- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 48–96
Letters to the Churches
Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Titus 3:8kusan 65 M.
Wannan magana tabbatacciya ce, ina kuma so ka nanata waɗannan abubuwa ƙwarai, domin waɗanda suka dogara ga Allah su himmantu ga aiki mai kyau. Waɗannan abubuwa suna da kyau sosai suna kuma da amfani ga kowane mutum.
- Titus 3:9kusan 65 M.
Amma ka guji jayayyar banza da ƙididdigar asali da gardandami da faɗace-faɗace game da Doka, gama ba su da riba kuma aikin banza ne.
- Titus 3:10kusan 65 M.
Ka gargaɗe mutumin da yake kawo tsattsaguwa sau ɗaya, ka kuma gargaɗe shi sau na biyu. Bayan haka, kada wani abu yă haɗa ka da shi.
- Titus 3:11kusan 65 M.
Ka dai san cewa irin mutumin nan ya taurare kuma mai zunubi ne; ya yanke wa kansa hukunci.
- Titus 3:12kusan 65 M.
Da zarar na aika Artemas ko Tikikus zuwa wurinka, sai ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka zo wurina a Nikofolis, domin na yanke shawara in ci damina a can.
- Titus 3:13kusan 65 M.
Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka taimaki Zenas lauyan nan da Afollos a hanyarsu ka kuma tabbata ba su rasa kome ba.
- Titus 3:14kusan 65 M.
Dole mutanenmu su koyi ba da kansu ga aikata abin da yake nagari, domin su iya biyan bukatunsu na yau da kullum kada kuma su yi rayuwar marar amfani.
- Titus 3:15kusan 65 M.
Dukan waɗanda suke tare da ni suna gaishe ka. Ka gaggai mini da masoyanmu, masu bangaskiya. Alheri yă kasance tare da ku duka.
- Filemon 1:1kusan 64 M.
Bulus, ɗan kurkuku saboda Kiristi Yesu, da kuma Timoti ɗan’uwanmu, Zuwa ga Filemon ƙaunataccen abokinmu da kuma abokin aikinmu,
- Filemon 1:2kusan 64 M.
zuwa kuma ga Affiya ’yar’uwarmu, zuwa kuma ga Arkiffus abokin famarmu, da zuwa kuma ga ikkilisiyar da take taruwa a gidanka.
- Filemon 1:3kusan 64 M.
Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.
- Filemon 1:4kusan 64 M.
Kullum nakan gode wa Allahna sa’ad da nake tuna da kai cikin addu’o’ina,
- Filemon 1:5kusan 64 M.
domin ina jin labari bangaskiyarka cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunarka da kake yi saboda dukan tsarkaka.
- Filemon 1:6kusan 64 M.
Ina addu’a ka zama mai ƙwazo cikin shaida bangaskiyarka, domin ka sami cikakken fahimta ta kowane abin da yake nagarin da muke da shi cikin Kiristi.
- Filemon 1:7kusan 64 M.
Ƙaunarka ta sa ni farin ciki ƙwarai ta kuma ƙarfafa ni, domin kai, ɗan’uwa, ka wartsake zukatan tsarkaka.
- Filemon 1:8kusan 64 M.
Saboda haka, ko da yake cikin Kiristi ina iya yin ƙarfin hali in umarce ka ka yi abin da ya kamata,
- Filemon 1:9kusan 64 M.
duk da haka ina roƙonka saboda ƙauna, na fi so in roƙe ka, ni Bulus tsoho, a yanzu kuma ga ni ɗan sarƙa saboda Kiristi Yesu.
- Filemon 1:10kusan 64 M.
Ina roƙonka saboda ɗana Onesimus, wanda ya zama ɗana yayinda nake cikin sarƙoƙi.
- Filemon 1:11kusan 64 M.
Dā kam, ba shi da amfani a gare ka, amma yanzu ya zama da amfani a gare ka da kuma gare ni.
- Filemon 1:12kusan 64 M.
Ina aike shi yă koma gare ka, shi da yake zuciyata.
- Filemon 1:13kusan 64 M.
Na so in riƙe shi a wurina a madadinka domin yă taimake ni yayinda nake cikin sarƙoƙi saboda bishara.
- Filemon 1:14kusan 64 M.
Sai dai ban so in yi kome ban da yardarka ba, domin kowane alherin da za ka yi, yă fito daga zuciyarka, ba na tilas ba.
- Filemon 1:15kusan 64 M.
Wataƙila abin da ya sa aka raba ka da shi na ɗan lokaci ƙanƙani shi ne don ka same shi da amfani
- Filemon 1:16kusan 64 M.
ba kamar bawa kuma ba, sai dai fiye da bawa, a matsayin ƙaunataccen ɗan’uwa. Shi ƙaunatacce ne sosai a gare ni amma a gare ka ya ma fi zama ƙaunatacce, kamar mutum da kuma kamar ɗan’uwa a cikin Ubangiji.
- Filemon 1:17kusan 64 M.
Saboda haka in ka ɗauke ni a kan ni abokin tarayya ne, sai ka marabce shi kamar yadda za ka marabce ni.