- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446 BC
Sinai & The Law
God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Fitowa 19:22kusan 1491 K.H.
Ko firistocin da za su kusato Ubangiji sai su tsarkake kansu, don kada in hallaka su.”
- Fitowa 19:23kusan 1491 K.H.
Musa ya ce wa Ubangiji, “Mutanen ba za su hau Dutsen Sinai ba, gama kai da kanka ka gargaɗe mu, ‘Ku sa iyaka kewaye da dutsen ku kuma tsarkake shi.’ ”
- Fitowa 19:24kusan 1491 K.H.
Ubangiji ya amsa, “Sauka ka kawo Haruna tare da kai. Amma kada firistoci da mutane su zarce iyakan nan, a kan za su zo wurin Ubangiji, don kada in hallaka su.”
- Fitowa 19:25kusan 1491 K.H.
Saboda haka Musa ya sauka wurin mutane ya kuma faɗa musu.
- Fitowa 20:1kusan 1491 K.H.
Sai Allah ya faɗi waɗannan kalmomi ya ce,
- Fitowa 20:2kusan 1491 K.H.
“Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta.
- Fitowa 20:3kusan 1491 K.H.
“Ba za ka yi wa kanka waɗansu alloli ba sai ni.
- Fitowa 20:4kusan 1491 K.H.
Ba za ka yi wa kanka waɗansu alloli a siffar wani abu a sama a bisa, ko a ƙarƙashin ƙasa, ko a ƙarƙashin ruwa ba.
- Fitowa 20:5kusan 1491 K.H.
Ba za ka durƙusa gare su, ko ka yi musu sujada ba. Gama ni, Ubangiji Allahnka mai kishi ne, nakan hukunta ’ya’ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina,
- Fitowa 20:6kusan 1491 K.H.
amma ina nuna ƙauna ga tsara dubbai na waɗanda suke ƙaunata, suke kuma kiyaye umarnaina.
- Fitowa 20:7kusan 1491 K.H.
Ba za ka yi amfani da sunan Ubangiji Allahnka a banza ba, gama Ubangiji zai hukunta duk wanda ya mai da sunansa banza.
- Fitowa 20:8kusan 1491 K.H.
Ka tuna da ranar Asabbaci domin ka kiyaye ta da tsarki.
- Fitowa 20:9kusan 1491 K.H.
Kwana shida za ka yi dukan aikinka,
- Fitowa 20:10kusan 1491 K.H.
amma rana ta bakwai Asabbaci ne ga Ubangiji, Allahnka. A ranar ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko ’yarka, ko bawa, ko baiwa, ko dabbarka, ko baƙon da yake zama tare da kai.
- Fitowa 20:11kusan 1491 K.H.
Gama kwana shida Ubangiji ya halicci sama da ƙasa, da teku, da duk abin da yake cikinsu, amma ya huta a rana ta bakwai. Saboda haka Ubangiji ya albarkaci ranar Asabbaci, ya kuma mai da ita mai tsarki.
- Fitowa 20:12kusan 1491 K.H.
Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.
- Fitowa 20:13kusan 1491 K.H.
Ba za ka yi kisankai ba.
- Fitowa 20:14kusan 1491 K.H.
Ba za ka yi zina ba.
- Fitowa 20:15kusan 1491 K.H.
Ba za ka yi sata ba.
- Fitowa 20:16kusan 1491 K.H.
Ba za ka ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinka ba.
- Fitowa 20:17kusan 1491 K.H.
Ba za ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka ba. Ba za ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka ba, ko bawansa, ko baiwarsa, ko sansa, ko jakinsa, ko duk abin da yake na maƙwabcinka ba.”
- Fitowa 20:18kusan 1491 K.H.
Da mutane suka ga tsawa da walƙiya, suka ji karar ƙaho, suka kuma ga dutsen yana hayaƙi, sai suka yi rawar jiki don tsoro. Suka tsaya da nisa
- Fitowa 20:19kusan 1491 K.H.
suka ce wa Musa, “Ka yi magana da mu da kanka, za mu kasa kunne. Amma kada Allah ya yi mana magana, don kada mu mutu.”
- Fitowa 20:20kusan 1491 K.H.
Musa ya ce wa mutane, “Kada ku ji tsoro, gama Allah ya zo don yă gwada ku, don ku riƙa girmama shi, don kuma kada ku yi zunubi.”
- Fitowa 20:21kusan 1491 K.H.
Sa’ad da mutane suka tsattsaya da nesa, sai Musa ya matsa kusa da girgije mai duhu, inda Allah yake.