Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 48–96

Letters to the Churches

Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.

2,767 ayoyi · 21 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ibraniyawa 11:9kusan 64 M.

    Ta wurin bangaskiya ya yi zama a ƙasar da aka yi masa alkawari kamar baƙo a baƙuwar ƙasa; ya zauna a tentuna, haka ma Ishaku da Yaƙub, waɗanda su ma magādan alkawarin nan ne tare da shi.

  2. Ibraniyawa 11:10kusan 64 M.

    Gama yana zuba ido ga birnin nan mai tushe, wanda mai zānen gininsa da kuma mai gininsa Allah ne.

  3. Ibraniyawa 11:11kusan 64 M.

    Ta wurin bangaskiya Ibrahim, ko da yake shekarunsa sun wuce, Saratu kanta kuma bakararriya ce ya iya zama mahaifi domin ya amince cewa shi wanda ya yi alkawarin mai aminci ne.

  4. Ibraniyawa 11:12kusan 64 M.

    Saboda haka, daga mutum ɗaya, wanda dā shi ma da matacce kusan ɗaya ne, zuriya masu yawa suka fito kamar taurari a sararin sama da kuma kamar yashin da ba a iya ƙirgawa a bakin teku.

  5. Ibraniyawa 11:13kusan 64 M.

    Duk mutanen nan suna cikin bangaskiya sa’ad da suka mutu. Ba su kuwa karɓi abubuwan da aka yi alkawari ba; sun dai hango su suka kuma marabce su daga nesa. Suka kuma amince cewa su baƙi ne, bare kuma a duniya.

  6. Ibraniyawa 11:14kusan 64 M.

    Mutane masu faɗin irin abubuwan nan sun nuna cewa suna neman ƙasar da take tasu.

  7. Ibraniyawa 11:15kusan 64 M.

    Da a ce suna tunanin ƙasar da suka bari a baya, da sun riga sun sami damar komawa.

  8. Ibraniyawa 11:16kusan 64 M.

    A maimako, suna marmarin wata ƙasa mafi kyau, ta sama. Saboda haka Allah ba ya kunya a kira shi Allahnsu, domin ya riga ya shirya musu birni.

  9. Ibraniyawa 11:17kusan 64 M.

    Ta wurin bangaskiya Ibrahim, sa’ad da Allah ya gwada shi, sai ya miƙa Ishaku hadaya. Shi da ya karɓi alkawaran ya yi shirin miƙa makaɗaicin ɗansa,

  10. Ibraniyawa 11:18kusan 64 M.

    ko da yake Allah ya ce masa, “Ta wurin Ishaku ne za a lissafta zuriyarka.”

  11. Ibraniyawa 11:19kusan 64 M.

    Ibrahim ya yi tunani cewa Allah yana iya tā da matattu, a misalce kuwa, ya sāke karɓan Ishaku daga matattu.

  12. Ibraniyawa 11:20kusan 64 M.

    Ta wurin bangaskiya ne Ishaku ya albarkaci Yaƙub da Isuwa game da nan gabansu.

  13. Ibraniyawa 11:21kusan 64 M.

    Ta wurin bangaskiya ne Yaƙub, sa’ad da yake bakin mutuwa, ya albarkaci kowane ɗan Yusuf, ya kuma yi sujada yayinda yake jingine a kan sandansa.

  14. Ibraniyawa 11:22kusan 64 M.

    Ta wurin bangaskiya ne Yusuf, sa’ad da kwanakinsa suka yi kusan ƙarewa, ya yi magana game da fitowar Isra’ilawa daga Masar ya kuma ba da umarni game da ƙasusuwansa.

  15. Ibraniyawa 11:23kusan 64 M.

    Ta wurin bangaskiya ne iyayen Musa suka ɓoye shi har wata uku bayan haihuwarsa, domin sun ga cewa shi ba kamar sauran yara ba ne, ba su kuwa ji tsoron umarnin sarki ba.

  16. Ibraniyawa 11:24kusan 64 M.

    Ta wurin bangaskiya ne Musa, sa’ad da ya yi girma, ya ƙi a kira shi ɗan diyar Fir’auna.

  17. Ibraniyawa 11:25kusan 64 M.

    Ya zaɓa yă sha wahala tare da mutanen Allah, maimakon yă ji daɗin sha’awace-sha’awacen zunubi na ɗan lokaci.

  18. Ibraniyawa 11:26kusan 64 M.

    Ya ɗauki wulaƙancin da yake sha saboda Kiristi ya fi dukiyar Masar daraja, domin ya sa ido ga ladansa.

  19. Ibraniyawa 11:27kusan 64 M.

    Ta wurin bangaskiya ya bar Masar, ba tare da jin tsoron fushin sarki ba; ya kuwa jure domin ya ga wannan wanda ba a iya gani.

  20. Ibraniyawa 11:28kusan 64 M.

    Ta wurin bangaskiya ya kiyaye Bikin Ƙetarewa ya kuma yayyafa jini, domin kada mai hallakar ’ya’yan fari yă taɓa ’ya’yan fari na Isra’ila.

  21. Ibraniyawa 11:29kusan 64 M.

    Ta wurin bangaskiya ne mutane suka bi ta cikin Jan Teku, sai ka ce a kan busasshiyar ƙasa; amma da Masarawa suka yi ƙoƙari su yi haka, sai aka nutsar da su.

  22. Ibraniyawa 11:30kusan 64 M.

    Ta wurin bangaskiya ne katangar Yeriko ta rushe, bayan mutane suka yi ta kewaye ta har kwana bakwai.

  23. Ibraniyawa 11:31kusan 64 M.

    Ta wurin bangaskiya ne ba a kashe Rahab karuwan nan, ta tare da marasa biyayya ba don ta marabci ’yan leƙan asiri.

  24. Ibraniyawa 11:32kusan 64 M.

    Me kuma zan faɗa? Ba ni da lokacin da zan ba da labari a kan Gideyon, Barak, Samson, Yefta, Dawuda, Sama’ila, da kuma annabawa,

  25. Ibraniyawa 11:33kusan 64 M.

    waɗanda ta wurin bangaskiya ne suka ci nasara a kan mulkoki, suka aikata adalci, suka kuma sami abin da aka yi alkawari; waɗanda suka rurrufe bakunan zakoki,