- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 970–930 BC
Solomon & The Temple
Solomon builds the great Temple in Jerusalem and rules with unprecedented wisdom and wealth before foreign gods divide his heart.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 2 Tarihi 3:7kusan 1011 K.H.
Ya shafe ginshiƙan saman ɗaki, madogaran ƙofofi, bangaye da kuma ƙofofin haikalin da zinariya, ya sassaƙa kerubobi a bangayen.
- 2 Tarihi 3:8kusan 1011 K.H.
Ya gina Wuri Mafi Tsarki, tsawonsa daidai da fāɗin haikalin. Tsawonsa kamu ashirin, fāɗinsa kuwa kamu ashirin. Ya shafe cikin da talenti ɗari shida na zinariya zalla.
- 2 Tarihi 3:9kusan 1011 K.H.
Nauyin ƙusoshin ya kai shekel hamsin na zinariya. Ya kuma shafe benaye da zinariya zalla.
- 2 Tarihi 3:10kusan 1011 K.H.
Cikin Wuri Mafi Tsarki ya yi kerubobi biyu, ya kuma shafe su da zinariya.
- 2 Tarihi 3:11kusan 1011 K.H.
Tsawon fikafikan kerubobin duka kamu ashirin ne, fiffike ɗaya, kamu biyar, ya taɓo bangon ɗakin, ɗaya fiffiken kuma wanda shi ma kamu biyar ne, ya taɓo fiffiken kerub ɗaya ɗin.
- 2 Tarihi 3:12kusan 1011 K.H.
Haka ma fiffiken kerub na biyu ɗin tsawonsa kamu biyar ne, ya taɓo bangon haikalin, ɗaya fiffiken shi ma tsawonsa kamu biyar ne, ya taɓo fiffiken kerub na farko.
- 2 Tarihi 3:13kusan 1011 K.H.
Tsawon fikafikan kerubobin ya kai kamu ashirin. Su kerubobin a tsaye suke, suna fuskantar babban zauren.
- 2 Tarihi 3:14kusan 1011 K.H.
Sai ya yi labule mai ruwan shuɗi, da shunayya, da garura, da lilin mai kyau, ya kuma ƙunshi hotunan kerubobin da aka saƙa a cikinsa.
- 2 Tarihi 3:15kusan 1011 K.H.
A gaban haikalin ya yi ginshiƙai biyu, waɗanda tsawonsu ya kai kamu talatin da biyar, ya yi wa ginshiƙan dajiya, tsayin kowace dajiya kamu biyar ne.
- 2 Tarihi 3:16kusan 1011 K.H.
Ya saƙa sarƙoƙi, ya kuma sa su a bisa ginshiƙan. Ya kuma yi rumman ɗari ya rataya wa sarƙoƙin.
- 2 Tarihi 3:17kusan 1011 K.H.
Ya kafa ginshiƙan a gaban haikalin, ɗaya a kudu, ɗaya kuma a arewa. Ya kira wanda yake kudun, Yakin, na arewan kuwa ya kira Bowaz.
- 2 Tarihi 4:1kusan 1011 K.H.
Ya yi bagaden tagulla mai tsawo kamu ashirin, fāɗinsa kamu ashirin, tsayinsa kuma kamu goma.
- 2 Tarihi 4:2kusan 1011 K.H.
Ya yi ƙaton kwano mai suna Teku na zubin ƙarfe, mai siffar da’ira, awonsa kamu goma ne daga da’ira zuwa da’ira tsayinsa kuma kamu biyar. Ya ɗauki magwaji mai tsawo kamu talatin ya auna shi kewaye.
- 2 Tarihi 4:3kusan 1011 K.H.
Ƙasa da da’ira kuwa, akwai siffofin bijimai kewaye da ita, goma ga kowane kamu guda. An yi zubin bijiman a jeri biyu a gefe guda na kwatarniya.
- 2 Tarihi 4:4kusan 1011 K.H.
Tekun ya tsaya a kan bijimai goma sha biyu, uku na fuskantar arewa, uku na fuskantar yamma, uku na fuskantar kudu, uku kuma na fuskantar gabas. Tekun ya zauna a kansu, kuma ƙarfafun bayansu suna wajen tsakiya.
- 2 Tarihi 4:5kusan 1011 K.H.
Kaurin ya kai tafin hannu, kuma da’iransa ya yi kama da’irar kwaf, kama furen da ya tohu. Ya riƙe randuna dubu uku.
- 2 Tarihi 4:6kusan 1011 K.H.
Sa’an nan ya yi daruna goma don wanki ya sa biyar a gefen kudu, biyar kuma a gefen arewa. A cikinsu kayan da za a yi amfani don ɗauraye hadayun ƙonawa, amma firistoci suna amfani da ƙaton kwano mai suna Teku don wanki.
- 2 Tarihi 4:7kusan 1011 K.H.
Ya yi wurin ajiye fitila goma na zinariya bisa ga tsari dominsu ya kuma sa su a haikali, biyar a gefen kudu, biyar kuma a gefen arewa.
- 2 Tarihi 4:8kusan 1011 K.H.
Ya yi tebur goma ya kuma sa su cikin haikalin, biyar a gefen kudu, biyar kuma a gefen arewa. Ya kuma yi kwanonin yayyafawa guda ɗari.
- 2 Tarihi 4:9kusan 1011 K.H.
Ya yi fili na firistoci da kuma babban fili da ƙofofi domin filin, ya shafe ƙofofin da tagulla.
- 2 Tarihi 4:10kusan 1011 K.H.
Ya sa ƙaton kwano mai suna Teku a gefen kudu, a kusurwa kudu maso gabas.
- 2 Tarihi 4:11kusan 1011 K.H.
Ya kuma yi tukwane da manyan cokula da kwanonin yayyafawa. Ta haka Huram ya gama aikin da ya yi wa Sarki Solomon a cikin haikalin Allah.
- 2 Tarihi 4:12kusan 1011 K.H.
Ginshiƙai biyu; kwanoni biyu masu siffar kwartaniya a bisa ginshiƙai; jeri biyu na tuƙaƙƙen adon kwanonin yayyafawa masu siffar kwartaniya a bisa ginshiƙai;
- 2 Tarihi 4:13kusan 1011 K.H.
rumman ɗari huɗu don jeri biyu na tuƙaƙƙe (layi biyu na rumman don kowane tuƙaƙƙe, mai adon kwano mai siffar kwartaniya a bisan ginshiƙai);
- 2 Tarihi 4:14kusan 1011 K.H.
dakalai da darunansu;