Skip to content

Hur

12 ayoyi · 25 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Hur

  1. Sai Yoshuwa ya yaƙi Amalekawa kamar yadda Musa ya umarta, Musa, Haruna da Hur kuwa suka tafi bisa tudu.

  2. Sa’ad da hannuwan Musa suka gaji, sai Haruna da Hur suka ɗauki dutse suka sa ya zauna a kai. Sa’an nan su kuma suka tsaya gefe da gefe, suna riƙe da hannuwansa har fāɗuwar rana.

  3. Ya ce wa dattawan, “Ku jira mu a nan, sai mun dawo wurinku. Haruna da Hur suna tare da ku, in wani yana da wata damuwa, sai yă je wurinsu.”

  4. “Duba, na zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuda,

  5. Sa’an nan ya ce wa Isra’ilawa, “Duba Ubangiji ya zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, daga kabilar Yahuda,

  6. (Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuda, ya yi dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa;

  7. Da Azuba ta mutu, Kaleb ya auri Efrat, wadda ta haifa masa Hur.

  8. Hur shi ne mahaifin Uri, Uri kuma shi ne mahaifin Bezalel.

  9. Waɗannan su ne zuriyar Kaleb. ’Ya’yan Hur maza, ɗan farin Efrata su ne, Shobal mahaifin Kiriyat Yeyarim,

  10. Zuriyoyin Yahuda su ne, Ferez, Hezron, Karmi, Hur da Shobal.

  11. Fenuwel shi ne mahaifin Gedor, kuma Ezer shi ne mahaifin Husha. Waɗannan su ne zuriyar Hur, ɗan farin Efrata da mahaifin Betlehem.

  12. Amma bagaden tagullar da Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, ya yi a Gibeyon a gaba tabanakul na Ubangiji; saboda haka Solomon da taron suka neme nufin Ubangiji a can.