- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 48–96
Letters to the Churches
Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 2 Korintiyawa 8:24kusan 60 M.
Saboda haka, ku nuna wa waɗannan mutane shaidar ƙaunarku, da kuma dalilin taƙamarmu da ku, domin ikkilisiyoyi su gani.
- 2 Korintiyawa 9:1kusan 60 M.
Babu wata bukata in rubuta muku game da hidiman nan ga tsarkaka.
- 2 Korintiyawa 9:2kusan 60 M.
Gama na san aniyarku na yin taimako, ina kuma taƙama a kan wannan ga Makidoniyawa, ina faɗin musu cewa tun bara, ku da kuke a Akayya a shirye kuke ku bayar. Ƙoƙarinku kuwa ya zuga yawancinsu ga aiki.
- 2 Korintiyawa 9:3kusan 60 M.
Amma ina aika ’yan’uwan nan don kada taƙamar da muke yi da ku, a kan wannan al’amari ta zama a banza, sai dai domin yă zama kuna nan a shirye, kamar yadda na faɗa za ku kasance.
- 2 Korintiyawa 9:4kusan 60 M.
Gama in waɗansu mutanen Makidoniya sun zo tare da ni, suka tarar ba a shirye kuke ba, kunya ta ishe mu, balle fa ku, saboda amincewa da muke yi da ku.
- 2 Korintiyawa 9:5kusan 60 M.
Saboda haka, na ga ya dace in roƙi ’yan’uwan nan su ziyarce ku kafin lokacin, su kuma gama shirye-shirye saboda bayarwa ta yardar ran da kuka yi alkawari. Ta haka bayarwar za tă zama a shirye, ta yardar rai ba ta dole ba.
- 2 Korintiyawa 9:6kusan 60 M.
Ku tuna fa, duk wanda ya yi shuki kaɗan zai girbe kaɗan, kuma duk wanda ya yi shuki da yawa, zai girbe a yalwace.
- 2 Korintiyawa 9:7kusan 60 M.
Ya kamata kowa yă bayar bisa ga abin da ya yi shawara a zuciyarsa, ba tare da jin nauyi ko don dole ba, gama Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai.
- 2 Korintiyawa 9:8kusan 60 M.
Allah kuwa yana da iko yă ba ku fiye da bukatarku, domin kullum ku wadata da kome ta kowace hanya, kuna ta bayarwa hannu sake, kowane irin kyakkyawan aiki.
- 2 Korintiyawa 9:9kusan 60 M.
Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Ya ba gajiyayyu hannu sake, ayyukansa na alheri madawwama ne.”
- 2 Korintiyawa 9:10kusan 60 M.
To, shi da yake ba mai shuka iri, yake kuma ba da abinci a ci, shi ne zai ba ku irin shukawa, yă riɓanya shi, yă kuma albarkaci ayyukanku na alheri da yawa.
- 2 Korintiyawa 9:11kusan 60 M.
Za a wadatar da ku ta kowace hanya, domin ku riƙa bayarwa hannu sake a kowane lokaci. Ta wurinmu kuma bayarwarku hannu sake za tă zama sanadin godiya ga Allah.
- 2 Korintiyawa 9:12kusan 60 M.
Wannan hidimar da kuke yi, ba bukatun mutanen Allah kaɗai take biya ba, amma tana cike da hanyoyin nuna godiya masu yawa ga Allah.
- 2 Korintiyawa 9:13kusan 60 M.
Aikin nan naku na alheri tabbatar bangaskiyarku ne, za a kuwa ɗaukaka Allah saboda kun bayyana yarda, cewa kun yi na’am da bisharar Kiristi, saboda kuma gudummawa da kuka yi musu da saura duka, hannu sake.
- 2 Korintiyawa 9:14kusan 60 M.
A cikin addu’arsu dominku kuwa, zukatansu za su koma gare ku, saboda mafificin alherin da Allah ya ba ku.
- 2 Korintiyawa 9:15kusan 60 M.
Godiya ga Allah, saboda kyautarsa da ta wuce misali!
- 2 Korintiyawa 10:1kusan 60 M.
Ni Bulus da kaina, ina roƙonku albarkacin tawali’u da sanyin hali na Kiristi, ni da ake yi wa kirari “marar tsanani” a cikinku, amma “mai matsawa” sa’ad da nake rabe da ku!
- 2 Korintiyawa 10:2kusan 60 M.
Ina roƙonku cewa sa’ad da na zo kada ku tilasta ni in matsa muku, gama na tabbata zan iya tsaya wa waɗanda suka ce abin da muke yi sha’anin duniya ne.
- 2 Korintiyawa 10:3kusan 60 M.
Ko da yake muna cikin duniya, ba ma yaƙi kamar yadda duniya take yi.
- 2 Korintiyawa 10:4kusan 60 M.
Makaman da muke yaƙi da su, ba makamai na duniya ba ne. Sai dai na ikon Allah ne, masu rushe wuraren mafaka masu ƙarfi.
- 2 Korintiyawa 10:5kusan 60 M.
Muna ka da masu gardama da kowane tunanin ɗaga kai da yake kafa kansa gāba da sanin Allah, muna kuma jan hankalin kowa ga bautar Kiristi.
- 2 Korintiyawa 10:6kusan 60 M.
A shirye muke mu hori kowane rashin biyayya, sa’ad da biyayyarku ta cika.
- 2 Korintiyawa 10:7kusan 60 M.
Kuna duban abubuwa bisa-bisa ne kawai. In wani ya ganin cewa shi na Kiristi ne, ya kamata yă sāke lura cewa kamar yadda yake na Kiristi, haka mu ma muke.
- 2 Korintiyawa 10:8kusan 60 M.
Ko da zan yi gadara fiye da kima a game da izinin nan namu, wanda Ubangiji ya bayar saboda inganta ku, ba don rushe ku ba, ba ni da abin jin kunya a ciki.
- 2 Korintiyawa 10:9kusan 60 M.
Ba na so yă zama kamar ina ƙoƙari in tsorata ku ne da wasiƙuna.