Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 48–96

Letters to the Churches

Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.

2,767 ayoyi · 21 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ibraniyawa 2:4kusan 64 M.

    Allah shi ma ya shaida ta wurin alamu, abubuwan banmamaki da mu’ujizai iri-iri, da kuma baye-bayen Ruhu Mai Tsarki da aka rarraba bisa ga nufinsa.

  2. Ibraniyawa 2:5kusan 64 M.

    Ba ga mala’iku ba ne ya sa su yi mulkin duniya mai zuwa, wanda muke magana a kai ba.

  3. Ibraniyawa 2:6kusan 64 M.

    Amma akwai wani wurin da wani ya shaida cewa, “Mene ne mutum, da kake tuna da shi, ɗan mutum da kake kula da shi?

  4. Ibraniyawa 2:7kusan 64 M.

    Ka sa shi ƙasa kaɗan da darajar mala’iku; ka naɗa shi da ɗaukaka da girma,

  5. Ibraniyawa 2:8kusan 64 M.

    ka kuma sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa.” Ta wurin sa kome a ƙarƙashinsa, Allah bai bar wani abu da bai sa a ƙarƙashinsa ba. Duk da haka a yanzu ba mu ga kowane abu a ƙarƙashinsa ba.

  6. Ibraniyawa 2:9kusan 64 M.

    Sai dai muna ganin Yesu, wanda aka mai da shi ƙasa kaɗan da darajar mala’iku, yanzu kuwa an naɗa shi da ɗaukaka da girma domin yă sha wahalar mutuwa, domin ta wurin alherin Allah yă ɗanɗana mutuwa saboda kowa.

  7. Ibraniyawa 2:10kusan 64 M.

    Ta wurin kawo ’ya’ya masu yawa zuwa ga ɗaukaka, ya dace cewa Allah, wanda dominsa da kuma ta wurinsa ne kome yake kasancewa, ya sa tushen cetonsu yă zama cikakke ta wurin shan wahala.

  8. Ibraniyawa 2:11kusan 64 M.

    Da shi wanda yake tsarkake mutane da kuma su waɗanda ake tsarkakewa duk ’yan iyali ɗaya ne. Saboda haka Yesu ba ya kunyan kiransu ’yan’uwansa.

  9. Ibraniyawa 2:12kusan 64 M.

    Ya ce, “Zan sanar da sunanka ga ’yan’uwana; a gaban jama’a zan rera yabonka.”

  10. Ibraniyawa 2:13kusan 64 M.

    Har wa yau ya ce, “Zan dogara gare shi.” Ya kuma ce, “Ga ni, da ’ya’yan da Allah ya ba ni.”

  11. Ibraniyawa 2:14kusan 64 M.

    Da yake ’ya’yan suna da nama da jini, shi ma sai ya ɗauki kamanninsu na mutum domin ta wurin mutuwarsa yă hallaka wanda yake riƙe da ikon mutuwa, wato, Iblis

  12. Ibraniyawa 2:15kusan 64 M.

    ya kuma ’yantar da waɗanda dukan rayuwarsu tsoron mutuwa ya riƙe su cikin bauta.

  13. Ibraniyawa 2:16kusan 64 M.

    Gama tabbatacce ba mala’iku ne ya taimaka ba, sai dai zuriyar Ibrahim.

  14. Ibraniyawa 2:17kusan 64 M.

    Saboda wannan dole a mai da shi kamar ’yan’uwansa ta kowace hanya, domin yă zama babban firist mai aminci da mai jinƙai cikin hidima ga Allah, yă kuma miƙa hadayar sulhu saboda zunuban mutane.

  15. Ibraniyawa 2:18kusan 64 M.

    Domin shi kansa ya sha wahala sa’ad da aka gwada shi, yana iya taimakon waɗanda ake yi wa gwaji.

  16. Ibraniyawa 3:1kusan 64 M.

    Saboda haka, ’yan’uwa tsarkaka, waɗanda suke da rabo a kiran nan na sama, ku kafa tunaninku a kan Yesu, manzo da kuma babban firist wanda muke shaidawa.

  17. Ibraniyawa 3:2kusan 64 M.

    Ya yi aminci ga wanda ya naɗa shi, kamar yadda Musa ya yi aminci ga dukan gidan Allah.

  18. Ibraniyawa 3:3kusan 64 M.

    An ga Yesu ya cancanci girma fiye da Musa, kamar yadda mai ginin gida ya fi gidan daraja.

  19. Ibraniyawa 3:4kusan 64 M.

    Gama kowane gida yana da wanda ya gina shi, amma maginin dukan abu Allah ne.

  20. Ibraniyawa 3:5kusan 64 M.

    Musa ya yi aminci a matsayin bawa cikin dukan gidan Allah, yana ba da shaida a kan abubuwan da za a faɗa nan gaba.

  21. Ibraniyawa 3:6kusan 64 M.

    Amma Kiristi mai aminci ne kamar ɗa a gidan Allah. Mu kuwa gidansa ne, in muka tsaya gabanmu gadi da kuma begen da muke taƙama a kai.

  22. Ibraniyawa 3:7kusan 64 M.

    Kamar dai yadda Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Yau, in kuka ji muryarsa,

  23. Ibraniyawa 3:8kusan 64 M.

    kada ku taurare zukatanku, yadda kuka yi a tawayen nan, a lokacin gwaji a hamada,

  24. Ibraniyawa 3:9kusan 64 M.

    inda kakanninku suka gwada ni, suka kuma gwada ni, ko da yake a cikin shekaru arba’in sun ga abin da na yi.

  25. Ibraniyawa 3:10kusan 64 M.

    Shi ya sa na yi fushi da wancan zamani, na kuma ce, ‘Kullum zukatansu a karkace suke, ba su kuma san hanyoyina ba.’