- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 48–96
Letters to the Churches
Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 2 Korintiyawa 7:15kusan 60 M.
Ƙaunar da yake yi muku ya ƙaru ƙwarai, duk sa’ad da yake tunawa da biyayyarku duka, da kuma irin yawan bangirman da kuka nuna masa lokacin da kuka karɓe shi.
- 2 Korintiyawa 7:16kusan 60 M.
Ina farin ciki ne don na amince da ku ƙwarai da gaske.
- 2 Korintiyawa 8:1kusan 60 M.
To, ’yan’uwa, muna so ku san abin da alherin Allah ya ba wa ikkilisiyoyin Makidoniya.
- 2 Korintiyawa 8:2kusan 60 M.
Gama sun sha wuya sosai saboda tsananin wahalar da suka shiga, har yawan farin cikinsu ya kai su ga yin alheri ta bayarwa ga waɗansu, ko da yake suna cikin tsananin talauci.
- 2 Korintiyawa 8:3kusan 60 M.
Gama ina shaida cewa sun bayar daidai gwargwadon iyawarsu, har ma fiye da ƙarfinsu. Su kansu,
- 2 Korintiyawa 8:4kusan 60 M.
sun roƙe mu sosai don su sami damar yin bayarwa a wannan hidima ga tsarkaka.
- 2 Korintiyawa 8:5kusan 60 M.
Ba su yi yadda muka za tă ba, sai ma suka fara ba da kansu ga Ubangiji, sa’an nan sai suka ba da kansu gare mu bisa ga nufin Allah.
- 2 Korintiyawa 8:6kusan 60 M.
Ganin haka sai muka roƙi Titus, da yake shi ne ya riga ya tsiro da wannan aikin alheri a cikinku, sai yă ƙarasa shi.
- 2 Korintiyawa 8:7kusan 60 M.
To, da yake kun fiffita a kowane abu cikin bangaskiya, cikin magana, cikin sani, cikin dukan ƙwazo, da kuma cikin ƙaunarku dominmu, sai ku fiffita a wannan aikin alheri ma.
- 2 Korintiyawa 8:8kusan 60 M.
Ba umarni nake ba ku ba, sai dai ina so in gwada gaskiyar ƙaunarku ne, ta wurin kwatanta ta da aniyar waɗansu.
- 2 Korintiyawa 8:9kusan 60 M.
Gama kun san alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi cewa ko da yake shi mawadaci ne, duk da haka, ya zama matalauci saboda ku, domin ta wurin talaucinsa, ku zama mawadata.
- 2 Korintiyawa 8:10kusan 60 M.
Ga shawarata a kan abin da ya fi muku kyau a wannan al’amari. Bara ku kuka fara bayarwa, kuka kuma zama na farko wajen niyyar yin haka.
- 2 Korintiyawa 8:11kusan 60 M.
Yanzu sai ku ƙarasa aikin da irin niyyar da kuka fara, ku yi haka gwargwadon ƙarfinku.
- 2 Korintiyawa 8:12kusan 60 M.
Gama in da niyyar bayarwa, za a karɓi bayarwa bisa ga abin da mutum yake da shi, ba bisa ga abin da ba shi da shi ba.
- 2 Korintiyawa 8:13kusan 60 M.
Ba nufi nake yi a sawwaƙe wa waɗansu, ku kuwa a jibga muku nauyin ba. Amma ya yi kyau dai
- 2 Korintiyawa 8:14kusan 60 M.
a raba daidai wa daida, sai ku taimake su a yanzu da yalwarku saboda rashinsu. Wata rana su ma su taimake ku da yalwarsu saboda rashinku, don a daidaita al’amari,
- 2 Korintiyawa 8:15kusan 60 M.
kamar yadda yake a rubuce cewa, “Wanda ya tara da yawa, bai tara fiye da bukatarsa ba, wanda kuma ya tara kaɗan, bai kāsa masa ba.”
- 2 Korintiyawa 8:16kusan 60 M.
Ina gode wa Allah, wanda ya sa a zuciyar Titus, irin kula da nake da shi dominku.
- 2 Korintiyawa 8:17kusan 60 M.
Ba kawai ya yarda yă je wurinku kamar yadda muka roƙe shi yă yi ba, amma ya so yă zo kamar yadda ya riga ya yi niyya.
- 2 Korintiyawa 8:18kusan 60 M.
Ga shi mun aiko ɗan’uwanmu nan tare da shi, wanda ikkilisiyoyi duka suna yabo saboda hidimarsa ga bishara.
- 2 Korintiyawa 8:19kusan 60 M.
Ba kuwa haka kaɗai ba, har ma ikkilisiyoyi sun zaɓe shi yă riƙa tafiya tare da mu kan wannan aikin alheri da muke yi saboda ɗaukakar Ubangiji, da kuma nuna kyakkyawar niyyarmu.
- 2 Korintiyawa 8:20kusan 60 M.
Muna gudu kada wani yă zarge mu, a kan yadda muke gudanar da wannan kyautar da aka bayar hannu sake.
- 2 Korintiyawa 8:21kusan 60 M.
Gama muna iya ƙoƙari mu yi abin da yake daidai, ba a gaban Ubangiji kaɗai ba, amma a gaban mutane ma.
- 2 Korintiyawa 8:22kusan 60 M.
Ban da wannan kuma, mun aiko da ɗan’uwanmu tare da su, wanda ya sha tabbatar mana da ƙwazonsa ta hanyoyi iri-iri, musamman yanzu, domin ya amince da ku da gaske.
- 2 Korintiyawa 8:23kusan 60 M.
Game da Titus kuma, shi abokin tarayyata ne, da kuma abokin aikina a cikinku; game da ’yan’uwanmu kuwa, su wakilai ne na ikkilisiyoyi, kuma su masu ɗaukaka Kiristi ne.