Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446 BC

Sinai & The Law

God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.

1,657 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Fitowa 20:22kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa wannan. ‘Kun gani da kanku cewa na yi magana da ku daga sama.

  2. Fitowa 20:23kusan 1491 K.H.

    Kada ku yi waɗansu alloli in ban da ni, kada ku yi wa kanku allolin azurfa ko na zinariya.

  3. Fitowa 20:24kusan 1491 K.H.

    “ ‘Ku yi mini bagaden ƙasa, ku kuma miƙa mini hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama, za ku hadayar da tumakinku da awakinku da shanu. Duk inda na sa a girmama sunana, zan zo wurinku, in sa muku albarka.

  4. Fitowa 20:25kusan 1491 K.H.

    In kuka yi mini bagade dutse, kada ku gina shi da sassaƙaƙƙun duwatsu, gama inda guduma ta taɓa duwatsun, sun haramtu ke nan.

  5. Fitowa 20:26kusan 1491 K.H.

    Kada ku gina wa bagadena matakala, domin kada yayinda wani yana hawa, mutane su ga tsiraicinsa.’

  6. Fitowa 21:1kusan 1491 K.H.

    “Waɗannan su ne dokokin da za ka sa a gabansu.

  7. Fitowa 21:2kusan 1491 K.H.

    “In ka sayi mutumin Ibraniyawa a matsayin bawa, zai bauta maka shekara shida. Amma a shekara ta bakwai, za ka ’yantar da shi, yă tafi ’yantacce, ba tare da ya biya kome ba.

  8. Fitowa 21:3kusan 1491 K.H.

    In ya zo shi kaɗai, zai tafi ’yantacce shi kaɗai; amma in yana da mata a lokacin da ya zo, za tă tafi tare da shi.

  9. Fitowa 21:4kusan 1491 K.H.

    In maigidansa ya yi masa aure, ta kuwa haifa masa ’ya’ya maza ko mata, matan da ’ya’yan, za su zama na maigidan, sai mutumin kaɗai zai tafi ’yantacce.

  10. Fitowa 21:5kusan 1491 K.H.

    “Amma in bawan ya furta ya ce, ‘Ina ƙaunar maigidana, da matata, da ’ya’yana, ba na so kuma in ’yantu,’

  11. Fitowa 21:6kusan 1491 K.H.

    dole maigidansa yă kai shi gaban alƙalai. Zai kai shi ƙofa ko madogarar ƙofa, yă huda kunnensa da basilla, sa’an nan zai zama bawansa duk tsawon kwanakinsa a duniya.

  12. Fitowa 21:7kusan 1491 K.H.

    “In mutum ya sayar da ’yarsa a matsayin baiwa, ba za a ’yantar da ita kamar bawa ba.

  13. Fitowa 21:8kusan 1491 K.H.

    In ba tă gamshi maigida wanda ya zaɓe ta domin kansa ba, dole yă bari a fanshe ta. Ba shi da dama yă sayar da ita ga baƙi, tun da yake bai kyauta mata ba.

  14. Fitowa 21:9kusan 1491 K.H.

    In ya zaɓe ta domin ɗansa, dole yă ba ta duk damar da ’ya ta mace take da shi.

  15. Fitowa 21:10kusan 1491 K.H.

    In ya auri wata mace, ba zai hana wa baiwar abinci da sutura ba, ba kuma zai ƙi kwana da ita ba.

  16. Fitowa 21:11kusan 1491 K.H.

    In bai tanada mata waɗannan abubuwa uku ba, sai tă tafi ’yantacciya, babu biyan kome.

  17. Fitowa 21:12kusan 1491 K.H.

    “Duk wanda ya bugi mutum har ya kashe shi, lalle a kashe shi.

  18. Fitowa 21:13kusan 1491 K.H.

    Amma in ba da nufin yă kashe shi ba, sai dai in Allah ne ya nufa haka, to, sai mutumin yă tsere zuwa inda zan nuna muku.

  19. Fitowa 21:14kusan 1491 K.H.

    Amma in mutumin ya yi dabara har ya kashe wani mutum da gangan, sai a ɗauke shi daga bagadena a kashe shi.

  20. Fitowa 21:15kusan 1491 K.H.

    “Duk wanda ya bugi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi.

  21. Fitowa 21:16kusan 1491 K.H.

    “Duk wanda ya saci mutum ya sayar da shi, ko kuwa aka iske shi a hannunsa, lalle kashe shi za a yi.

  22. Fitowa 21:17kusan 1491 K.H.

    “Duk wanda ya la’anta mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi.

  23. Fitowa 21:18kusan 1491 K.H.

    “Idan mutane suka yi faɗa, ɗayan ya jefa ɗayan da dutse, ko ya naushe shi amma bai mutu ba, sai dai ya yi ta jiyya,

  24. Fitowa 21:19kusan 1491 K.H.

    idan mutumin ya sāke tashi ya yi tafiya ko da yana dogarawa da sanda ne, wanda ya buge shi zai kuɓuta, sai dai zai biya diyyar lokacin da ya ɓata masa, yă kuma lura da shi, har yă warke sarai.

  25. Fitowa 21:20kusan 1491 K.H.

    “In mutum ya dūke bawansa ko baiwarsa da sanda, sai bawan ko baiwar ta mutu saboda dūkan, dole a hukunta shi,