Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446 BC

Sinai & The Law

God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.

1,657 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Fitowa 25:28kusan 1491 K.H.

    Ka yi sandunan da itacen ƙirya, ka dalaye su da zinariya, da sandunan ne za ku riƙa ɗaukan teburin.

  2. Fitowa 25:29kusan 1491 K.H.

    Da zinariya zalla kuma za ka yi farantansa, da kwanoninsa na tuya, da butocinsa, da kwanoninsa domin zuban hadayu.

  3. Fitowa 25:30kusan 1491 K.H.

    Ka sa burodin Kasancewa a kan wannan tebur, yă kasance a gabana kullum.

  4. Fitowa 25:31kusan 1491 K.H.

    “Ka yi wurin ajiye fitilar da zinariya zalla, ka kuma yi gindinsa tare da gorar jikinsa da ƙerarriyar zinariya; kwafunansa da suka yi kamar furanni, tohonsa da furanninsa su yi yadda za su zama ɗaya da shi.

  5. Fitowa 25:32kusan 1491 K.H.

    Wurin ajiye fitilar yă kasance da rassa shida, rassan nan za su miƙe daga kowane gefe na wurin ajiye fitilan, uku a gefe guda, uku kuma a ɗaya gefen.

  6. Fitowa 25:33kusan 1491 K.H.

    Kwafuna uku masu siffar furanni almon, da toho, da kuma furannin za su kasance a rashe guda, uku a kan rashe na biye, haka kuma a kan saura rassan shida da suka miƙe daga wurin ajiye fitilan.

  7. Fitowa 25:34kusan 1491 K.H.

    A bisa wurin ajiye fitilan kuwa za a kasance da kwafuna huɗu masu siffar furannin almon, da toho, da furanni.

  8. Fitowa 25:35kusan 1491 K.H.

    Toho ɗaya zai kasance a ƙarƙashin rassa biyu na farkon da suka miƙe daga wurin ajiye fitilan, toho na biyu a ƙarƙashin rassa biyu na biye, toho na uku a ƙarƙashin rassa na uku, rassa shida ke nan duka.

  9. Fitowa 25:36kusan 1491 K.H.

    Tohon da kuma rassan za su kasance ɗaya da wurin ajiye fitilan da aka yi da ƙerarriyar zinariya.

  10. Fitowa 25:37kusan 1491 K.H.

    “Sa’an nan ka yi fitilu bakwai, ka sa su a bisa wurin ajiye fitilan ta yadda za su haskaka wajen da suka fuskanta.

  11. Fitowa 25:38kusan 1491 K.H.

    Za a yi lagwaninsa da manyan farantansa da ƙerarriyar zinariya.

  12. Fitowa 25:39kusan 1491 K.H.

    Da zinariya zalla na talenti ɗaya za ka yi wurin ajiye fitilan da waɗannan abubuwa duka.

  13. Fitowa 25:40kusan 1491 K.H.

    Sai ka lura ka yi su daidai bisa ga fasalin da aka nuna maka a kan dutse.

  14. Fitowa 26:1kusan 1491 K.H.

    “Ka yi tabanakul da labule goma na lilin mai laushi a naɗe shi biyu, a saƙa labulen da ulu mai ruwan shuɗi, da ulu mai ruwan shunayya, da kuma ulu mai ruwan ja. Waɗannan labule za a yi musu zānen siffofin kerubobi, aikin gwani.

  15. Fitowa 26:2kusan 1491 K.H.

    Dukan labulen, girmansu zai zama kamu ashirin da takwas, fāɗinsu kuwa kamu huɗu. Labulen su zama daidai wa daida.

  16. Fitowa 26:3kusan 1491 K.H.

    Ka haɗa labule biyar tare, ka yi haka kuma da suran biyar ɗin.

  17. Fitowa 26:4kusan 1491 K.H.

    Ka sa wa labulen rammuka da ulu mai ruwan shuɗin a gefen ƙarshe na labule ɗaya, a kuma yi haka a ƙarshen gefe na ɗaya kuma.

  18. Fitowa 26:5kusan 1491 K.H.

    Ka yi wa labulen rammuka hamsin a ɗayan labule, ka kuma yi haka a ƙarshe ɗayan labulen, rammukan su fuskanci juna.

  19. Fitowa 26:6kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan ka yi maɗauri hamsin na zinariya don amfanin ɗaura labulen a haɗe, domin tabanakul yă zama ɗaya.

  20. Fitowa 26:7kusan 1491 K.H.

    “Ka yi labule goma sha ɗaya na gashin akuya da za ka rufe tabanakul.

  21. Fitowa 26:8kusan 1491 K.H.

    Tsawon kowanne yă zama kamu talatin, fāɗinsa kuma yă zama kamu huɗu. Labulen za su zama daidai wa daida.

  22. Fitowa 26:9kusan 1491 K.H.

    Ka haɗa labule biyar ka ɗinka. Haka kuma za ka yi da sauran shidan. Ka naɗe shida ɗin biyu, ka yi labulen ƙofar tentin da shi.

  23. Fitowa 26:10kusan 1491 K.H.

    Ka yi rammuka hamsin a ƙarshen gefen kashi ɗaya na labulen, haka kuma a ƙarshen kashi ɗayan.

  24. Fitowa 26:11kusan 1491 K.H.

    Sai ka kuma yi maɗauri hamsin da tagulla, ka ɗaura su a haɗe da tentin su zama ɗaya.

  25. Fitowa 26:12kusan 1491 K.H.

    Ragowar rabin labulen da yake a bisa tenti kuma sai a bar shi yana lilo a bayan tabanakul.