Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 48–96

Letters to the Churches

Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.

2,767 ayoyi · 21 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Amma ya ce mini, “Alherina ya ishe ka, domin a cikin rashin ƙarfi ne ake ganin cikar ikona.” Saboda haka, zan ƙara yin taƙama da farin ciki game da rashin ƙarfina, domin ikon Yesu Kiristi yă zauna tare da ni.

  2. Shi ya sa nake murna cikin rashin ƙarfi, da zagi, da shan wahaloli, da tsanantawa, da matsaloli, saboda Kiristi. Don a sa’ad da nake marar ƙarfi a nan ne nake da ƙarfi.

  3. Na yi wauta kam, amma ku ne kuke tilasta mini, ku ne kuwa ya kamata ku yaba mini, domin ba inda na kāsa waɗannan mafiffitan manzanni, ko da yake ni ba kome ba ne.

  4. Abubuwan da suke tabbatar da manzo, alamu, abubuwa da kuma ayyukan banmamaki, an aikata su a cikinku da matuƙar nacewa.

  5. Ta yaya ne darajarku ba tă kai ta sauran ikkilisiyoyi ba, ko kuwa don dai ban nawaita muku ba ne? Ku gafarta mini wannan laifi!

  6. Yanzu a shirye nake in ziyarce ku sau na uku, ba zan kuma nawaita muku ba, don ba kayanku nake so ba, ku nake so. Gama ba yara ne da ɗaukar nauyin iyayensu ba, sai dai iyaye ne da ɗaukar nauyin yaran.

  7. Don haka ina farin ciki in kashe dukan abin da nake da shi a kanku, har in ba da kaina ma dominku. In na ƙaunace ku fiye da haka, za ku rage ƙaunarku gare ni ne?

  8. To, shi ke nan, ban nawaita muku ba. Ashe, sai ku ce dabara na yi muku, na shawo kanku ta hanyar yaudara!

  9. Na cuce ku ne ta wurin wani daga cikin waɗanda na aiko a gare ku?

  10. Na roƙi Titus ya zo wurinku. Na kuma aiki ɗan’uwanmu tare da shi. Ko Titus ya cuce ku ne? Ba ruhu ɗaya yake bi da mu ba? Ba kuma hanya guda muka bi ba?

  11. Ko tun dā can, kuna tsammani muna kāre kanmu a gare ku ne? A gaban Allah muke magana, kamar waɗanda suke cikin Kiristi. Ƙaunatattuna, kome da muke yi, muna yi ne don inganta ku ne.

  12. Gama ina tsoro, in na zo, in tarar da ku dabam da yadda nake so, ku ma ku tarar da ni dabam da yadda kuke so. Ina tsoro kada yă zama akwai faɗa, da kishi, da fushi mai zafi, da tsattsaguwa, da ɓata suna, da gulma, da girman kai, da hargitsi.

  13. Ina tsoro kada sa’ad da na sāke zuwa, Allahna zai ƙasƙantar da ni a gabanku, kuma in yi baƙin ciki saboda waɗanda suka yi zunubi a dā, ba su kuma tuba daga aikin ƙazanta, da na fasikanci, da kuma lalata da suka sa kansu a ciki ba.

  14. Wannan za tă zama ziyarata ta uku a wurinku ke nan. “Dole a tabbatar da kowace magana ta bakin shaidu biyu ko uku.”

  15. Na riga na yi muku gargaɗi sa’ad da nake tare da ku a zuwana na biyu. Yanzu da ba na nan tare da ku, ina maimaita irin gargaɗin nan domin in na zo ba wanda zai kuɓuce wa horon nan,

  16. da yake kuna neman tabbaci cewa Kiristi yana magana ta wurina ne. To, ai, shi ba rarrauna ba ne a gare ku, amma ƙaƙƙarfa ne a cikinku.

  17. Ko da yake tabbatacce an gicciye shi cikin rashin ƙarfi, duk da haka, yana rayuwa bisa ga ikon Allah. Haka mu ma marasa ƙarfi ne a cikinsa, amma ta wurin ikon Allah za mu rayu tare da shi don mu yi muku hidima.

  18. Ku gwada kanku ku gani ko kuna cikin bangaskiya; ku auna kanku. Ashe, ba ku san cewa Kiristi Yesu yana cikinku ba? Sai ko in kun fāɗi gwajin.

  19. Ina fata za ku gane cewa ba mu fāɗi gwajin ba.

  20. Muna addu’a ga Allah kada ku aikata wani laifi. Ba don mutane su gani cewa mun ci gwajin ba ne, a’a, sai dai don ku yi abin da yake daidai, ko da yake zai zama kamar mun fāɗi gwajin ne.

  21. Kai, ba dama mu saɓa wa gaskiya, sai dai mu bi bayan gaskiyar.

  22. Murna muke sa’ad da ba mu da ƙarfi, ku kuwa kuna da ƙarfi. Addu’armu ita ce, ku zama cikakku.

  23. Shi ya sa nake rubuta waɗannan abubuwa, sa’ad da ba na nan tare da ku, domin sa’ad da na zo, kada yă zama mini tilas in yi muku tsanani a game da nuna ikon nan da Ubangiji ya ba ni saboda ingantawa, ba saboda rushewa ba.

  24. A ƙarshe ’yan’uwa, sai wata rana. Ku yi ƙoƙari ku zama cikakku. Ku saurari roƙona, ku zama da tunani ɗaya, ku yi zaman salama. Allah na ƙauna da salama kuwa zai kasance tare da ku.

  25. Ku gaggai da juna da sumba mai tsarki.