Tsallake zuwa abun ciki

circa 1380–1050 BC

The Judges & Ruth

Israel cycles through rebellion, oppression, and rescue under charismatic leaders—culminating in Ruth's faithful love story.

703 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Mahukunta 9:56kusan 1233 K.H.

    Ta haka Allah ya sāka muguntar da Abimelek da ya yi wa mahaifinsa ta wurin kisan ’yan’uwansa saba’in.

  2. Mahukunta 9:57kusan 1233 K.H.

    Allah kuma ya sa muguntar mutanen Shekem suka koma kansu. La’anar Yotam ɗan Yerub-Ba’al kuma ta kama su.

  3. Mahukunta 10:1kusan 1232 K.H.

    Bayan zamanin Abimelek, sai Tola ɗan Fuwa ɗan Dodo daga Issakar ya tashi don yă ceci Isra’ila. Yana zama a Shamir a ƙasar tudu ta Efraim.

  4. Mahukunta 10:2kusan 1232 K.H.

    Ya shugabanci Isra’ila shekara ashirin da uku sa’an nan ya mutu, aka kuma binne shi a Shamir.

  5. Mahukunta 10:3kusan 1209 K.H.

    Bayansa kuma sai Yayir daga Gileyad, wanda ya shugabanci Isra’ila shekara ashirin da biyu.

  6. Mahukunta 10:4kusan 1209 K.H.

    Yana ’ya’ya talatin, waɗanda suke hawan jakuna talatin. Sun shugabanci birane talatin a Gileyad, har wa yau ana ce da biranen Hawwot Yayir.

  7. Mahukunta 10:5kusan 1209 K.H.

    Sa’ad da Yayir ya mutu, sai aka binne shi a Kamon.

  8. Mahukunta 10:6kusan 1187 K.H.

    Isra’ilawa suka sāke yin mugayen ayyuka a gaban Ubangiji. Suka shiga bautar Ba’al da Ashtarot, da kuma allolin Aram, allolin Sidon, allolin Mowab, Ammonawa da kuma allolin Filistiyawa. Kuma domin Isra’ilawa sun bar Ubangiji ba su ƙara bauta masa ba,

  9. Mahukunta 10:7kusan 1187 K.H.

    sai ya fusata da su. Ya sayar da su ga hannun Filistiyawa da Ammonawa,

  10. Mahukunta 10:8kusan 1187 K.H.

    waɗanda suka fatattake su a shekarar suka kuma ragargaza su. Shekara goma sha takwas suka yi ta danne dukan Isra’ilawan da suke gabashin Urdun a Gileyad, ƙasar Amoriyawa.

  11. Mahukunta 10:9kusan 1187 K.H.

    Ammonawa su ma suka haye Urdun domin su yi yaƙi da Yahuda, Benyamin da kuma gidan Efraim; Isra’ila kuwa suka kasance cikin wahala ƙwarai da gaske.

  12. Mahukunta 10:10kusan 1187 K.H.

    Sa’an nan Isra’ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, suka ce, “Mun yi maka zunubi, mun bar Allahnmu muka shiga bautar Ba’al.”

  13. Mahukunta 10:11kusan 1187 K.H.

    Ubangiji ya ce, “Sa’ad da Masarawa, Amoriyawa, Ammonawa, Filistiyawa,

  14. Mahukunta 10:12kusan 1187 K.H.

    Sidoniyawa, Amalekawa da kuma mutanen Mawon suka wulaƙanta ku kuka kuwa yi mini kuka, ban cece ku daga hannunsu ba?

  15. Mahukunta 10:13kusan 1187 K.H.

    Amma kuka bar ni kuka bauta wa waɗansu alloli, saboda haka ni ma ba zan ƙara cece ku ba.

  16. Mahukunta 10:14kusan 1187 K.H.

    Ku tafi ku yi wa allolin da kuka zaɓa. Bari su cece ku sa’ad da kuke cikin wahala!”

  17. Mahukunta 10:15kusan 1187 K.H.

    Amma Isra’ilawa suka ce wa Ubangiji, “Mu dai mun yi zunubi. Ka yi da mu abin da ka ga dama, amma muna roƙonka ka cece mu a yanzu.”

  18. Mahukunta 10:16kusan 1187 K.H.

    Sa’an nan suka zubar da allolin nan daga cikinsu suka bauta wa Ubangiji. Ubangiji kuwa bai ƙara daure da azabar da Isra’ila suke sha ba.

  19. Mahukunta 10:17kusan 1187 K.H.

    Sa’ad da aka kira Ammonawa su yi ɗamarar yaƙi, sai su kuma kafa sansani a Gileyad, Isra’ilawa kuwa suka tattaru suka kafa sansani Mizfa.

  20. Mahukunta 10:18kusan 1187 K.H.

    Shugabannin mutanen Gileyad suka cewa juna, “Duk wanda zai fara fāɗa wa Ammonawa shi zai zama shugaban duk waɗanda suke zama a Gileyad.”

  21. Yefta mutumin Gileyad, jarumi ne ƙwarai. Mahaifinsa ne Gileyad; mahaifiyar kuwa karuwa ce.

  22. Matar Gileyad ta haifa masa ’ya’ya maza, kuma sa’ad da suka yi girma, sai suka kore Yefta, suka ce “Ba ka da gādo a cikin iyalinmu, domin kai ɗan wata mace ce.”

  23. Saboda haka Yefta ya tsere daga ’yan’uwansa ya zauna a ƙasar Tob, inda waɗansu ’yan iska suka kewaye shi suka bi shi.

  24. Mahukunta 11:4kusan 1187 K.H.

    Ana nan, sa’ad da Ammonawa suka kai wa Isra’ilawa hari,

  25. Mahukunta 11:5kusan 1187 K.H.

    dattawan Gileyad suka je suka nemo Yefta daga ƙasar Tob.