Tsallake zuwa abun ciki

circa 970–930 BC

Solomon & The Temple

Solomon builds the great Temple in Jerusalem and rules with unprecedented wisdom and wealth before foreign gods divide his heart.

635 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. 1 Sarakuna 6:22kusan 1011 K.H.

    Haka ya dalaye dukan cikin da zinariya. Ya kuma dalaye bagade na cikin wuri mai tsarki da zinariya.

  2. 1 Sarakuna 6:23kusan 1011 K.H.

    A wuri mai tsarki na can ciki, ya yi kerubobi biyu na itacen zaitun, kowanne mai tsayi kamu goma.

  3. 1 Sarakuna 6:24kusan 1011 K.H.

    Fiffike ɗaya na kerub na fari tsawonsa kamu biyar ne, ɗayan fiffike kuma kamu biyar, kamu goma daga ƙarshen fiffike zuwa ƙarshen fiffike.

  4. 1 Sarakuna 6:25kusan 1011 K.H.

    Kerub na biyun shi ma kamu goma ne, gama kerubobi biyun sun yi kama da juna a girma da kuma siffa.

  5. 1 Sarakuna 6:26kusan 1011 K.H.

    Tsayin kowane kerub kamu goma ne.

  6. 1 Sarakuna 6:27kusan 1011 K.H.

    Ya ajiye kerubobin a ɗaki na can cikin haikalin, da fikafikansu a buɗe. Fiffiken kerub ɗaya ya taɓa bango guda, yayinda fiffiken ɗayan ya taɓa ɗayan bangon, kuma fikafikansu sun taɓa juna a tsakiyar ɗakin.

  7. 1 Sarakuna 6:28kusan 1011 K.H.

    Ya dalaye kerubobin da zinariya.

  8. 1 Sarakuna 6:29kusan 1011 K.H.

    A bangaye kewaye da haikali, a ɗakuna ciki da waje, ya zāzzāna kerubobi, itatuwan dabino, da furanni buɗaɗɗu.

  9. 1 Sarakuna 6:30kusan 1011 K.H.

    Ya kuma rufe ƙasan ɗakuna ciki da wajen haikali da zinariya.

  10. 1 Sarakuna 6:31kusan 1011 K.H.

    Don ƙofar shiga wuri mai tsarki na ciki kuwa, ya yi ƙofofin katakon zaitun da madogarai masu gefe biyar.

  11. 1 Sarakuna 6:32kusan 1011 K.H.

    A kan ƙofofin katakan zaitun kuwa ya zāzzāna kerubobi, itatuwa dabino, da furanni buɗaɗɗu, ya kuma dalaye kerubobin, da kuma itatuwan dabinon da zinariya.

  12. 1 Sarakuna 6:33kusan 1011 K.H.

    Haka ma ya yi madogarai masu gefe huɗu na katakon zaitun don ƙofar shiga zuwa babban zaure.

  13. 1 Sarakuna 6:34kusan 1011 K.H.

    Ya yi ƙofofi biyu na itacen fir, kowanne yana da shafi biyu da suke juyewa a maɗaurai.

  14. 1 Sarakuna 6:35kusan 1011 K.H.

    Ya zāzzāna kerubobi, itatuwan dabino, da kuma furanni buɗaɗɗu a kansu, ya kuma dalaye su da zinariyar da aka buga daidai a kan sassaƙa.

  15. 1 Sarakuna 6:36kusan 1011 K.H.

    Ya kuma gina filin ciki da sassaƙaƙƙun duwatsu, jeri uku, da jeri ɗaya na katakan itacen al’ul.

  16. 1 Sarakuna 6:37kusan 1011 K.H.

    An kafa tushen haikalin Ubangiji a shekara ta huɗu, a watan Zif.

  17. 1 Sarakuna 6:38kusan 1011 K.H.

    A shekara ta goma sha ɗaya, a watan Bul, wata na takwas ke nan, aka gama haikalin daidai yadda aka tsara shi bisa ga fasalinsa. Solomon ya ɗauki shekara bakwai yana ginin haikalin.

  18. Ya ɗauki Solomon shekaru goma sha uku kafin yă gama gina fadarsa.

  19. Ya gina fadarsa mai suna Kurmin Lebanon, tsawonsa kamu ɗari, fāɗinsa kamu hamsin, tsayinsa kuma kamu talatin, a bisa jeri huɗu na ginshiƙan itacen al’ul, aka shimfiɗa katakan itacen al’ul a bisa ginshiƙan.

  20. Aka yi rufin da al’ul bisa ginshiƙan da suke bisa ginshiƙai arba’in da biyar, goma sha biya a kowane jeri.

  21. Aka kuma yi tagogi masu sandunan ƙarfe, jeri uku, kowace taga tana ɗaura da ’yar’uwarta, har jeri uku.

  22. Dukan ƙofofin da madogaransu murabba’i ne, taga kuma tana ɗaura da ’yar’uwarta har jeri uku.

  23. Ya yi babban zaure mai ginshiƙai, tsawonsa kamu hamsin, fāɗinsa kuwa kamu talatin. A gabansa kuwa akwai shirayi, kuma a gaban wannan shirayi akwai ginshiƙai da kuma rufin da yake a shimfiɗe.

  24. Ya kuma gina shirayi ta sarauta, da ya kira Zauren Adalci, inda zai riƙa yin shari’a, ya kuma rufe dukan daɓensa da itacen al’ul daga ƙasa har sama.

  25. A fadar da zai zauna kuwa, wadda aka gina a can baya, ya yi ta da irin fasali guda. Solomon ya kuma yi wata fada kamar wannan zaure domin ’yar Fir’auna, wadda ya auro.