
- Mattiyu 12:28kusan 31 M.
Amma in ina fitar da aljanu ta wurin Ruhun Allah ne, to, fa, mulkin Allah ya zo muku ke nan.
- Mattiyu 12:29kusan 31 M.
“Ko kuwa, yaya wani zai iya shiga gidan mai ƙarfi yă ƙwace masa kaya ba tare da ya fara daure mai ƙarfin nan tukuna ba? Sa’an nan zai iya washe gidansa.
- Mattiyu 12:30kusan 31 M.
“Wanda ba ya tare da ni, yana gāba da ni ne, kuma wanda ba ya taya ni tarawa, watsarwa yake yi.