Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446 BC

Sinai & The Law

God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.

1,657 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Fitowa 23:4kusan 1491 K.H.

    “In ka ga saniyar abokin gābanka, ko jakinsa ya ɓace, ka yi ƙoƙari ka mai da shi wurinsa.

  2. Fitowa 23:5kusan 1491 K.H.

    In ka ga jakin wani maƙiyinka ya fāɗi a ƙarƙashin kayan da ya ɗauka, kada ka bar shi can, ka yi ƙoƙari ka taimake shi.

  3. Fitowa 23:6kusan 1491 K.H.

    “Kada ku kāsa yin adalci ga matalauci a wurin shari’a.

  4. Fitowa 23:7kusan 1491 K.H.

    Ku yi nesa da ƙage. Kada ku kashe marar laifi tare da mai adalci, gama ba zan bar mugun yă tafi haka kawai ba.

  5. Fitowa 23:8kusan 1491 K.H.

    “Kada ka karɓi cin hanci, gama cin hanci yakan makanta waɗanda suke gani, yakan kuma karkatar da maganar masu adalci.

  6. Fitowa 23:9kusan 1491 K.H.

    “Kada ka zalunci baƙo, ku kanku kun san halin baƙunci, gama dā ku baƙi ne a Masar.

  7. Fitowa 23:10kusan 1491 K.H.

    “Shekara shida za ku nome gonakinku ku girbe amfanin gonar,

  8. Fitowa 23:11kusan 1491 K.H.

    amma a shekara ta bakwai za ku bar ƙasa tă huta. Sa’an nan matalautan da suke cikinku za su sami abinci daga cikinta, namun jeji kuma za su ci abin da aka bari. Ku yi haka da gonakinku na inabi, da na itatuwan zaitun.

  9. Fitowa 23:12kusan 1491 K.H.

    “Kwana shida za ku yi aikinku, amma a rana ta bakwai, kada ku yi aiki, saboda saniyarku da jakinku su huta, haka kuma bawan da aka haifa a gidanku, da kuma baƙon da yake a cikinku yă wartsake.

  10. Fitowa 23:13kusan 1491 K.H.

    “Ku mai da hankali, ku yi biyayya da duk abin da na faɗa muku. Kada ku kira sunaye waɗansu alloli; kada a ji su a bakinku.

  11. Fitowa 23:14kusan 1491 K.H.

    “Sau uku a shekara za ku yi mini biki.

  12. Fitowa 23:15kusan 1491 K.H.

    “Ku yi Bikin Burodi Marar Yisti, kwana bakwai za ku ci burodi marar yisti, kamar yadda na umarce ku. Ku yi wannan a lokacin da aka ayana a watan Abib, gama a watan ne kuka fito daga Masar. “Kada wani yă zo a gabana hannu wofi.

  13. Fitowa 23:16kusan 1491 K.H.

    “Ku yi Bikin Girbi da nunan fari na amfanin shuke-shuken gonarku. “Ku yi Bikin Tattarawa a ƙarshen shekara, sa’ad da kuka tattara amfani daga gonarku.

  14. Fitowa 23:17kusan 1491 K.H.

    “Sau uku a shekara, maza duka za su bayyana a gaban Ubangiji Mai Iko Duka.

  15. Fitowa 23:18kusan 1491 K.H.

    “Kada ku miƙa mini hadayar jini tare da wani abu mai yisti. “Ba za a bar kitsen bikin hadayata yă kwana ba.

  16. Fitowa 23:19kusan 1491 K.H.

    “Dole ne ku kawo mafi kyau daga nunan fari na gonakinku a gidan Ubangiji Allahnku. “Kada ku dafa ɗan akuya a cikin madarar mahaifiyarsa.

  17. Fitowa 23:20kusan 1491 K.H.

    “Ga shi, zan aika mala’ika a gabanku, yă tsare ku a tafiyarku, yă kuma kawo ku wurin da na shirya.

  18. Fitowa 23:21kusan 1491 K.H.

    Ku saurare shi, ku kuma kasa kunne ga abin da yake faɗa. Kada ku yi masa tawaye; ba zai gafarta tawayenku ba, gama shi wakilina ne.

  19. Fitowa 23:22kusan 1491 K.H.

    In kun kasa kunne sosai ga abin da yake faɗi, kuka kuma yi abin da na faɗa, zan zama magabci ga abokan gābanku, zan kuma yi hamayya da abokan hamayyanku.

  20. Fitowa 23:23kusan 1491 K.H.

    Mala’ikana zai sha gabanku, yă kawo ku cikin ƙasar Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Kan’aniyawa, da Hiwiyawa, da kuma Yebusiyawa, zan kuma kawar da su.

  21. Fitowa 23:24kusan 1491 K.H.

    Kada ku durƙusa wa allolinsu, ko ku yi musu sujada, ko kuma ku bi al’adunsu. Za ku hallaka dukan allolinsu, ku kuma farfasa keɓaɓɓun duwatsunsu.

  22. Fitowa 23:25kusan 1491 K.H.

    Ku bauta wa Ubangiji Allahnku, albarkansa kuwa za tă kasance a kan abincinku da ruwan shanku. Zan ɗauke cuta daga cikinku.

  23. Fitowa 23:26kusan 1491 K.H.

    A ƙasarku, mace ba za tă yi ɓari ba, ba kuma za a sami marar haihuwa ba. Zan ba ku tsawon rai.

  24. Fitowa 23:27kusan 1491 K.H.

    “Zan aiki razanata a gabanku, in kuma sa ruɗami a cikin kowace al’ummar da za ku sadu da ita. Zan sa duk abokan gābanku su juye da baya, su gudu.

  25. Fitowa 23:28kusan 1491 K.H.

    Zan aiki rina a gabanku, su kori Hiwiyawa, Kan’aniyawa da kuma Hittiyawa.