Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Mattiyu 10:3kusan 33 M.

    Filibus da Bartolomeyu; Toma da Mattiyu mai karɓar haraji; Yaƙub ɗan Alfayus da Taddayus;

  2. Mattiyu 10:4kusan 33 M.

    Siman Zilot da kuma Yahuda Iskariyot wanda ya bashe Yesu.

  3. Mattiyu 10:5kusan 33 M.

    Waɗannan sha biyun ne Yesu ya aika da umarni cewa, “Kada ku je cikin Al’ummai, ko kuwa ku shiga wani garin Samariyawa.

  4. Mattiyu 10:6kusan 33 M.

    A maimakon haka ku je wajen ɓatattun tumakin Isra’ila.

  5. Mattiyu 10:7kusan 33 M.

    Sa’ad da kuke tafiya, ku yi wa’azi, kuna cewa, ‘Mulkin sama ya kusato.’

  6. Mattiyu 10:8kusan 33 M.

    Ku warkar da marasa lafiya, ku tā da matattu, ku tsabtacce kutare, ku kuma fitar da aljanu. A kyauta kuka samu, ku kuma bayar a kyauta.

  7. Mattiyu 10:9kusan 33 M.

    “Kada ku riƙe wata zinariya ko azurfa ko jan ƙarfe a aljihunanku,

  8. Mattiyu 10:10kusan 33 M.

    kada ku ɗauki jaka don tafiya, ko ƙarin riga, ko takalma ko sanda; domin ma’aikaci ya cancanci hakkinsa.

  9. Mattiyu 10:11kusan 33 M.

    Kowane gari ko ƙauyen da kuka shiga, ku nemi mai mutunci a wurin, ku kuma zauna a gidansa har sai kun tashi.

  10. Mattiyu 10:12kusan 33 M.

    Da shigarku gidan, ku yi gaisuwa.

  11. Mattiyu 10:13kusan 33 M.

    In gidan na kirki ne, bari salamarku ta zauna a kansa; in kuwa ba mai kirki ba, salamarku ta komo muku.

  12. Mattiyu 10:14kusan 33 M.

    Duk wanda ya ƙi marabtarku ko ya ƙi sauraron kalmominku, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku sa’ad da kuka fita gidan ko garin.

  13. Mattiyu 10:15kusan 33 M.

    Gaskiya nake gaya muku, za a fi jin tausayin Sodom da Gomorra a ranar shari’a fiye da wannan gari.

  14. Mattiyu 10:16kusan 33 M.

    “Ina aikan ku kamar tumaki a cikin kyarketai. Saboda haka ku zama masu wayo kamar macizai, kuma marasa ɓarna kamar kurciyoyi.

  15. Mattiyu 10:17kusan 33 M.

    Ku yi hankali da mutane; za su miƙa ku ga majalisa su kuma yi muku bulala a majami’unsu.

  16. Mattiyu 10:18kusan 33 M.

    Saboda ni, za a ja ku zuwa gaban gwamnoni da gaban sarakuna domin ku ba da shaida a gabansu, da kuma ga Al’ummai.

  17. Mattiyu 10:19kusan 33 M.

    Amma sa’ad da suka kama ku, kada ku damu game da abin da za ku faɗa ko kuwa yadda za ku faɗe shi. A lokacin za a ba ku abin da za ku faɗa,

  18. Mattiyu 10:20kusan 33 M.

    gama ba ku ba ne kuke magana, amma Ruhun Ubanku ne yake magana ta wurinku.

  19. Mattiyu 10:21kusan 33 M.

    “Ɗan’uwa zai ci amanar ɗan’uwansa, a kuma kashe shi, Uba ma zai yi haka da ɗansa; ’ya’ya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su.

  20. Mattiyu 10:22kusan 33 M.

    Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya jure har ƙarshe zai sami ceto.

  21. Mattiyu 10:23kusan 33 M.

    Sa’ad da aka tsananta muku a wannan wuri, ku gudu zuwa wancan. Gaskiya nake gaya muku, kafin ku gama zazzaga dukan biranen Isra’ila, Ɗan Mutum zai zo.

  22. Mattiyu 10:24kusan 33 M.

    “Ɗalibi ba ya fin malaminsa, haka ma, bawa ba ya fin maigidansa.

  23. Mattiyu 10:25kusan 33 M.

    Ya isa wa ɗalibi yă zama kamar malaminsa, haka ma bawa kamar maigidansa. In har an kira wanda yake kan gida Be’elzebub,me za su ce game da mutanen gidansa?

  24. Mattiyu 10:26kusan 33 M.

    “Saboda haka kada ku ji tsoronsu. Ba abin da yake a rufe da ba za a tone ba, ko kuwa a ɓoye da ba za a bayyana ba.

  25. Mattiyu 10:27kusan 33 M.

    Abin da na faɗa muku a asirce, ku faɗe shi a sarari; abin da aka faɗa muku a kunne, ku yi shelarsa daga kan rufin ɗaki.