Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446 BC

Sinai & The Law

God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.

1,657 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Fitowa 18:24kusan 1491 K.H.

    Musa ya kasa kunne ga surukinsa, ya kuma aikata duk abin da ya faɗa.

  2. Fitowa 18:25kusan 1491 K.H.

    Ya zaɓi mutane masu iyawa daga cikin dukan Isra’ila, ya naɗa su shugabannin mutane, shugabanni a kan dubbai, ɗari-ɗari, hamsin-hamsin da goma-goma.

  3. Fitowa 18:26kusan 1491 K.H.

    Suka yi hidimar alƙalanci na mutane a dukan lokaci. Gardandamin da suke da wuya, suka kawo wurin Musa, amma ƙananan batuttuwa, suka shari’anta a tsakaninsu.

  4. Fitowa 18:27kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan Musa ya sallame surukinsa Yetro, ya kuwa koma ƙasarsa.

  5. Fitowa 19:1kusan 1491 K.H.

    A rana ta farko a cikin watan uku bayan da Isra’ilawa suka bar Masar, a wannan rana, suka iso Hamadar Sinai.

  6. Fitowa 19:2kusan 1491 K.H.

    Bayan da suka tashi daga Refidim, suka shiga Hamadar Sinai, sai Isra’ilawa suka yi sansani a gaban dutsen.

  7. Fitowa 19:3kusan 1491 K.H.

    Sai Musa ya hau kan dutsen don yă sadu da Allah, Ubangiji kuwa ya kira shi daga dutsen ya ce, “Wannan shi ne abin da za ka faɗa wa gidan Yaƙub, da kuma abin da za ka faɗa wa mutanen Isra’ila.

  8. Fitowa 19:4kusan 1491 K.H.

    ‘Ku da kanku kun ga abin da na yi wa Masar, da yadda na ɗauko ku a kan fikafikan gaggafa na kawo ku wurina.

  9. Fitowa 19:5kusan 1491 K.H.

    Yanzu, in kuka yi mini cikakken biyayya, kuka kuma kiyaye yarjejjeniyata, to, za ku zama keɓeɓɓiyar taska a gare ni a cikin dukan al’ummai. Ko da yake duk duniya tawa ce,

  10. Fitowa 19:6kusan 1491 K.H.

    za ku zama firistoci masu tsarki da kuma al’umma keɓaɓɓiya a gare ni.’ Waɗannan su ne kalmomin da za ka faɗa wa Isra’ilawa.”

  11. Fitowa 19:7kusan 1491 K.H.

    Sai Musa ya koma ya aika a kira dukan dattawan mutane, ya bayyana dukan kalmomin da Ubangiji ya umarta, ya faɗa.

  12. Fitowa 19:8kusan 1491 K.H.

    Dukan mutane suka amsa gaba ɗaya suka ce, “Za mu yi duk abin da Ubangiji ya faɗa.” Sai Musa ya mayar wa Ubangiji amsar da mutane suka bayar.

  13. Fitowa 19:9kusan 1491 K.H.

    Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Ina zuwa wurinka a cikin baƙin hadari, domin mutane su ji ni ina maganar da kai, domin su amince da kai koyaushe.” Sa’an nan Musa ya faɗa wa Ubangiji abin da mutane suka ce.

  14. Fitowa 19:10kusan 1491 K.H.

    Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Tafi wurin mutanen, ka tsarkake su yau da gobe, ka sa su wanke tufafinsu.

  15. Fitowa 19:11kusan 1491 K.H.

    Su zama da shiri a rana ta uku, gama a ranar ce Ubangiji zai sauko a kan Dutsen Sinai a idon dukan mutane.

  16. Fitowa 19:12kusan 1491 K.H.

    Sai ka yi wa jama’a iyaka kewaye da dutsen, ka kuma faɗa musu cewa, ‘Ku mai da hankali, kada ku hau dutsen ko ku taɓa gefensa. Duk wanda ya taɓa dutsen, lalle za a kashe shi.

  17. Fitowa 19:13kusan 1491 K.H.

    Za a jajjefe shi da duwatsu, ko a harbe shi da kibiyoyi, ba hannun da zai taɓa shi. Mutum ko dabbar da ya taɓa, ba za a bar shi da rai ba.’ Lokacin da aka ji muryar ƙaho ne kawai za su iya taru a gindin dutsen.”

  18. Fitowa 19:14kusan 1491 K.H.

    Bayan da Musa ya gangara wurin mutane, ya tsarkake su, sai suka wanke tufafinsu.

  19. Fitowa 19:15kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan ya ce wa mutane, “Ku shirya kanku domin rana ta uku. Ku ƙame kanku daga yin jima’i.”

  20. Fitowa 19:16kusan 1491 K.H.

    A safiyar rana ta uku, aka yi tsawa, da walƙiyoyi, sai ga girgije mai duhu a bisa dutsen, aka tsananta busar ƙaho, sai dukan jama’ar da suke cikin sansani suka yi rawar jiki.

  21. Fitowa 19:17kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan Musa ya jagoranci mutane daga sansani domin su sadu da Allah, sai suka tsaya a gefen dutsen.

  22. Fitowa 19:18kusan 1491 K.H.

    Dutsen Sinai kuwa ya tunnuƙe duka da hayaƙi, gama Ubangiji ya sauko a bisan dutsen cikin wuta. Hayaƙin ya hau kamar hayaƙin da yake fitowa daga matoya, duk dutsen ya yi rawa da ƙarfi,

  23. Fitowa 19:19kusan 1491 K.H.

    sai karar ƙaho ya yi ta ƙaruwa. Sa’an nan Musa ya yi magana, murya Allah kuwa ta amsa masa.

  24. Fitowa 19:20kusan 1491 K.H.

    Ubangiji ya sauko a kan ƙwanƙolin Dutsen Sinai, ya kira Musa zuwa ƙwanƙolin dutsen. Musa kuwa ya haura

  25. Fitowa 19:21kusan 1491 K.H.

    sai Ubangiji ya ce masa, “Ka sauka ka faɗa wa jama’a, kada su kuskura su ƙetare layin iyakan nan, garin son zuwa don ganin Ubangiji, gama duk waɗanda suka yi haka za su mutu.