Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 48–96

Letters to the Churches

Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.

2,767 ayoyi · 21 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. A wannan taƙamata ba na magana yadda Ubangiji zai yi ba ne, sai dai magana ce irin ta wawa.

  2. Da yake mutane da yawa suna taƙama irin ta duniya, ni ma haka zan yi.

  3. Ku kam kuna da wayo sosai, har kuna jimre wa wawaye da murna!

  4. Gaskiyar ita ce, kuna haƙuri da duk wanda ya sa ku bauta ko ya cuce ku ko ya more ku ko ya nuna muku isa ko kuma ya mare ku a fuska.

  5. Ina jin kunya in ce mun nuna kāsawa da ba mu yi waɗannan abubuwan ba! Abin da wani yake da ƙarfin hali yin taƙama a kai, shi ne ni ma nake ƙarfin hali yin taƙama a kai. Ina magana kamar wawa ne.

  6. In su Ibraniyawa ne, ni ma haka. In su Isra’ilawa ne, ni ma haka. In su zuriyar Ibrahim ne, ni ma haka.

  7. In su bayin Kiristi ne, ni na fi su ma, ina magana kamar ruɗaɗɗe ne fa! Ai, na fi su shan fama ƙwarai da gaske, da shan dauri, na sha dūka marar iyaka, na sha hatsarin mutuwa iri-iri.

  8. Sau biyar Yahudawa suka yi mini bulala arba’in ɗaya babu.

  9. Sau uku aka bulale ni da bulalar ƙarfe, sau ɗaya aka jajjefe ni da duwatsu, sau uku jirgin ruwa ya ragargaje ina ciki, na kwana na kuma yini ruwan teku yana tafiya da ni.

  10. Na yi tafiye-tafiye da yawa, na sha hatsari a koguna, na sha hatsarin ’yan fashi, na sha hatsari a hannun kabilarmu, na sha hatsari a hannun al’ummai, na sha hatsari a birane, na sha hatsari a jeji, na sha hatsari a teku, na kuma sha hatsarin ’yan’uwa na ƙarya.

  11. Na yi fama, na shan wuya, ga kuma rashin barci sau da yawa. Na san abin da ake nufin da jin yunwa da ƙishirwa, sau da yawa kuwa na kasance da rashin abinci, na sha sanyi da zaman tsirara.

  12. Ban da waɗannan abubuwa, kowace rana ina ɗauke da nauyin kula da dukan ikkilisiyoyi.

  13. Wane ne ya rasa ƙarfi, da ban ji shi a jikina ba? Wane ne ya fāɗi cikin zunubi, da ban ji zafin wannan ba?

  14. In ma lalle ne in yi taƙama, to, sai in yi taƙama da abubuwan da suka nuna rashin ƙarfina.

  15. Allah Uban Ubangiji Yesu Kiristi, wanda yabo ta tabbata a gare shi har abada, ya san cewa ba ƙarya nake yi ba.

  16. A Damaskus, gwamnan da yake ƙarƙashin Sarki Aretas, ya sa tsare ƙofofin birnin Damaskus, don yă kama ni.

  17. Amma aka saukar da ni cikin kwando ta tagar katanga, na kuɓuce masa.

  18. Dole in ci gaba da yin taƙama. Ko da yake ba za tă amfane ni ba, zan yi magana a kan ru’uyoyi da wahayoyi waɗanda na karɓa daga Ubangiji.

  19. Na san wani a cikin Kiristi wanda shekaru goma sha huɗu da suka wuce an ɗauke zuwa sama ta uku. Ko a cikin jiki ne, ko kuwa ba a cikin jiki ba, ni dai ban sani ba, Allah ne ya sani.

  20. Na kuma san cewa wannan mutum, ko a cikin jiki ne, ko kuma ba a cikin jiki ba, ni dai ban sani ba, amma Allah ne ya sani,

  21. an ɗauke shi ne zuwa aljanna. Ya ji waɗansu abubuwa waɗanda ba zai iya faɗarsu da kalmomi ba, abubuwan da ba a ba wa mutum damar faɗi.

  22. Zan yi taƙama game da mutum irin wannan, sai dai ni ba zan yi taƙama da kaina ba, sai dai a kan rashin ƙarfina.

  23. Ko da zan so yin gadara ma, ba zan zama wawa ba, gama gaskiya zan faɗa. Amma na bar zancen haka, don kada wani ya ɗauke ni fiye da yadda yake ganina, ko yadda yake jin maganata.

  24. Don kada in cika da girman kai saboda waɗannan mafifitan manyan wahayoyi, sai aka sa mini wata ƙaya a jikina wadda ta zama ɗan saƙon Shaiɗan, don ta wahalshe ni.

  25. Sau uku na roƙi Ubangiji yă raba ni da wannan abu.