Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 48–96

Letters to the Churches

Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.

2,767 ayoyi · 21 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ibraniyawa 9:26kusan 64 M.

    Da a ce haka ne, ai, da Kiristi ya sha wahala sau da yawa tun halittar duniya. Amma yanzu ya bayyana sau ɗaya tak a ƙarshen zamanai domin yă kawar da zunubi ta wurin miƙa kansa hadaya.

  2. Ibraniyawa 9:27kusan 64 M.

    Kamar dai yadda aka ƙaddara wa mutum yă mutu sau ɗaya, bayan haka kuma sai shari’a,

  3. Ibraniyawa 9:28kusan 64 M.

    haka aka miƙa Kiristi hadaya sau ɗaya domin yă ɗauke zunuban mutane masu yawa; zai kuma bayyana sau na biyu, ba don yă ɗauki zunubi ba, sai dai don yă kawo ceto ga waɗanda suke jiransa.

  4. Ibraniyawa 10:1kusan 64 M.

    Dokar, inuwa ce kawai ta kyawawan abubuwa masu zuwa, wannan inuwar ba ita ce ainihin abubuwan ba ne. Saboda haka ba za tă taɓa mai da masu matsowa kusa don yin sujada cikakku ta wurin irin hadayun da ake maimaitawa ba fasawa shekara-shekara ba.

  5. Ibraniyawa 10:2kusan 64 M.

    Da a ce za tă iya, da ba su daina miƙa hadayu ba? Ai, da an riga an tsabtacce masu yin sujada sau ɗaya tak, da kuma ba za su ƙara damuwa da zunubansu ba.

  6. Ibraniyawa 10:3kusan 64 M.

    Amma waɗancan hadayu abin tunawa da zunubai ne na kowace shekara,

  7. Ibraniyawa 10:4kusan 64 M.

    domin ba zai taɓa yiwuwa jinin bijimai da na awaki yă kawar da zunubai ba.

  8. Ibraniyawa 10:5kusan 64 M.

    Saboda haka, sa’ad da Kiristi ya shigo duniya ya ce, “Hadaya da sadaka kam ba ka so, sai dai ka tanadar mini jiki;

  9. Ibraniyawa 10:6kusan 64 M.

    hadayun ƙonawa da kuma hadayun zunubi ba ka ji daɗin.

  10. Ibraniyawa 10:7kusan 64 M.

    Sai na ce, ‘Ga ni nan, a rubuce yake cikin naɗaɗɗen littafi na zo in aikata nufinka, ya Allah.’ ”

  11. Ibraniyawa 10:8kusan 64 M.

    Da farko ya ce, “Hadayu da sadakoki, hadayun ƙonawa da hadayun zunubi ba ka so, ba ka kuwa jin daɗinsu” (ko da yake doka ta bukaci a yi su).

  12. Ibraniyawa 10:9kusan 64 M.

    Sa’an nan ya ce, “Ga ni nan, na zo in aikata nufinka.” Ya kawar da na farkon domin yă kafa na biyun.

  13. Ibraniyawa 10:10kusan 64 M.

    Kuma bisa ga wannan nufi, aka mai da mu masu tsarki ta wurin miƙa hadayar jikin Yesu Kiristi sau ɗaya tak.

  14. Ibraniyawa 10:11kusan 64 M.

    Kowace rana kowane firist yakan tsaya yin hidimar ibadarsa; sau da sau yakan miƙa hadayu iri ɗaya, waɗanda ba za su taɓa kawar da zunubai ba.

  15. Ibraniyawa 10:12kusan 64 M.

    Amma da Kiristi ya miƙa hadaya ɗaya ta dukan lokaci saboda zunubai, sai ya zauna a hannun dama na Allah.

  16. Ibraniyawa 10:13kusan 64 M.

    Tun daga lokacin nan yana jira a mai da abokan gābansa matashin ƙafafunsa,

  17. Ibraniyawa 10:14kusan 64 M.

    gama ta wurin hadayan nan guda ɗaya ya kammala har abada waɗanda ake tsarkake.

  18. Ibraniyawa 10:15kusan 64 M.

    Ruhu Mai Tsarki ma ya yi mana shaida game da wannan. Da farko ya ce,

  19. Ibraniyawa 10:16kusan 64 M.

    “Wannan shi ne alkawarin da zan yi da su bayan wannan lokaci, in ji Ubangiji. Zan sa dokokina a cikin zukatansu, in kuma rubuta su a kan zukatansu.”

  20. Ibraniyawa 10:17kusan 64 M.

    Sai ya ƙara da cewa, “Zunubansu da kurakuransu ba zan ƙara tunawa da su ba.”

  21. Ibraniyawa 10:18kusan 64 M.

    In an gafarta zunubai, babu sauran bukatar miƙa hadaya.

  22. Ibraniyawa 10:19kusan 64 M.

    Saboda haka, ’yan’uwa, da yake muna da wannan tabbaci na shiga Wuri Mafi Tsarki ta wurin jinin Yesu,

  23. Ibraniyawa 10:20kusan 64 M.

    ta wurin sabuwa, rayayyiyar hanya kuma wadda aka buɗe mana ta labulen nan, wato, jikinsa,

  24. Ibraniyawa 10:21kusan 64 M.

    da yake kuma muna da babban firist mai mulkin gidan Allah,

  25. Ibraniyawa 10:22kusan 64 M.

    bari mu matso kusa da Allah da zuciya mai gaskiya da kuma cikakken tabbaci mai zuwa ta wurin bangaskiya. Bari mu bar zukatan da tsabta, lamirinmu babu mugunta, da kuma jikunanmu a wanke da ruwa.