- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 48–96
Letters to the Churches
Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ibraniyawa 5:1kusan 64 M.
Akan zaɓi kowane babban firist daga cikin mutane ne, akan kuma naɗa shi domin yă wakilce su a kan al’amuran Allah, domin yă miƙa kyautai da hadayu saboda zunubai.
- Ibraniyawa 5:2kusan 64 M.
Da yake babban firist ɗin mai kāsawa ne, yana iya bin da jahilai da kuma waɗanda suka kauce hanya, a hankali.
- Ibraniyawa 5:3kusan 64 M.
Shi ya sa dole yă miƙa hadayu domin zunubansa, da kuma domin zunuban mutane.
- Ibraniyawa 5:4kusan 64 M.
Ba wanda yakan kai kansa a wannan matsayi mai girma; sai ko Allah ya kira shi, kamar yadda aka yi wa Haruna.
- Ibraniyawa 5:5kusan 64 M.
Haka ma Kiristi bai kai kansa neman ɗaukaka na zama babban firist ba. Allah ne dai ya ce masa, “Kai Ɗana ne; yau na zama Uba a gare ka.”
- Ibraniyawa 5:6kusan 64 M.
Ya kuma ya ce a wani wuri, “Kai firist ne na har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.”
- Ibraniyawa 5:7kusan 64 M.
A lokacin da Yesu ya yi rayuwa a duniya, ya yi addu’o’i da roƙe-roƙe tare da kuka mai zafi da kuma hawaye ga wannan wanda yake da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa ji shi saboda tsananin bangirman da ya yi.
- Ibraniyawa 5:8kusan 64 M.
Ko da yake shi ɗa ne, ya yi biyayya ta wurin shan wahala
- Ibraniyawa 5:9kusan 64 M.
kuma da aka mai da shi cikakke, sai ya zama hanyar samun madawwamin ceto ga dukan waɗanda suke masa biyayya.
- Ibraniyawa 5:10kusan 64 M.
Allah kuwa ya naɗa shi yă zama babban firist, bisa ga tsarin Melkizedek.
- Ibraniyawa 5:11kusan 64 M.
Muna da abubuwa masu yawa da za mu faɗa game da wannan batu, sai dai yana da wuya a bayyana, da yake ba ku da saurin ganewa.
- Ibraniyawa 5:12kusan 64 M.
Gaskiya, a yanzu ya kamata a ce kun zama malamai, sai ga shi kuna bukatar wani yă sāke koya muku abubuwa masu sauƙi game da abin da Allah ya faɗa. Kuna bukatar madara, ba abinci mai kauri ba!
- Ibraniyawa 5:13kusan 64 M.
Duk wanda yake rayuwa a kan madara, shi kamar jariri ne har yanzu, kuma bai san ainihi mene ne ya dace ba.
- Ibraniyawa 5:14kusan 64 M.
Amma abinci mai kauri na balagaggu ne, waɗanda suka hori kansu don su bambanta tsakanin nagarta da mugunta.
- Ibraniyawa 6:1kusan 64 M.
Dole mu yi ƙoƙarin zama balagaggu mu kuma fara tunani game da abubuwan da suka fi koyarwan nan mai sauƙi game da Kiristi. Bai kamata mu ci gaba da magana game da me ya sa dole mu juye daga ayyukan da suke kawo mutuwa da kuma me ya sa za mu kasance da bangaskiya a cikin Allah ba.
- Ibraniyawa 6:2kusan 64 M.
Kuma bai kamata mu ci gaba da koyar da umarnai game da baftisma, ɗibiya hannuwa, tashin matattu, da kuma madawwamin hukunci ba.
- Ibraniyawa 6:3kusan 64 M.
Da yardar Allah, za mu ci gaba ga ƙarin ganewa.
- Ibraniyawa 6:4kusan 64 M.
Waɗanda suka taɓa samun haske, waɗanda suka ɗanɗana kyauta ta sama, waɗanda suka sami rabo cikin Ruhu Mai Tsarki,
- Ibraniyawa 6:5kusan 64 M.
waɗanda suka ɗanɗana daɗin maganar Allah da kuma ikokin zamani mai zuwa,
- Ibraniyawa 6:6kusan 64 M.
ba ya yiwuwa a sāke kawo su ga tuba in suka kauce, domin suna sāke gicciye Ɗan Allah ke nan suna kuma kunyata shi a gaban jama’a.
- Ibraniyawa 6:7kusan 64 M.
Ƙasar da take shan ruwan sama da yake fāɗi a kanta kullum da kuma take ba da hatsin da yake da amfani ga waɗanda ake noma dominsu, takan sami albarkar Allah.
- Ibraniyawa 6:8kusan 64 M.
Amma ƙasar da take ba da ƙaya da sarƙaƙƙiya ba ta da amfani tana kuma cikin hatsarin la’ana. A ƙarshe za a ƙone ta.
- Ibraniyawa 6:9kusan 64 M.
Abokaina, ko da yake muna irin maganan nan, mun tabbata kuna yi abubuwan nan masu kyau da waɗanda suka sami ceto suke yi.
- Ibraniyawa 6:10kusan 64 M.
Allah ba marar adalci ba ne. Ba zai manta da aikinku da kuma ƙaunar da kuka nuna masa wajen taimakon mutanensa da kuma ci gaba da taimakonsu da kuke yi ba.
- Ibraniyawa 6:11kusan 64 M.
Muna so kowannenku yă nuna ƙwazon nan har zuwa ƙarshe, domin ku tabbatar da begenku.