Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446 BC

Sinai & The Law

God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.

1,657 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Fitowa 25:3kusan 1491 K.H.

    “Ga iri jerin kayan da za ka karɓo daga hannunsu, “zinariya, da azurfa, tagulla,

  2. Fitowa 25:4kusan 1491 K.H.

    shuɗi, shunayya da jan zare, lallausan lilin, da gashin akuya,

  3. Fitowa 25:5kusan 1491 K.H.

    fatun ragunan da aka wanke, fatun awaki masu kyau, itacen akashiya,

  4. Fitowa 25:6kusan 1491 K.H.

    mai domin fitila, kayan yaji domin man keɓewa da kuma turare mai ƙanshi,

  5. Fitowa 25:7kusan 1491 K.H.

    da duwatsun Onis, da duwatsun da za a mammanne a efod da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.

  6. Fitowa 25:8kusan 1491 K.H.

    “Sa’an nan ka sa su yi mini wuri mai tsarki, domin in zauna a cikinsu.

  7. Fitowa 25:9kusan 1491 K.H.

    Ka ƙera wannan tabanakul da duk kayan da suke ciki da waje, daidai yadda zan nuna maka.

  8. Fitowa 25:10kusan 1491 K.H.

    “Ka sa a yi akwatin alkawarin da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kuma kamu ɗaya da rabi.

  9. Fitowa 25:11kusan 1491 K.H.

    Ka dalaye shi da zinariya zalla ciki da waje, za ka yi wa gefe-gefensa ado da gurun zinariya.

  10. Fitowa 25:12kusan 1491 K.H.

    Ka kewaye akwatin da zoban zinariya huɗu ka kuma haɗa su da ƙafafunsa huɗu, zobai biyu a kowane gefe.

  11. Fitowa 25:13kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan ka yi sanduna da itacen ƙirya, ka dalaye su da zinariya.

  12. Fitowa 25:14kusan 1491 K.H.

    Ka sa sandunan a cikin zoban, a gefen akwatin domin ɗaukansa.

  13. Fitowa 25:15kusan 1491 K.H.

    Sanduna za su kasance a cikin waɗannan zoban akwatin alkawarin; ba za a cire su ba.

  14. Fitowa 25:16kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan ka sa Shaidar da zan ba ka, a cikin akwatin.

  15. Fitowa 25:17kusan 1491 K.H.

    “Ka yi murfin kafara da zinariya zalla, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kuma kamu ɗaya da rabi.

  16. Fitowa 25:18kusan 1491 K.H.

    Ka kuma yi kerubobi biyu da zinariyar da aka ƙera, ka sa a gefen nan biyu na murfin.

  17. Fitowa 25:19kusan 1491 K.H.

    Ka yi kerubobi biyu, ɗaya a wannan gefe, ɗaya kuma a ɗayan gefen; za ka manne su a kan murfin, su zama abu ɗaya.

  18. Fitowa 25:20kusan 1491 K.H.

    Kerubobin su kasance da fikafikansu a buɗe, domin su inuwantar da murfin, za su fuskanci juna, suna duba murfin.

  19. Fitowa 25:21kusan 1491 K.H.

    Ka sa murfin a bisa akwatin ka kuma sa allunan dokokin alkawarin da zan ba ka a ciki.

  20. Fitowa 25:22kusan 1491 K.H.

    Can, a bisa murfin da yake tsakanin kerubobi biyu da suke bisa akwatin alkawari na Shaida, zan sadu da kai, in kuma ba ka dukan umarnai domin Isra’ilawa.

  21. Fitowa 25:23kusan 1491 K.H.

    “Ka yi tebur da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu, fāɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa kuma kamu ɗaya da rabi.

  22. Fitowa 25:24kusan 1491 K.H.

    Ka dalaye shi da zinariya zalla ka kuma yi masa ado kewaye da gurun zinariya.

  23. Fitowa 25:25kusan 1491 K.H.

    Ka yi dajiya mai fāɗin tafin hannu, ka kuma yi wa dajiyar ado da gurun zinariya.

  24. Fitowa 25:26kusan 1491 K.H.

    Ka yi zoban zinariya huɗu domin teburin, ka daure su a kusurwoyi huɗu, inda ƙafafu huɗun suke.

  25. Fitowa 25:27kusan 1491 K.H.

    Zoban za su kasance kusa da dajiyar don riƙe sandunan da za a yi amfani don ɗaukar teburin.