Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446 BC

Sinai & The Law

God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.

1,657 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Fitowa 26:13kusan 1491 K.H.

    Tsawon labulen tenti zai zama kamu ɗaya a kowane gefe, abin da ya rage kuma sai a bar shi ya yi ta lilo a kowane gefe don yă rufe tabanakul.

  2. Fitowa 26:14kusan 1491 K.H.

    Ka yi abin rufe tentin da fatun raguna da aka rina ja, a kansa kuma ka rufe shi da fatun shanun teku.

  3. Fitowa 26:15kusan 1491 K.H.

    “Ka yi tabanakul da katakon itacen ƙiryar da aka kakkafa a tsaye.

  4. Fitowa 26:16kusan 1491 K.H.

    Tsawon kowane katako zai zama kamu goma, fāɗinsa kuma kamu ɗaya da rabi,

  5. Fitowa 26:17kusan 1491 K.H.

    ka kafa katakan suna duban juna. Ka yi da dukan katakan tabanakul haka.

  6. Fitowa 26:18kusan 1491 K.H.

    Ka shirya katakai ashirin a gefen kudu na tabanakul,

  7. Fitowa 26:19kusan 1491 K.H.

    ka kuma yi rammuka arba’in da azurfar da za a sa wa katakan nan ashirin. Za a sa kawunan katakan da aka fiƙe a cikin rammukan.

  8. Fitowa 26:20kusan 1491 K.H.

    Game da ɗayan gefen, gefen arewa na tabanakul, za ka kafa katakai ashirin,

  9. Fitowa 26:21kusan 1491 K.H.

    da rammukan azurfa arba’in, biyu a ƙarƙashin kowane katako.

  10. Fitowa 26:22kusan 1491 K.H.

    Ka kafa katakai shida don can ƙarshen katakan, wato, a wajen yamma na ƙarshen tabanakul,

  11. Fitowa 26:23kusan 1491 K.H.

    ka kuma kafa katakai biyu a kusurwoyi can ƙarshe.

  12. Fitowa 26:24kusan 1491 K.H.

    Za a haɗa katakan nan a kusurwa daga ƙasa zuwa sama a daure su. Haka za a yi da katakan kusurwa na biyu.

  13. Fitowa 26:25kusan 1491 K.H.

    Ta haka za a sami katakai takwas da rammukansu na azurfa guda goma sha shida, kowane katako yana da rammuka biyu.

  14. Fitowa 26:26kusan 1491 K.H.

    “Ka kuma yi sanduna da itacen ƙirya. Sanduna biyar domin katakai na gefe ɗaya na tabanakul,

  15. Fitowa 26:27kusan 1491 K.H.

    biyar domin katakai wancan gefe, biyar kuma domin na gefe wajen yamma, can ƙarshen tabanakul.

  16. Fitowa 26:28kusan 1491 K.H.

    Sandan da yake tsakiyar katakan, zai bi daga wannan gefe zuwa ƙarshen wancan gefe.

  17. Fitowa 26:29kusan 1491 K.H.

    Ka dalaye dukan katakan da zinariya, ka kuma yi zoban zinariya don su riƙe sandunan. Ka kuma dalaye sandunan da zinariya.

  18. Fitowa 26:30kusan 1491 K.H.

    “Ka yi tabanakul bisa ga fasalin da aka nuna maka a bisa dutsen.

  19. Fitowa 26:31kusan 1491 K.H.

    “Ka yi labule mai ruwan shuɗi, shunayya da jan zare da kuma lallausan lilin da aka tuƙa, da zānen kerubobin da mai fasaha ya yi.

  20. Fitowa 26:32kusan 1491 K.H.

    Ka rataye shi a bisa dogayen sanduna huɗun nan na itacen ƙirya, waɗanda aka dalaye da zinariya, waɗanda suke tsaya a rammuka huɗu na azurfa.

  21. Fitowa 26:33kusan 1491 K.H.

    Ka rataye labule daga maɗauri, ka sa akwatin alkawari a bayan labulen. Labulen zai raba Wurin Mai Tsarki da Wurin Mafi Tsarki.

  22. Fitowa 26:34kusan 1491 K.H.

    Ka sa murfin kafara a bisa akwatin alkawari a Wuri Mafi Tsarki.

  23. Fitowa 26:35kusan 1491 K.H.

    Ka sa tebur a gaba labulen, a gefen arewa na tabanakul, ka kuma sa wurin ajiye fitilan ɗaura da shi, a wajen kudu.

  24. Fitowa 26:36kusan 1491 K.H.

    “Game da ƙofar shigar tenti kuwa, ka yi labule mai ruwan shuɗi, shunayya da jan zare na lallausan lilin da aka tuƙa, aikin gwani.

  25. Fitowa 26:37kusan 1491 K.H.

    Ka yi ƙugiyoyin zinariya domin wannan labule da katakai itacen ƙirya biyar, waɗanda aka dalaye da zinariya. Ka kuma yi zubi na tagulla biyar dominsu.