circa AD 48–96
Letters to the Churches
Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ibraniyawa 7:17kusan 64 M.
Gama nassi ya ce, “Kai firist ne na har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.”
- Ibraniyawa 7:18kusan 64 M.
Ta haka aka kawar da ƙa’ida marar ƙarfi da kuma marar amfani
- Ibraniyawa 7:19kusan 64 M.
(gama doka ba tă mai da wani abu cikakke ba), yanzu kuwa bege mafi kyau ya ɗauki matsayinta. Ta haka kuma muka matso kusa da Allah.
- Ibraniyawa 7:20kusan 64 M.
Ba kuwa da rashin rantsuwa aka yi haka ba. Waɗansu sun zama firistocin ba tare da wata rantsuwa ba,
- Ibraniyawa 7:21kusan 64 M.
shi wannan ya zama firist ta wurin rantsuwar da Allah ya yi da ya ce masa, “Ubangiji ya rantse, ba kuwa zai canja zuciyarsa ba, ‘Kai firist ne na har abada.’ ”
- Ibraniyawa 7:22kusan 64 M.
Saboda wannan rantsuwa, Yesu ya zama tabbacin alkawari mafi kyau.
- Ibraniyawa 7:23kusan 64 M.
To, akwai waɗannan firistoci da yawa, da yake mutuwa ta hana su cin gaba da aikin zaman firist;
- Ibraniyawa 7:24kusan 64 M.
amma Yesu ba zai mutu ba, don haka zai zama firist har abada.
- Ibraniyawa 7:25kusan 64 M.
Saboda haka ya iya ba da ceto gaba ɗaya ga masu zuwa wurin Allah ta wurinsa, gama kullum a raye yake saboda yă yi roƙo dominsu.
- Ibraniyawa 7:26kusan 64 M.
Irin wannan babban firist ne muke bukata, shi mai tsarki ne, marar aibi, mai tsabta, ba kamar mu masu zunubi ba sam. An ɗaukaka shi fiye da kome a sama.
- Ibraniyawa 7:27kusan 64 M.
Ba ya bukata yă yi ta miƙa hadayu kowace rana saboda zunubansa, sa’an nan saboda zunuban mutane kamar sauran firistoci. Ya miƙa hadaya sau ɗaya tak, sa’ad da ya miƙa kansa.
- Ibraniyawa 7:28kusan 64 M.
Gama doka takan naɗa babban firist a cikin mutane masu kāsawa; amma rantsuwar da ta zo bayan dokar, ta naɗa Ɗan, wanda aka mai da shi cikakke har abada.
- Ibraniyawa 8:1kusan 64 M.
Abin da muke magana a nan shi ne, muna da irin wannan babban firist, wanda ya zauna a hannun dama na kursiyin Maɗaukaki a sama,
- Ibraniyawa 8:2kusan 64 M.
wanda yake hidima a cikin wuri mai tsarki, tabanakul na gaskiya wanda Ubangiji ne ya kafa, ba mutum ba.
- Ibraniyawa 8:3kusan 64 M.
Da yake dole kowane babban firist da aka naɗa yă miƙa baye-baye da hadayu, haka ma wannan ya bukaci yă kasance da abin da zai miƙa.
- Ibraniyawa 8:4kusan 64 M.
Da a ce yana a duniya ne, da bai zama firist ba, domin a nan akwai mutanen da doka ta naɗa don su miƙa baye-baye.
- Ibraniyawa 8:5kusan 64 M.
Suna hidima a cikin tsattsarkan wuri wanda yake hoto da kuma siffar abin da yake cikin sama. Shi ya sa aka gargaɗi Musa sa’ad da yana dab da gina tabanakul cewa, “Ka lura fa, ka yi kome daidai bisa ga zānen da aka nuna maka a kan dutsen.”
- Ibraniyawa 8:6kusan 64 M.
Amma hidimar da Yesu ya karɓa tana da fifiko a kan tasu, kamar yadda alkawarin da shi ne yake matsakanci ya fi na dā fifiko nesa, an kuma kafa shi a kan alkawura mafi kyau.
- Ibraniyawa 8:7kusan 64 M.
Gama da a ce alkawari na fari ba shi da wani laifi, da ba sai an sāke neman wani ba.
- Ibraniyawa 8:8kusan 64 M.
Amma Allah ya sami mutane da laifi ya ce, “Ina gaya muku lokaci yana zuwa, sa’ad da zan yi sabon alkawari da gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda.
- Ibraniyawa 8:9kusan 64 M.
Ba zai zama kamar irin alkawarin da na yi da kakanni-kakanninsu sa’ad da na kama hannunsu don in fitar da su daga Masar ba, domin ba su yi aminci da alkawarina ba, sai na juya musu baya, in ji Ubangiji.
- Ibraniyawa 8:10kusan 64 M.
Wannan shi ne alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila, bayan lokacin nan, in ji Ubangiji. Zan sa dokokina a cikin zukatansu, in kuma rubuta su a kan zukatansu. Zan zama Allahnsu, su kuwa za su zama mutanena.
- Ibraniyawa 8:11kusan 64 M.
Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa ba, balle mutum yă ce wa ɗan’uwansa, ‘Ka san Ubangiji,’ domin dukansu za su san ni, daga ƙaraminsu zuwa babba.
- Ibraniyawa 8:12kusan 64 M.
Gama zan gafarta muguntarsu ba zan kuma ƙara tuna da zunubansu ba.”
- Ibraniyawa 8:13kusan 64 M.
Ta wurin kira wannan alkawari “sabo,” ya mai da na farin tsoho ke nan; abin da yake tsoho yana kuma daɗa tsufa, zai shuɗe nan ba da daɗewa ba.