- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446 BC
Sinai & The Law
God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Fitowa 17:15kusan 1491 K.H.
Musa ya gina bagade, sai ya kira shi Ubangiji shi ne Tutata.
- Fitowa 17:16kusan 1491 K.H.
Ya ce, “Gama an ɗaga hannuwa sama zuwa kursiyin Ubangiji, Ubangiji zai yaƙi Amalekawa daga tsara zuwa tsara.”
- Fitowa 18:1kusan 1491 K.H.
Ana nan sai Yetro firist na Midiyan, kuma surukin Musa, ya ji duk abin da Allah ya yi wa Musa da mutanensa Isra’ila, da kuma yadda Ubangiji ya fitar da Isra’ila daga Masar.
- Fitowa 18:2kusan 1491 K.H.
Bayan da Musa ya tura matarsa Ziffora gida, sai surukinsa Yetro ya karɓe ta
- Fitowa 18:3kusan 1491 K.H.
da ’ya’yanta biyu maza. Ana kira ɗaya Gershom, domin Musa ya ce, “Na zama baƙo a baƙuwar ƙasa”;
- Fitowa 18:4kusan 1491 K.H.
ɗayan kuma Eliyezer, domin ya ce, “Allah mahaifina ya taimake ni ya cece ni daga takobin Fir’auna.”
- Fitowa 18:5kusan 1491 K.H.
Yetro surukin Musa tare da ’ya’yan Musa da matarsa suka zo wurin Musa a hamada, inda suka kafa sansani kusa da dutsen Allah
- Fitowa 18:6kusan 1491 K.H.
Yetro ya riga ya aika wa Musa cewa, “Ni surukinka Yetro, ina zuwa wurinka tare da matarka da ’ya’yanka maza biyu.”
- Fitowa 18:7kusan 1491 K.H.
Sai Musa ya tafi yă taryi surukinsa, ya sunkuya ya yi masa sumba. Suka gai da juna, sa’an nan suka shiga tenti.
- Fitowa 18:8kusan 1491 K.H.
Musa kuwa ya faɗa wa surukinsa duk abubuwan da Ubangiji ya yi wa Fir’auna da Masarawa domin Isra’ila, da batun wahalolin da suka sha a hanya, da yadda Ubangiji ya cece su.
- Fitowa 18:9kusan 1491 K.H.
Yetro ya yi murna da jin duk abubuwa masu kyau da Ubangiji ya yi wa Isra’ila, wajen cetonsu daga hannun Masarawa.
- Fitowa 18:10kusan 1491 K.H.
“Yabo ga Ubangiji wanda ya cece ku daga hannun Masarawa da na Fir’auna, wanda kuma ya cece mutanensa daga hannun Masarawa.
- Fitowa 18:11kusan 1491 K.H.
Yanzu na san cewa Ubangiji ya fi kowane allah, gama ya yi wannan ga masu girman kai da kuma waɗanda suka wulaƙanta Isra’ila.”
- Fitowa 18:12kusan 1491 K.H.
Sa’an nan Yetro surukin Musa, ya kawo hadaya ta ƙonawa da waɗansu hadayu wa Allah, Haruna ya zo tare da dukan dattawan Isra’ila, suka ci abinci tare da surukin Musa a gaban Allah.
- Fitowa 18:13kusan 1491 K.H.
Kashegari, Musa ya zauna domin yă yi wa mutane shari’a, sai suka tsaya kewaye da shi daga safe har yamma.
- Fitowa 18:14kusan 1491 K.H.
Sa’ad da surukinsa ya lura da duk abin da Musa yake yi saboda mutane, sai ya ce, “Mene ne wannan da kake yi wa mutane? Don me kai kaɗai kake zama kana yin shari’a wa mutane, yayinda mutanen nan suke tsaya kewaye da kai daga safe har yamma?”
- Fitowa 18:15kusan 1491 K.H.
Musa ya amsa ya ce, “Saboda mutanen suna zuwa wurina, don su nemi nufin Allah.
- Fitowa 18:16kusan 1491 K.H.
Duk lokacin da suke da gardama, akan kawo su a wurina, ni kuma sai in raba tsakaninsu, in kuma koya musu dokokin Allah da farillansa.”
- Fitowa 18:17kusan 1491 K.H.
Surukin Musa ya amsa ya ce, “Abin da kake yi ba daidai ba ne.
- Fitowa 18:18kusan 1491 K.H.
Kai da dukan mutanen da suke zuwa wurinka za ku gajiyar da kanku. Aikin ya fi ƙarfinka; ba za ka iya yinsa kai kaɗai ba.
- Fitowa 18:19kusan 1491 K.H.
Ka kasa kunne gare ni yanzu, zan ba ka shawara, Allah kuma yă kasance tare da kai. Kai za ka zama wakilin mutane a gaban Allah, ka kuma kawo gardamansu gare shi.
- Fitowa 18:20kusan 1491 K.H.
Ka koya musu dokokinsa da farillarsa, ka kuma nuna musu hanyar rayuwa da ayyukan da za su yi.
- Fitowa 18:21kusan 1491 K.H.
Amma ka zaɓi mutane masu iyawa daga dukan mutane, maza masu tsoron Allah, amintattu, masu ƙin rashawa, ka sanya su shugabanni na dubbai, ɗari-ɗari, hamsin-hamsin da goma-goma.
- Fitowa 18:22kusan 1491 K.H.
Bari waɗannan mutane su sassanta mutane a kan ƙananan matsaloli, amma kowace babban matsala, ko bukata ta musamman, sai su kawo wurinka, ƙananan matsaloli kuma sai su yanke hukuncin da kansu. Ta haka ne za su taimaka wajen ɗaukan nauyin jama’a, don su sa aikin yă zama maka da sauƙi.
- Fitowa 18:23kusan 1491 K.H.
In ka yi haka, Allah ya umarta za ka iya jimre gajiyar, kuma dukan mutanen nan za su koma gida da murna.”