Tsallake zuwa abun ciki

circa 1380–1050 BC

The Judges & Ruth

Israel cycles through rebellion, oppression, and rescue under charismatic leaders—culminating in Ruth's faithful love story.

703 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Mahukunta 11:31kusan 1187 K.H.

    duk abin da ya fara fitowa daga ƙofar gidana don yă tarye ni, sa’ad da na komo daga yaƙi da Ammonawa, zai zama na Ubangiji, zan miƙa shi hadaya ta ƙonawa.”

  2. Mahukunta 11:32kusan 1187 K.H.

    Sa’an nan Yefta ya haye zuwa wajen Ammonawa don yaƙi da su. Ubangiji kuwa ya ba da su a hannuwansa.

  3. Mahukunta 11:33kusan 1187 K.H.

    Ya hallaka birane ashirin tun daga Arower zuwa yankin Minnit, har zuwa Abel-Keramim. Haka Isra’ila ta cinye Ammonawa ƙaf.

  4. Mahukunta 11:34kusan 1187 K.H.

    Sa’ad da Yefta ya komo gida a Mizfa, wa ya fito yă tarye shi, ’yarsa tilo, tana rawa kiɗin ganguna! Ita ce kaɗai ’yarsa. Ban da ita ba shi da ɗa ko ’ya.

  5. Mahukunta 11:35kusan 1187 K.H.

    Da ya gan ta, sai ya yayyage tufafinsa ya yi kuka ya ce, “Kaito! ’Yata! Kin karya mini gwiwa, kuma na lalace, domin na yi wa’adi ga Ubangiji da ba zan iya in karya ba.”

  6. Mahukunta 11:36kusan 1187 K.H.

    Ta ce, “Mahaifina, idan ka riga ka yi wa Ubangiji magana, sai ka yi da ni yadda ka yi alkawari, da yake Ubangiji ya ɗau maka fansa a kan Ammonawa.”

  7. Mahukunta 11:37kusan 1187 K.H.

    Sai ta kuma ce, “Sai dai, ka biya mini wannan bukata guda. Ka ba ni wata biyu in yi ta yawo da ni da ƙawayena a kan duwatsu mu yi makoki, domin ba zan yi aure ba.”

  8. Mahukunta 11:38kusan 1187 K.H.

    Ya ce mata, “Ki tafi,” Ya bar ta tă tafi har wata biyu. Ita da ’yan matan suka tafi a kan duwatsu suka yi ta makoki domin ba za tă taɓa aure ba.

  9. Mahukunta 11:39kusan 1187 K.H.

    Bayan watanni biyu ɗin sai ta komo wurin mahaifinta ya kuwa yi da ita yadda ya yi wa’adi. Ita kuwa ba tă taɓa san namiji ba. Wannan ya zama al’ada a Isra’ila,

  10. Mahukunta 11:40kusan 1187 K.H.

    cewa kowace shekara ’yan mata sukan fita kwana huɗu don yin bikin tunawa da ’yar Yefta mutumin Gileyad.

  11. Mutanen Efraim suka tattaro mayaƙansu, suka haye zuwa Zafon suka cewa Yefta, “Don me ka tafi ka yaƙi Ammonawa ba ka gayyace mu ba? Za mu ƙone gidanka a kanka.”

  12. Yefta ya ce, “Ni da mutanena mun yi ta jayayya sosai da Ammonawa, ko da yake na kira ku, amma ba ku cece ni daga hannuwansu ba.

  13. Da na ga ba za ku taimake ni ba, sai na yi kasai da raina na kuwa haye don in yaƙi Ammonawa, Ubangiji kuwa ya ba ni nasara a kansu. To, don me kuka zo yau don ku yaƙe ni?”

  14. Sa’an nan Yefta ya tara mutanen Gileyad wuri guda ya kuma yaƙi Efraim. Mutanen Gileyad suka fatattake su domin mutanen Efraim sun ce, “Ku Mutanen Gileyad masu neman mafaka ne cikin Efraim da Manasse.”

  15. Mutanen Gileyad suka ƙwace mashigan Urdun masu zuwa Efraim, duk sa’ad da wani daga Efraim da ya tsira ya ce, “Bari in haye,” sai mutane Gileyad su ce “Kai mutumin Efraim ne?” In ya ce, “A’a,”

  16. sai su ce, “To, ka ce, ‘Shibbolet.’ ” In ya ce, “Sibbolet,” saboda ba sa iya faɗin kalmar daidai, sai su kama shi su kashe a mashigan Urdun. Aka kashe mutanen Efraim dubu arba’in da biyu a ta haka.

  17. Yefta ya shugabanci Isra’ila shekara shida. Sa’an nan Yefta mutumin Gileyad ya mutu, aka kuwa binne shi wani gari a Gileyad.

  18. Bayansa, Ibzan mutumin Betlehem, ya shugabanci Isra’ila.

  19. Yana ’ya’ya maza talatin da ’ya’ya mata talatin. Ya ba da auren ’ya’yansa mata ga waɗanda ba daga dangi ba, ga ’ya’yansa maza kuwa ya kawo ’yan mata talatin su zama matansu waje da danginsa. Ibzan ya shugabanci Isra’ila shekara bakwai.

  20. Sa’an nan Ibzan ya mutu, aka kuwa binne shi Betlehem.

  21. Mahukunta 12:11kusan 1174 K.H.

    Bayansa, Elon mutumin Zebulun, ya shugabanci Isra’ila shekara goma.

  22. Mahukunta 12:12kusan 1174 K.H.

    Sa’an nan Elon ya mutu, aka kuwa binne shi a Aiyalon a ƙasar Zebulun.

  23. Mahukunta 12:13kusan 1164 K.H.

    Bayansa, Abdon ɗan Hillel, daga Firaton, ya shugabanci Isra’ila.

  24. Mahukunta 12:14kusan 1164 K.H.

    Yana da ’ya’ya maza arba’in da ’yan taɓa kunne talatin, waɗanda suka hau jakuna saba’in. Ya shugabanci Isra’ila shekara takwas.

  25. Mahukunta 12:15kusan 1156 K.H.

    Sa’an nan Abdon ɗan Hillel ya mutu, aka kuwa binne shi a Firaton a Efraim, a ƙasar tudu ta Amalekawa.