Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446 BC

Sinai & The Law

God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.

1,657 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Fitowa 22:10kusan 1491 K.H.

    “In mutum ya ba da jaki, ko saniya, ko tunkiya, ko kowace dabba wa maƙwabcinsa ajiya, sai abin ya mutu, ko ya ji rauni, ko an ɗauke shi, in ba shaida,

  2. Fitowa 22:11kusan 1491 K.H.

    rantsuwa ce za tă raba tsakaninsu a gaban Ubangiji cewa babu hannunsa a dukiyar maƙwabcinsa. Mai dukiyar kuwa zai yarda da rantsuwar, ba za a bukaci wanda aka bai wa amanar yă biya ba.

  3. Fitowa 22:12kusan 1491 K.H.

    Amma idan satan dabbar ce aka yi, dole wanda aka bai wa ajiyar yă biya mai dabbar taran da aka ci masa.

  4. Fitowa 22:13kusan 1491 K.H.

    In naman jeji ne ya kashe ta, zai nuna gawar don shaida, ba za a kuwa sa maƙwabcin yă biya abin da naman jeji ya kashe ba.

  5. Fitowa 22:14kusan 1491 K.H.

    “In mutum ya yi aron dabba daga wurin maƙwabcinsa, sai dabbar ta ji rauni ko ta mutu, yayinda mai shi ba ya nan, dole wanda ya yi aron dabbar yă biya.

  6. Fitowa 22:15kusan 1491 K.H.

    Amma idan mai dabbar yana a wurin, wanda ya karɓa aron, ba zai biya kome ba. In an yi hayar dabbar ce, to, kuɗin da aka biya na hayar zai zama a madadin rashin.

  7. Fitowa 22:16kusan 1491 K.H.

    “Idan mutum ya ruɗe budurwa, wadda ba wanda yake nemanta, ya kuma kwanta da ita, dole yă biya kuɗin aurenta, za tă kuma zama matarsa.

  8. Fitowa 22:17kusan 1491 K.H.

    In mahaifinta ya ƙi yă ba da ita ga mutumin, dole mutumin yă biya dukiya daidai da abin da akan biya domin budurwai.

  9. Fitowa 22:18kusan 1491 K.H.

    “Kada ku bar maiya da rai.

  10. Fitowa 22:19kusan 1491 K.H.

    “Duk mutumin da ya yi jima’i da dabba dole a kashe shi.

  11. Fitowa 22:20kusan 1491 K.H.

    “Duk wanda ya yi hadaya ga wani allah ban da Ubangiji, dole a hallaka shi.

  12. Fitowa 22:21kusan 1491 K.H.

    “Kada a wulaƙanta, ko a zalunci baƙo, domin dā ku baƙi ne a ƙasar Masar.

  13. Fitowa 22:22kusan 1491 K.H.

    “Kada ku ci zalin gwauruwa, ko maraya.

  14. Fitowa 22:23kusan 1491 K.H.

    In kuka yi haka, idan kuma suka yi kuka gare ni, zan ji kukansu.

  15. Fitowa 22:24kusan 1491 K.H.

    Zan husata, in kuma kashe ku da takobi; matanku kuma, su ma su zama gwauraye, ’ya’yanku kuwa su zama marayu.

  16. Fitowa 22:25kusan 1491 K.H.

    “In kun ba wa jama’ata matalauta da suke tsakaninku bashin kuɗi, kada ku zama kamar masu ba da rance; kada ku sa yă biya da ruwa.

  17. Fitowa 22:26kusan 1491 K.H.

    In kun ɗauki mayafi maƙwabcinku a matsayin jingina, ku mayar masa kafin fāɗuwar rana,

  18. Fitowa 22:27kusan 1491 K.H.

    domin mayafin ne abin da yake da shi na rufe jikinsa. To, da me zai rufu yă yi barci? Sa’ad da ya yi mini kuka, zan ji, gama ni mai tausayi ne.

  19. Fitowa 22:28kusan 1491 K.H.

    “Kada ku yi maganar saɓo ga Allah, ko ku la’anta mai mulkin mutanenku.

  20. Fitowa 22:29kusan 1491 K.H.

    “Kada ku jinkirta fitar da zakarku daga rumbunanku, ko harajin kayan da kuka saya. “Dole ku ba ni ’ya’yan farinku maza.

  21. Fitowa 22:30kusan 1491 K.H.

    Ku yi haka da shanunku da tumakinku. Bari su kasance da iyayensu mata, har kwana bakwai, amma ku ba ni su a rana ta takwas.

  22. Fitowa 22:31kusan 1491 K.H.

    “Za ku kasance mutanena masu tsarki. Saboda kada ku ci naman da namun jeji suka kashe; ku jefa wa karnuka.

  23. Fitowa 23:1kusan 1491 K.H.

    “Kada ku baza rahoton ƙarya. Kada kuma ku haɗa baki da mugayen mutane har da ku zama munafukai ta wurin ba da shaidar ƙarya.

  24. Fitowa 23:2kusan 1491 K.H.

    “Kada ku yi abin da ba daidai ba, don galibin mutane suna yin haka. Sa’ad da kuke ba da shaida a gaban shari’a, kada ku ba da shaidar ƙarya a kauce wa gaskiya don ku faranta wa taron jama’a rai.

  25. Fitowa 23:3kusan 1491 K.H.

    Kada ku yi wa matalauci sonkai a gaban shari’a.